29
Sep
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta ce, Tattalin Arzikin Nijeriya ya ƙaru da kashi 4.23 cikin ɗari a darajar GDP a zango na biyu na shekarar 2025 idan aka kwatanta da shekarar 2024. Hukumar ta bayyana haka ne a cikin rahoton GDP na Nijeriya na zango na biyu na shekarar 2025 da ta fitar a Abuja a ranar Litinin. Rahoton ya nuna cewa wannan ci gaban ya fi kashi 3.48 da aka samu a zango na biyu na 2024, haka kuma ya fi kashi 3.13 da aka samu a zangon farko na 2025. A cewar rahoton,…
