01
Oct
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina An buƙaci majalisar zartaswa ta gyara hanyar Marabar Ɗan Ali, Ɗan Ali, Dangani, Kwanar Gwarjo zuwa cikin garin Musawa, dukkansu dake cikin ƙaramar hukumar Ɗanmusa da Musawa. Yan majalisar dokoki da ke wakiltar ƙananan hukumomin Ɗanmusa da Musawa Hon. Aminu Garba Sai Baba, Musawa Hon. Lawal H. Yaro Away, Su ka gabatar da kudirin buƙatar gyara hanyar, a zaman majalisar ƙarƙashin jagorancin Kakakin majalisar Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura. Da yake gabatar da jawabinsa, yayin da yake gabatar da ƙudirin, ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Musawa Hon. Lawal H. Yaro Away ya bayyana cewa"…
