03
Oct
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Kiyaye Haɗura ta ƙasa FRSC ta bayyana yadda wasu direbobi masu tuƙin ganganci a watan Satumba 2025 suka kashe jami’an hukumar biyar yayin da suke kan aikinsu. Bisa ga takardar da jami’in wayar da kan jama’a na Hukumar Olusegun Ogungbemide ya fitar ranar Talata ya nuna cewa hakan ya faru ne a sassa biyar na Hukumar da ke faɗin ƙasar nan a tsakanin wata ɗaya. Ya ce sassa da ranakun da jami’an hukumar suka gamu da ajalin sun haɗa fa ranar 6 ga Satumba a Ekiti, ranar 8 ga Satumba a sannan Ogun,…
