ukarofi

12715 Posts
 Yadda nake gudanar da sana’ar da mata ke yi a Legas — Babangida Musawa

 Yadda nake gudanar da sana’ar da mata ke yi a Legas — Babangida Musawa

Daga DAUDA USMAN a Legas Shugaban ƙungiyar masu sana’ar sayar da dafaffen abinci a Legas, wato masu tuwo, shinkafa da sauran dangoginsu, Alhaji Babangida Mati Musawa, wanda ke gudanar da sana’arsa a kasuwar Mile 12 International Market a Legas, ya shawarci mata Hausawa da sauran ‘yan ƙungiyarsa su ƙara himma wajen tsaftace abincin da suke girkawa don kare lafiyar masu siya da al’umma baki ɗaya. Alhaji Babangida Mati Musawa, ɗan asalin Jihar Katsina, ya yi wannan jawabi ne a yayin taron wata-wata na ƙungiyar ’Yan Tuwo-Tuwo da aka gudanar a Mile 12, inda suka tattauna kan matsalolin ƙungiyar da hanyoyin…
Read More
M.D na kasuwannin Sabon Gari, Singa da Galadima ya gwangwaje mata 150 da jarin N10,000 kowaccen su

M.D na kasuwannin Sabon Gari, Singa da Galadima ya gwangwaje mata 150 da jarin N10,000 kowaccen su

Daga RABIU SANUSI a Kano Shugaban kasuwannin Sabon Gari, Singa da Galadima, Alhaji Abdul Bashir ya raba wa mata kimanin ɗari da hamsin jarin dubu goma-goma ga kowaccensu. A jawabin shi, Manajan Daraktan kasuwannin Sabon Gari, Galadima Alhaji Abdul Bashir ya ce yana ƙara godiya ga Allah bisa wannan nasarar ta yau da ya yi namijin ƙoƙarin. Shugaban rukunin kasuwannin ya ce wannan tunani na yau na da nasaba da irin ƙoƙarin mata bisa riƙe amana da jajircewa da suke da shi a dukkan rayuwar. Yace wannan karon sun ɗauko mata 150 don basu wani ɗan tallafi wanda ba shi…
Read More
Daliban Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko ɗangote da ke Wudil sun karrama MD KAROTA

Daliban Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko ɗangote da ke Wudil sun karrama MD KAROTA

Daga RABIU SANUSI a Kano Wasu ɗaliban Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko ɗangote da ke Wudil a Jihar Kano sun karrama Manajan Darakta na KAROTA, Dr. Faisal Mahmud Kabir da shaidar girmawa. ɗaliban waɗanda sukekKaratun Digiri na Part Time sun yi wannan yunƙurin ne ganin irin hidimar da Manajan Daraktan hukumar ta KAROTA yake wajen tallafawa ilimi a faɗin Jihar Kano. Da yake ƙarin bayani , Shugaban ƙungiyar ɗaliban Jami'ar Kwamared Ibrahim Shafir Hashim ya ce wannan ziyara na da nasaba da irin ƙoƙarin Shugaban na KAROTA wajen tallafawa ɗalibai daga makarantu daban-daban. Kwamared Ibrahim Shafir ya cigaba da…
Read More
Muna ci gaba da gamsuwa da jagorancin Alhaji Shehu Samfam a Legas — Alhaji Mukhtar Jabo

Muna ci gaba da gamsuwa da jagorancin Alhaji Shehu Samfam a Legas — Alhaji Mukhtar Jabo

Daga DAUDA USMAN a Legas Daya daga cikin shugabannin manyan ɓangarorin kasuwar Mile 12 International Market da ke birnin Legas, Alhaji Mukhtar Jabo, wanda shi ne shugaban ɓangaren kasuwancin busasshen barkono, ya bayyana cewa su da sauran shugabannin sassa daban-daban na kasuwar suna ci gaba da gamsuwa da irin jagorancin da babban shugaban kasuwar, Alhaji Shehu Usman Jibrin Samfam (Sardaunan Abeokuta), ke bayarwa. Alhaji Mukhtar Jabo, ɗan asalin Jihar Jigawa kuma mazaunin unguwar Mile 12 a Legas, ya ce ba bu shakka cewa jagorancin Alhaji Shehu Samfam ya kawo sabuwar rayuwa da ci gaba a kasuwar Mile 12, wanda hakan…
Read More
‘Yan bindiga sun kai hari a Kankiya duk da sulhun da aka yi da su a yankunan Jihar Katsina

‘Yan bindiga sun kai hari a Kankiya duk da sulhun da aka yi da su a yankunan Jihar Katsina

