ukarofi

12735 Posts
NAPTIP ta kama mahaifi na ƙoƙarin safarar ’yarsa zuwa Iraƙi don ci-rani

NAPTIP ta kama mahaifi na ƙoƙarin safarar ’yarsa zuwa Iraƙi don ci-rani

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane ta ƙasa (NAPTIP) ta ce ta kama aƙalla mutane biyar da ake zargi da safarar mutane tare da ceto mutane 24 a Filin Jirgin Sama na ƙasa Nnamdi Azikiwe, Abuja. Hukumar ta ce daga cikin waɗanda aka cafke ɗin, har da wani uba da ya yi ƙoƙarin safarar ɗiyarsa zuwa Baghdad, babban birnin ƙasar Iraƙ. Jami’in Yaɗa Labarai na NAPTIP, Vincent Adekoye, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba. Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan…
Read More
Shugaban APC ya alaƙanta talauci da silar ta’addanci a Nijeriya 

Shugaban APC ya alaƙanta talauci da silar ta’addanci a Nijeriya 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana talauci a matsayin babbar matsalar ta'addanci, da garkuwa da mutane, da rashin tsaro a Nijeriya. Yilwatda ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a wajen bikin cika shekaru 20 da lambar yabo ta ƙungiyar reshen jihar Filato a kasar Amurka (PSA-USA), wanda aka gudanar a ranar Laraba a birnin Lanham na jihar Maryland. Taron ya kasance mai taken “Rage talauci: Hanya zuwa zaman lafiya.” Yayin da yake bayyana talauci a matsayin “dodo mai kai da ruwa” da gwamnati ke yaki da shi,…
Read More
Dalibin Jami’ar Bayero na daf da karɓe kambun ‘Guinness’ a fannin fentin fuskar mutum

Dalibin Jami’ar Bayero na daf da karɓe kambun ‘Guinness’ a fannin fentin fuskar mutum

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano  Wani ɗalibin Jami’ar Bayero mai suna Collins Whitworth, ya yi ƙoƙarin shiga kundin tarihin duniya na Guinness a fannin fentin fuska mafi yawa cikin minti uku. Da goyon bayan kamfanin Indomie, Collins ya fente fuskar mutum 17 a cikin ƙasa da minti 3, lamarin da ya karya kambun da Emilia Zakonnoɓa ta kafa na fentin fuskar mutum 12 a ranar 30, ga Yuli, 2025. An gudanar da taron sanya fentin ne a ranar Laraba, a harabar sabuwar Jami’ar Bayero da ke Kano.  Ga yadda sakamakon yunƙurin shiga kundin tarihin nasa ya kasance:   Gwaji na 1:…
Read More
Ambaliya: Neja ta umarci mazauna wasu yankuna su janye jikinsu 

Ambaliya: Neja ta umarci mazauna wasu yankuna su janye jikinsu 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin Jihar Neja ta gargaɗi mazauna wasu yankuna da ke bakin Kogin Neja da Kogin Kaduna da su koma wuraren da suka fi aminci bayan an fara sakin ruwa daga manyan dam-dam na ruwa a jihar. Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ce ta fitar da wannan gargadi a cikin wata sanarwa da Darakta-Janar ɗinta, Abdullahi Baba-Arah, ya sanya wa hannu a ranar Alhamis. Baba-Arah ya bayyana cewa lamarin ya biyo bayan sakin ruwa da ake yi daga dam-dam na Kainji, Shiroro, Zungeru, da Jebba. A cewarsa, "Ma’aikatar Kula da Ruwa…
Read More
Hukumar Raya Kogunan Hadeja da Jama’are ta yi bikin Ranar Koguna ta Duniya

Hukumar Raya Kogunan Hadeja da Jama’are ta yi bikin Ranar Koguna ta Duniya

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano Ranar Lahadin ƙarshen watan Satumba ce ranar da Majalisar ɗinkin Duniya ta ware, domin bikin Ranar Kogunan Duniya, domin wayar da kan jama’a kan muhimmancin koguna da ƙoramai ga cigaban al’umma. A wannan rana hukumomin ruwa, masana’antu da ƙungiyoyi masu kula da muhalli kan gudanar da bukukuwa, domin ƙara ilimantar da jama’a kan kula da lafiyar koguna. A bana, Hukumar Kula da Raya Kogunan Haɗeja da Jama’are ta shirya taron faɗakarwa a Fadar Koma da ke ƙaramar Hukumar Wudil a Jihar Kano, inda aka gabatar da lakcoci da tattaunawa kan alfanun koguna. Shugaban hukumar,…
Read More
Gwamna Fubara ya sauke dukkan kwamishinoni a Ribas

