17
Oct
*Ministan Shari’a ya yi ƙarin haske kan yafiyar Tinubu ga wasu fursunonin Nijeriya Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta yi ƙarin hasken cewa, babu wani fursuna da aka saki sakamakon yafiya da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi musu a kwanakin baya lokacin bikin ’Yancin Kai, ciki kuwa har da Maryam Sanda, wacce ta kashe mijinta, Bilyaminu Bello. Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Tarayya, Lateef Fagbemi (SAN), a cikin wata sanarwa jiya Alhamis, yayin da ƙorafi ya yi yawa biyo bayan sakin jerin sunayen mutum 82 da…
