ukarofi

12735 Posts
Yan bindiga sun sace kansiloli biyu a Zamfara

Yan bindiga sun sace kansiloli biyu a Zamfara

‘ Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau A ranar Laraba ne wasu ‘yan bindiga suka sace wasu kansilolin ƙaramar hukumar Maradun guda biyu a Zamfara. Rahotanni sun nuna cewa an yi garkuwa da Kansilolin guda biyu masu wakiltar Gidan Goga da Tsibiri a ƙaramar hukumar Maradun a Unguwar Mareri da ke Gusau babban birnin jihar. Wakilinmu ya ruwaito cewa an yi garkuwa da Kansilolin biyu ne a ƙofar gidajen su dake unguwar ta Mareri da misalin karfe 6:50 na yammacin ranar Laraba. A yayin da Wakilin mu ya tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar DSP Yazid Abubakar…
Read More
Sulhu da yan bindiga a mulkin Dikko Raɗɗa, Mustapha Inuwa ba shi da bakin magana

Sulhu da yan bindiga a mulkin Dikko Raɗɗa, Mustapha Inuwa ba shi da bakin magana

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Mai ba gwamna shawara kan harkokin jam'iyyun siyasa a Katsina Malam Shafi'u Ruwan ya ce 'yan bindiga ne suka nemi sulhu da al'ummomin yankunan da ke fama da rashin tsaro,saɓanin lokacin gwamnatin baya da Mustapha Inuwa ya riƙe muƙamin sakataren gwamnati. Duwan na mai da martani ne kan maganar da madugun jam'iyar ADC a Katsina Mustapha Inuwa wanda ya soki yadda ake gudanar da sulhu da 'yan bindiga ba tare da sun ajiye makami ba. Ya ce ƙananan hukumomi 8 da suka rungumi sulhu da yan bindigan,"Su yan bindigan suka buƙaci haka, sabanin gwamnatin su…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya amince da samar da cibiyar kula da ciwon daji a Katsina

Gwamna Raɗɗa ya amince da samar da cibiyar kula da ciwon daji a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan ya amince da hakan ne lokacin da tawagar likitoci daga ƙasar Masar "Egypt" suka kawo mashi ziyarar ban kwana, bayan sun duba wuraren da ake shirin gina cibiyar lafiya ta zamani a jihar Katsina. Tawagar ta yaba da jajircewar gwamnatin jihar wajen inganta kiwon lafiya, musamman shirin gina cibiyar kula da cutar daji da sauran fannoni na musamman. Likitocin kuma sun bada shawarar a samar da cibiyar a tsohon ginin Katsina City Mall, kuma gwamnan ya amince . Gwamna Raɗɗa ya tabbatar da shirin sa na haɗin gwiwa da likitocin don tabbatar da wannan…
Read More
Jami’ar ABU sadaka mai wanzuwa ga gamji!

Jami’ar ABU sadaka mai wanzuwa ga gamji!

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Bayan bawa ya koma ga Allah bias koyarwar addinin Islama da Firimiya Sir Ahmadu Bello ya koma ga Allah a kai, duk ayyukan sa na lada sun yanke sai sadaka mai wanzuwa da su ka hada da kafa wani abu na alheri da mutane su ke cin moriyarsa. Aƙalla a ce ka dasa bishiya ko ka tona rijiya da bayan baka nan mutane su ke cin moriya to za ka cigaba da samun lada. Firimiya ya jagoranci shuka alheri a lokacin rayuwar sa ya jajirce wajen kafa jami’ar ABU a Zaria da manufar al’ummar da za…
Read More
Nazari littafin ‘Baba Zube’ na 5 (Gwamnati)

Nazari littafin ‘Baba Zube’ na 5 (Gwamnati)

