ukarofi

12715 Posts
Majalisar Dokokin Katsina ta amince da kasafin kuɗin cike giɓi karon farko na shekara ta 2025

Majalisar Dokokin Katsina ta amince da kasafin kuɗin cike giɓi karon farko na shekara ta 2025

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Majalisar ta amince da kasafin kuɗin cike giɓi a karon farko na shekara ta 2025 da ya kai Naira biliyan ɗari da talatin da bakwai da miliyan dari biyar da talatin da tara da dubu ɗari shidda da ashirin da huɗu da naira dari da saba'in da ɗaya da kwabo ashirin da huɗu. Shugaban majalisar Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura ya bayyana haka jim kaɗan bayan amincewa da rahoton kasafin kuɗin da kuma yiwa ƙudurin dokar karatu na uku. Shugaban kwamitin Hon Lawal Yaro ya ce ƙaramin kasafin kuɗin bai canza kasafin kuɗi na 2025.…
Read More
Gudunmawar marubuta ga cigaban ƙasa

Gudunmawar marubuta ga cigaban ƙasa

Daga JIBRIN YUSUF KAILA A yayin da ýan Nijeriya ke cigaba da bayyana farincikinsu da murna albarkacin cika shekaru 65 da samun ýancin kan Nijeriya daga turawan mulkin mallaka na ƙasar Ingila, lallai ya kamata mu tambayi kawunanmu, wacce gudunmawa ce marubuta ya kamata su taka don samar da cigaban ƙasa?  Tabbas muna cikin wani lokaci da Nijeriya ke cikin buki da murna, ya zama wajibi ga kowanne ɗan ƙasa nagari, ya yi nazari da kyau don tunawa da gwagwarmayar da mazan jiya suka yi wajen samar wa ƙasar nan 'yancin kai. Dole mu kasance masu duba abin da ya…
Read More
Kano ta haura zuwa mataki na huɗu daga na 35 a jihohin da suka fi ƙwazo kan aiwatar da dokoki kan sauyin yanayi a Nijeriya

Kano ta haura zuwa mataki na huɗu daga na 35 a jihohin da suka fi ƙwazo kan aiwatar da dokoki kan sauyin yanayi a Nijeriya

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Jihar Kano ta samu babban ci gaba a jerin jihohin da suka fi kula da dokokin sauyin yanayi da ake kira 'Subnational Climate Governance' , inda ta haura daga matsayi na 35 zuwa na 4 a cikin jihohin Najeriya. Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na jihar, Dakta Dahir M. Hashim ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Kano, yana mai cewa wannan nasara ta samo asali ne daga gyare-gyaren gwamnati da ƙarfafa cibiyoyi da kuma shirye-shiryen al’umma da suka gina tsarin kula da sauyin yanayi mai dacewa da…
Read More
NFF ta dakatar da alƙalan wasan da su ka busa wasan Kano Pillars da Shooting Stars

NFF ta dakatar da alƙalan wasan da su ka busa wasan Kano Pillars da Shooting Stars

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Kwamitin alƙali wasa na hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasa NFF ta dakatar da alƙalan wasa guda uku da suka busa wasan Kano Pillars da Shooting Stars na gasar firimiya ta ƙasa, NPFL, wanda aka tashi 1-1 a filin wasa na Sani Abacha da ke jihar Kano. An dakatar da su ɗin ne bisa gaza bin ƙa'idojin busa na ƙasa a wasan na mako na 8, lamarin da ya haifar da rikici bayan an tashi daga wasan. A sanarwar da sakataren kwamitin, Aminu Muhammad, ya sakawa hannu aka rabawa manema labarai , NFF ta dakatar da…
Read More
Sharhin littafin ‘Asalin Labarina’

Sharhin littafin ‘Asalin Labarina’

Daga BAMAI A. DABUWA KKM Sunan Littafi: Asalin Labarina. Marubuci: Ayuba Muhd Danzaki. Shekarar Bugu: 2022. Bugu: AGP Computers Fagge. ISBN: Babu. Shafi: 144. Yanayi: Damina. Jigo: Soyayya da Zamantakewa. Salo: Fagen Waje. Mai Sharhi: Bamai A. Dabuwa Kkm. Gabatarwa/Tsokaci: 'Asalin Labarina', labari ne na wani matashin mai kuɗi Ziya'u wanda ya haɗu da matsalolin rayuwa kala-kala. Matsalolin da idan aka jarrabi jahili da su sai ya ɗaga kai sama da cewa wai me na maka ne? Duk da haka shi ya yi haƙuri, kodayake, ya mutum zai yi da abin da ya fi ƙarfin wuta wai inji kishiyar ƙonanniya.…
Read More
Kotu ta yanke masa hukuncin shekaru 14 bisa yi wa ‘yar shekara 12 fyaɗe a Kano