Gwamna Fubara ya sauke dukkan kwamishinoni a Ribas

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya kori dukkanin kwamishinoni da sauran jami’an gwamnati da ke aiki ƙarƙashin gwamnatinsa. Wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Nelson Chukwudi, ya fitar a birnin Fatakwal a daren Laraba ya bayyana cewa wannan mataki ya fara aiki nan take. An yi sallamar ne saboda hukuncin Kotun ƙoli da ya shafi dukkanin kwamishinonin da sauran jam'an da ya kora. Gwamna Siminalayi Fubara ya sallami jami'an gwamnatinsa ne a lokacin Bikin Ranar ’Yancin Nijeriya. Sanarwar da Nelson Chukwudi ya fitar ta ce, “Gwamna ya sallami dukkanin kwamishinoni da sauran jami’an gwamnati da…
Read More
Tsaikon diflomasiyya ya sa ’yan Nijeriya 270 zaman gidajen yarin Habasha

Tsaikon diflomasiyya ya sa ’yan Nijeriya 270 zaman gidajen yarin Habasha

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Darurruwan 'yan Nijeriya ne ke ci gaba da zama gudajen yarin ƙasar Habasha a cikin mawuyacin hali yayin da yarjejeniyar fahimtar juna ta diplomasiyya da aka daɗe ana jira tsakanin ƙasashen biyu na fuskantar tsaiko. Yayin da yake magana a ranar Laraba, ƙaramar Ministan Harkokin Waje, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, ta tabbatar da cewa Nijeriya ta kammala dukkan ƙa’idojin da suka dace amma ta zargi Habasha da yin jinkiri wajen aiwatarwa. "Ma'aikatar ta cika nata ɓangaren na ƙa'idojin miƙa waɗanda aka yanke wa hukunci. ɓangaren Habasha ne ke jinkiri," inji ta a wata sanarwa da mai taimaka…
Read More
Fashi: Yadda ’yar jarida ta rasa ranta sakamakon tsirgowa daga bene hawa uku a Abuja

Fashi: Yadda ’yar jarida ta rasa ranta sakamakon tsirgowa daga bene hawa uku a Abuja

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kwamishinan 'yan sanda na Babban Birnin Tarayya Abuja, CP Ajao Adewale, ya tabbatar da cewa Somtochukwu Maduagwu, ’yar jaridar gidan talbijin na Arise News ta rasa ranta ne bayan ta faɗo daga hawa na uku na gidanta a wani hari da wasu ‘yan fashi da makami suka kai a Katampe, Abuja. An bayar da rahoton cewa, lamarin mai ratsa zuciya ya afku ne da sanyin safiyar ranar Litinin a Unique Apartments, wani tagwayen bene mai hawa uku mai ɗauke da gidaje 18 da ke yankin Katampe a ƙarƙashin yankin Mabushi. Yayin da ya ke magana a…
Read More
Tura matan shugabannin ƙananan hukumomin Adamawa horo Turkiyya ya janyo cece-kuce

Tura matan shugabannin ƙananan hukumomin Adamawa horo Turkiyya ya janyo cece-kuce

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Tura matan shugabannin ƙananan hukumomi 21 na Jihar Adamawa birnin Istanbul na ƙasar Turkiyya, domin halartar taron horarwa na mako guda kan jagoranci da cigaban al’umma ya janyo cece-ku-ce, inda ma'aikata, ’yan fansho, da ƙungiyoyin farar hula suka bayyana matakin a matsayin rashin hankali, almubazzaranci, da kuma cin zarafin al'umma. An rawaito cewa, wannan tafiya mai cike da cece-ku-ce da rahotanni suka ce ta haɗa da wasu manyan jami'an ma'aikatar ƙananan hukumomi, ta haifar da fushi a jihar da tuni ke fama da matsalar bashin fansho, da rashin biyansu haƙƙoƙinsu, da kuma taɓarɓarewar tattalin arziki, inda…
Read More
Shekaru 65 da ‘yanci: Daga yanzu wahala ta ƙare – Tinubu

Shekaru 65 da ‘yanci: Daga yanzu wahala ta ƙare – Tinubu

*Cikin shekaru biyu mun samu gagarumin cigaba, inji Shugaban ƙasa *Yunwa na kashe ’yan Nijeriya, amma ko a jikin Tinubu – Atiku *Kada ku yanke ƙauna da cigaban ƙasa – Jonathan ga 'yan Nijeriya *Akwai buƙatar kishin ƙasa da haɗin kan al’umma, inji Sarkin Kasuwar Beirut Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce, gwamnatinsa ta samu gagarumin cigaba a fannoni daban-daban cikin shekaru biyu da suka gabata, duk da ƙalubalen tattalin arziki da tsaro da ƙasar ta fuskanta. A jawabin da ya gabatar yayin bikin cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai, Shugaba…
Read More