"Littafi 'Baba Zube' ya haska wa makaranta yadda gwamnati ke amfani da jami'an tsaro wajen daƙile barazana" Daga SALIHU ISHAK IBRAHIM MAKERA  Mawallafi: Khadi Muhammad Uthman El-Mainari Madaba'a: Gaskiya Corporation Limited, Zariya Shekarar Dab'i: 2025 Yawan Shafuka: 145 Farashi: Ba a ambata ba. Manazarci: Salihu Ishaƙ Ibrahim Maƙera A karo na biyar yau na ke gabatar da nazari kan jerin littattafan da Mai Shari'a, Khadi Muhammad Uthman El-Mainari na Kotun ɗaukaka ƙara ta Shari'ar Musulunci da ke a Jihar Bauchi yake wallafawa a salon bayar da labari irin na 'Magana Jari Ce' na marigayi Malam Abubakar Imam.  A baya mun…
Read More
NUJ ta buƙaci ’yan jarida su mayar da hankali kan lalubo mafita wajen warware matsalolin Arewacin Najeriya

NUJ ta buƙaci ’yan jarida su mayar da hankali kan lalubo mafita wajen warware matsalolin Arewacin Najeriya

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban Ƙungiyar ’yan jarida ta ƙasa (NUJ), Kwamared Alhassan Yahya Abdullahi, ya yi kira ga ’yan jarida su rungumi aikin jarida a matsayin mafita ko hanyar shawo kan matsalolin da ke addabar Arewacin Najeriya. Dr Al Hassan ya yi wannan kira ne a wajen taron cika shekara 38 da ƙirƙiro, jihar Katsina wanda aka gudanar a Hayatt Regency Suite bisa jagorancin ƙungiyar NUJ ta Jihar Katsina. Abdullahi ya bayyana damuwa kan matsalolin ilimi, kiwon lafiya, da talauci da ke ƙara taɓarɓarewa a jihohin Arewa, inda ya ambaci yawaitar yaran da ba sa zuwa makaranta, matsalar…
Read More
Shugaban ƙaramar hukumar Gombe zai mayar da yara 1,000 makaranta

Shugaban ƙaramar hukumar Gombe zai mayar da yara 1,000 makaranta

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Shugaban ƙaramar hukumar Gombe, Barista Sani Ahmad Haruna, ya bayyana shirin mayar da yara 1,000 da ba sa zuwa makaranta kafin ƙarshen watan Oktoba na bana. Ya ce za a yi musu rijista tare da samar da jakunkuna, littattafai da sauran kayan karatu domin inganta iliminsu da kuma sauƙaƙa wa iyaye nauyin da ke kan su. Barista Sani ya bayyana haka ne a wani taro da aka gudanar domin rarraba kayan makaranta ga ɗaruruwan yara a cikin ƙaramar hukumar, abin da ya kawo farin ciki da kwarin gwiwa ga iyaye da malamai. Ya ce…
Read More
Ya kamata zaman lafiya da adalci su zama gadon Nijeriya, inji Jakadiya Fatima Paga

Ya kamata zaman lafiya da adalci su zama gadon Nijeriya, inji Jakadiya Fatima Paga

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Yayin da Najeriya ke murnar cikar ta shekaru 65 da samun ‘yancin kai, jakadiya Fatima M. Paga, wakiliyar UN Women ga gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ta yi kira da a mayar da zaman lafiya da adalci ginshiƙin rayuwa da gadon ƙasa. A wani saƙo na musamman na ranar ƙasa, Jakadiya Paga ta ce akwai buƙatar shugabanni su tashi tsaye wajen fitar da manufofi masu ma’ana, domin sauya halin da al’umma ke ciki, musamman a Arewa maso Gabas inda ake fama da tsaro da bala’o’in yanayi. “Na shaida da idona yadda mutane ke…
Read More
Bai kamata a yi sulhu da ’yan bindiga ba tare da sun miƙa makamansu ba – Mustapha Inuwa

Bai kamata a yi sulhu da ’yan bindiga ba tare da sun miƙa makamansu ba – Mustapha Inuwa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Jagoran adawa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a Jihar Katsina, Mustapha Muhammad Inuwa, ya bayyana damuwarsa kan tsarin sulhu da ’yan ta’adda ba tare da an karɓi muggan makaman da ke hannun su ba. Ya ce hakan na barazana ga zaman lafiyar al’umma duba da irin ayyukan ta’addanci da suke ci gaba da yi, ciki har da kisan mutane, garkuwa da su domin neman kuɗin fansa, satar dabbobi da kuma ƙona kadarorin gwamnati da na jama’a a cewar Mustapha Inuwa. A wata hira da manema labarai a Katsina,Inuwa ya ce sulhun ba zai amfani…
Read More