Kotu ta yanke masa hukuncin shekaru 14 bisa yi wa ‘yar shekara 12 fyaɗe a Kano

Daga USMAN KAROFI a Abuja Wata babbar kotu a Jihar Kano mai lamba 3, ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Farouk Lawan, ta yanke wa wani mutum mai suna Ahmed Muhammed hukuncin ɗaurin shekaru 14 a gidan yari bayan ta same shi da laifin yi wa yarinya ‘yar shekara 12 fyaɗe. Rahotanni sun bayyana cewa an kama wanda ake zargin tun a shekara ta 2006, inda daga baya aka gurfanar da shi a gaban kotu kan wannan zargi. Lauyan gwamnati, Barista Ibrahim Araf Garba, ya gabatar da shaidu huɗu yayin zaman shari’ar, yayin da wanda ake tuhumar ya musanta laifin da ake…
Read More
Sarki Sanusi II ya halarci taron ƙungiyar Injiniyoyi ta duniya a China

Sarki Sanusi II ya halarci taron ƙungiyar Injiniyoyi ta duniya a China

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sanusi II, ya halarci babban taron Ƙungiyar Injiniyoyi ta duniya, wato World Federation of Engineering Organizations (WFEO) 2025, da aka gudanar a birnin Shanghai, ƙasar China, a ranar Litinin, taron ya tattaro manyan masana da shugabanni daga sassan duniya domin tattaunawa kan ci gaban fasaha da injiniyanci a duniya. An gudanar da taron ne ƙarƙashin jagorancin Shugaban WFEO na duniya, Injiniya Mustapha Shehu, wanda ɗan asalin Kano ne. Wannan ya ƙara bai wa taron armashi, duba da yadda ‘yan Najeriya, musamman ƴan Kano, ke taka muhimmiyar rawa a harkar…
Read More
Ma’aikatan Zamfara sama da 3000 da aka dakatar sun gudanar da addu’o’in neman agaji gurin Allah

Ma’aikatan Zamfara sama da 3000 da aka dakatar sun gudanar da addu’o’in neman agaji gurin Allah

By SANUSI MUHAMMAD a Gusau Ɗaruruwan ma'aikatan da gwamnatin Jihar Zamfara ta dakatar da abashin su kimanin watanni Takwas da suka gabata, sun gudanar da addu'a ta musamman don neman agajin gaggawa gurin Allah. Shamsuddeen Muhammad Soja, wanda mataimakin shugaban ƙungiyar ma'aikatan da gwamnatin ta dakatar, a zantawar sa da wakilin mu, ya bayyana cewar, su kimanin 3000 ne matsalar ta shafa . A cewar sa, sunyi duk ƙoƙarin da ya dace Wajen tuntuɓar gwamnatin jihar don kawo ƙarshen matsalar su amma abun ya gagara. Soja ya ƙara da cewar, a ƙarshe sunje ofishin shugaban ma'aikatan jihar, inda ya tabbatar…
Read More
Koya wa mata sana’o’i domin kula da kan su da iyalan su na daga cikin murin mu – Zulai Bebeji 

Koya wa mata sana’o’i domin kula da kan su da iyalan su na daga cikin murin mu – Zulai Bebeji 

"Kungiyar  Matanmu a Yau Organization na da manufofin taimakon mata da yara" DAGA MUKHTAR YAKUBU Masu karatu barkanmu da sake ganin zagayowar sati lafiya, sannunku da jimirin bibiyar jaridar Blueprint Manhaja. A wannan makon shafin Gimbiya zai kawo wa masu karatu rahoto na wata ƙungiya da me rajin kare martabar mata ta hanyar koyar da su sana'o'i domin dogaro da kai. Da kuma tsaya masu a lokacin da suke buƙatar taimako. Hakazalika ƙungiyar ta waiwaye ɓangaren ƙananan yara da sha'anin da ya shafe su. Kamar yadda muka sha faɗa, shafin bai karkata a iya fira da mata kawai ba, maimakon…
Read More
El-Rasheed ya nemi Gwamnatin Tarayya ta sake gyaran hanyar Gombe–Dukku–Darazo

El-Rasheed ya nemi Gwamnatin Tarayya ta sake gyaran hanyar Gombe–Dukku–Darazo

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Dukku/Nafada, Hon. Abdullahi El-Rasheed Bala, ya buƙaci gaggawar shiga tsakani daga gwamnatin tarayya domin gyara da sake gina hanyar Gombe–Dukku–Darazo, wacce ya bayyana a matsayin muhimmiyar hanya ta tattalin arziki da ke haɗa al’ummomi da dama a yankin Arewa maso Gabas. Ɗan majalisar, wanda kwanan nan ya kai ziyarar gani da ido kan hanyar, ya ce manufar wannan ziyara ita ce duba halin da hanyar ke ciki da kuma tattara bayanai kai tsaye domin ƙarfafa tattaunawarsa da hukumomi da cibiyoyin raya yankin da abin ya shafa. Hon. El-Rasheed ya…
Read More