18
Oct
Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ƙaddamar da shirin tallafin karatun ‘yan mata na AGILE tare da tallafin gyaran makarantu (SIGs), domin inganta ilimi da ƙarfafa ‘yan mata a faɗin jihar. An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne a otal ɗin Custodian da ke Gombe, inda mataimakin gwamna, Dakta Manasseh Jatau, ya wakilci gwamnan. Ya bayyana cewa gwamnati na ɗaukar ilimi a matsayin ginshiƙin ci gaban al’umma, musamman wajen bai wa ‘yan mata damar ci gaba da karatu da samun ilimin zamani. “Idan ka ilmantar da ‘ya mace, ka ilmantar da al’umma; idan ka ƙarfafa…
