17
Oct
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta bayyana cewa, hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya, ta sauka zuwa kashi 18.02 a watan Satumba, 2025, idan aka kwatanta da kashi 20.12 da aka samu a watan Agusta. A cewar rahoton hukumar, hauhawar farashin kayayyaki gaba ɗaya a watan Satumba ta kasance kashi 0.72, yayin da farashin kayan abinci ya ragu da kashi 1.57, idan aka kwatanta da watan da ya gabata. Ragin na zuwa ne sakamakon saukar farashin kayayyakin abinci kamar masara, garri, wake, gero, dankali, albasa, kwai, tumatir, da barkono. Haka kuma, an bayyana cewa matsakaicin…
