ukarofi

12715 Posts
Zargin ɓatanci: Kwamitin Shura na Kano ya tattauna da Malam Triumph a ofishin DSS

Zargin ɓatanci: Kwamitin Shura na Kano ya tattauna da Malam Triumph a ofishin DSS

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano A ƙoƙarin magance rikici da tabbatar da zaman lafiya, kwamitin shura na Jihar Kano ya gana da Malam Lawal Abubakar, da aka fi sani da Triumph, a ofishin hukumar tsaro ta DSS. Ganawar na da nasaba da zarge-zargen da ake masa na yin wasu kalamai da ake ganin sun ƙunshi ɓatanci ga Manzon Allah (SAW). Wannan mataki ya biyo bayan ƙarar da wasu malamai da al’ummar Musulmi suka shigar, inda suka buƙaci a ɗauki matakin doka akan kalaman da Malam ya yi a cikin wata huɗuba ko wa’azi da ya gabatar. Kazalika, kwamitin ya bayyana…
Read More
Al’ummar kudancin Katsina sun gudanar da zaman sasanci da ‘yan bindiga

Al’ummar kudancin Katsina sun gudanar da zaman sasanci da ‘yan bindiga

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ƙananan hukumomin Bakori, ƙanƙara ,Ƙafur, Funtua da malumfashi suka halarci zaman sulhun da ya gudana a garin Kakumi da ke ƙaramar hukumar Bakori. A ɓangaren 'yan bindigan akwai su Ado Aleru da Isiya kwashen Garwa da kuma Babano waɗanda sanannun 'yan ta'adda ne da suka daɗe suna hallaka mutanen yankin. Shugaban ƙaramar hukumar Bakori Alhaji Abubakar Musa Barde wanda ya ɗauki nauyin zaman ya bayyana zaman sulhun a matsayin babban al'amari da zai sake gina yarda da juna a tsakanin Hausawa da Fulani a yankin. Shima ɗan majalisar dokoki da ke wakilan ƙaramar hukumar Bakori…
Read More
Ya mutu bayan yi masa dashen ƙodar alade

Ya mutu bayan yi masa dashen ƙodar alade

Mutum na farko da aka yi wa dashen ƙodar alade ya mutu wata biyu bayan yi masa aikin. Richard Slyman mai shekara 62 ya yi ta fama da ciwon ƙoda kafin a yi masa wannan tiyata a watan Maris. Babban asibitin Massachusetts ne ya sanar da rasuwar tasa a ranar Lahadi, sai dai ba a tabbatar da ko mutuwar tasa na da alaƙa da tiyatar da aka masa. Tiyatar da aka yi wa Slayman ta shiga tarihi, saboda yadda aka yi ta ƙalau, ba tare da samun wata matsala ba, saɓani waɗanda aka sha yi a baya. Dama dai bayanai…
Read More
Likitoci sun cire cokula da burushi a cikin mara lafiya

Likitoci sun cire cokula da burushi a cikin mara lafiya

Likitoci a Asibitin Deɓnandani da ke yankin Hapur a ƙasar Indiya, sun yi nasarar cire wasu baƙin ababe a cikin wani mara lafiya mai kimanin shekaru 40 bayan masa wani aiki na tsawon sa’o’i biyar a farkon wannan watan. A ranar 17 ga watan Satumbar da ta gabata aka kwantar da shi sakamakon ciwon ciki mai tsanani, amai da kasala. A yayin da ake masa aikin ne aka yi arangama da cokulan silba guda 29, alburushi 19 da biro biyu. Aikin haska ciki da aka yi gabanin haka ya nuna wani baƙon yanayi, lamarin da ya girgiza tawagar likitocin. Babban…
Read More
NIRSAL ta ware tallafin Naira biliyan 70 ga harkar noma a 2025

NIRSAL ta ware tallafin Naira biliyan 70 ga harkar noma a 2025

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar da ke bayar da lamuni kan harkar noma ta Babban Bankin Nijeriya (NIRSAL) ta bayyana samun gagarumar nasara a ayyukanta na bana, inda ta taimaka wajen samun fiye da Naira Biliyan 70 a matsayin tallafin kuɗi daga bankuna don bunƙasa harkokin noma da kasuwancin noma zuwa ƙarshen shekarar 2025 — abin da ke zama shekara mafi nasara tun bayan kafuwarta. Tun daga lokacin da aka kafa ta a 2013, wannan sakamako na bana ya kai kusan kashi 25 cikin ɗari na jimillar Naira Biliyan 270 da hukumar ta taimaka wajen samarwa ga ɓangaren noma tun…
Read More
Musk ya zama mutum na farko da ya mallaki Dala biliyan 500