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Dandazon ’yan bindiga kimanin 100 a kan babura sun kai hari a yankin Kankiya da ke Jihar Katsina inda suka halaka mutum ɗaya tare da jikkata wasu da dama. Shaidu sun ce ’yan bindiga sun kai harin a yankin Kwadawa da ke Gundumar Gashi da ke ƙaramar Hukumar Kankiya, inda ake Ana zargin maharan sun kai harin ɗaukar fansa ne. Maharan da suka kai farmaki a yankin da ke Gabahsin ƙaramar hukumar, sun sace dabbobi da ba a san adadinsu ba, suna masu barazanar halaka duk mutanen yankin. Wakilinmu ya ruwaito cewa a halin…
Read More
Samun kiredit a Turanci ko Lissafi ba wajibi ba ne ga masu neman gurbin karatu a jami’a – Minista

Samun kiredit a Turanci ko Lissafi ba wajibi ba ne ga masu neman gurbin karatu a jami’a – Minista

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin tarayya ta sanar da wani sabon tsari da zai bai wa ɗalibai damar shiga manyan makarantu ba tare da wajibcin samun Lissafi ko Turanci a WAEC ko NECO. Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwar da ma’aikatar ilimi ta Nijeriya ta fitar mai ɗauke da kwanan watan 13 ga watan Oktobar 2025. Sabuwar dokar, wacce Ministan Ilimi, Maruf Tunji Alausa, CON, ya gabatar, ya ce, wani mataki ne shirin sabunta fatan al’umma da bai wa kowa damar samun ilimi. Alausa ya ce, la’akari da cewa a kowacce shekara akan samu ɗalibai sama da…
Read More
Amnesty ta nemi Tinubu ya soke yafiyar da ya yi wa waɗanda su ka aikata manyan laifuka 

Amnesty ta nemi Tinubu ya soke yafiyar da ya yi wa waɗanda su ka aikata manyan laifuka 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Kungiyar rajin kare haƙƙin ɗan Adam, Amnesty International ta bayyana damuwa kan afuwar da Shugaba Bola Tinubu ya yi a kwanan nan, inda ta buƙaci gwamnati da ta sake duba matakin. A ranar Alhamis da ta gabata, Tinubu ya bayar da afuwa ta shugaban ƙasa ga ɗaya daga cikin jagororin da su ka kafa Nijeriya, Herbert Macaulay, da kuma tsohon ministan babban birnin tarayya a zamanin mulkin Babangida, Manjo Janar Mamman ɓatsa (ritaya), da Maryam Sanda da aka yanke wa hukuncin kisa sakamakon kashe mijinta da ta yi da sauran wasu mutane 172. Sai…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta kafa gidan rediyo na manoma

Gwamnatin Katsina za ta kafa gidan rediyo na manoma

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Kwamishinan ma'aikatan gona Farfesa Ahmad Muhammad Bakori ya sanar da haka a hira da manema labarai kan ziyarar aiki da mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima zai kawo a Katsina mako mai zuwa. Mataimakin shugaban ƙasar zai kawo ziyarar aiki na kwana biyu inda zai jagoranci buɗe taron hukumar bunƙasa ƙanana da matsakaitan sana'o'i SMSE ta ƙasa a Katsina. Zai kuma ƙaddamar da wasu ayyuka na bunƙasa ƙasa da gwamnatin Dikko Raɗɗa ta aiwatar. Farfesa Bakori ya ce mazaunin gidan rediyon zai kasance a cibiyar kula da manoma da aka kammala gina wa, ana sa…
Read More
Gwamna Lawal ya mayar da malaman makaranta 103 da aka kora bakin aiki

Gwamna Lawal ya mayar da malaman makaranta 103 da aka kora bakin aiki

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da mayar da malaman makaranta 103 da aka kora don su koma makarantun da suke koyarwa ba tare da ɓata lokaci ba. Kwamishinan ilimi, kimiyya da fasaha na jihar, Alh. Wadatau Madawaki ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishin sa a yau Juma’a. A cewarsa, gwamnan ya umurci ma’aikatarsa da ta biya dukkan albashin su na watanni bakwai daga watan Janairu zuwa Yuli na wannan shekara. Madawaki ya bayyana cewa malaman da abin ya shafa na daga cikin malamai 780 da kwamitin…
Read More
Yadda afuwar da Tinubu ya yi wa wasu masu harƙallar miyagun ƙwayoyi ta bar baya da ƙura

Yadda afuwar da Tinubu ya yi wa wasu masu harƙallar miyagun ƙwayoyi ta bar baya da ƙura

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Matakin da Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ɗauka na yin afuwa ga mutane kusan 50 da aka yanke wa hukunci sakamakon laifuka na miyagun ƙwayoyi ya bar baya da ƙura a yayin da wasu ke gargaɗin cewa matakin na aika wani saƙo marar fasali game da yakin da Nijeriya ke yi da miyagun ƙwayoyi. Mutane 50 ɗin na cikin jumullar fursunoni 175 da suka rabauta da afuwar da majalisar bai wa shugaban ƙasa shawara a ranar Alhamis ɗin da ta gabata. Mafi yawan waɗanda aka yafewa cikin 50 ɗin nan an same su da…
Read More