Musk ya zama mutum na farko da ya mallaki Dala biliyan 500

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Elon Musk a ranar Alhamis ya zama mutum na farko da aka kiyasta ya mallaki dalar Amurka biliyan 500. Wannan a cewar Mujallar Amurka Forbes, dukiya ce da ya fi samu a hannun jarin kamfanin ƙera motoci na Tesla da na'urar sararin samaniyar Spaceɗ. Forbes ta ƙididdige dukiyar Musk a kusan dala biliyan 150 fiye da wanda ya kafa Oracle Larry Ellison. Mujallar daga baya ta sake duba kiyasin zuwa dala biliyan 499.1. Arzikin Musk ya fi na sauran hamshaƙan attajirai wuyar kiyasin saboda yawancin kamfanoninsa ba a sayar da su a bainar jama'a. Musk ya…
Read More
Tattalin arzikin Nijeriya na bunƙasa a zamanin Tinubu – Akume

Tattalin arzikin Nijeriya na bunƙasa a zamanin Tinubu – Akume

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya bayyana cewa tattalin arzikin Nijeriya na samun ci gaba a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa hakan alama ce ta ci gaba a tafiyar ƙasar. Akume ya faɗi haka ne a yayin ƙaddamar da taron ƙungiyar Shugabannin Kiristoci ta Arewacin Nijeriya (NOCRELA) da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis. Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa taken taron shi ne “Rawar da shugabannin Kirista ke takawa wajen gina ƙasa.” Akume ya ce, tattalin arzikin ƙasar ya nuna alamun inganta, inda ya ambaci cewa tattalin…
Read More
Sabon tsarin haraji ya fayyace dokar masu samun kuɗi ta intanet – Oyedele

Sabon tsarin haraji ya fayyace dokar masu samun kuɗi ta intanet – Oyedele

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban Kwamitin Shugaban ƙasa kan Sauya Tsarin Haraji da Manufofin Kuɗi, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa kuɗaɗen shiga daga kadarorin intanet kamar cryptocurrency ba sabbin abubuwan haraji ba ne a tsarin Nijeriya, domin tuni dokar harajin mutum ta tanade su tun da farko. Ya ce, sabon tsarin dokar haraji da aka amince da shi bai ƙirƙiri sabbin haraji ba, sai dai ya bayyana, ya sauƙaƙa, kuma ya daidaita tsarin da ke akwai. Oyedele ya yi wannan bayani ne a taron tattaunawa da manema labarai da masu tasiri da masana da aka gudanar a Lagas a ƙarshen…
Read More
Tsarin cinikin ɗanyen mai da Naira zai ci gaba da aiki – Tinubu

Tsarin cinikin ɗanyen mai da Naira zai ci gaba da aiki – Tinubu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta ci gaba da aiwatar da tsarin “ɗanyen mai a naira” da ake amfani da shi wajen tallafa wa masu tace mai na cikin gida, domin rage kuɗin tace mai da canjin farashin dalar Amurka. ƙaramin Ministan Albarkatun Mai, Sanata Heineken Lokpobiri, ne ya bayyana haka a taron ƙungiyar Masu Tace Mai ta Nijeriya (CORAN) Summit 2025 da aka gudanar a Legas ranar Talata. Lokpobiri ya ce, manufar gwamnati ita ce tabbatar da cewa duk ganga ɗaya na mai da ake fitarwa daga Nijeriya na taimakawa wajen biyan buƙatun cikin…
Read More
Hanyoyin  rage damuwa cikin sauƙi

Hanyoyin  rage damuwa cikin sauƙi

Tare da BILKISU YUSUF ALI A rayuwar yau da kullum, kowa na iya fuskantar damuwa ko dai daga aiki,ko  karatu ko  matsin rayuwa, ko wasu ƙalubale na yau da kullum. Damuwa na iya haifar da cututtuka da ruɗani da  rashin bacci wanda kan iya haifar da ciwon zuciya. Amma da zarar an fahimci  hanyoyin magance damuwa  mutum zai iya komawa cikin hayyacinsa  da natsuwa. Hanyoyi biyar da aka tabbatar daga bincike wajen rage damuwa cikin sauƙi: 1. Yin numfashi mai zurfi a hankali Yin numfashi cikin natsuwa ta hanyar shakar iska da hanci, rike shi na ‘yan daƙiƙu, sannan a…
Read More