ukarofi

12735 Posts
Majalisar Dokokin Ribas ta ƙuduri aniyar binciken kantoman riƙo Ibok-Ete Ibas

Majalisar Dokokin Ribas ta ƙuduri aniyar binciken kantoman riƙo Ibok-Ete Ibas

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Wani sabon rikici na neman kunno kai a jihar Ribas da ke Kudu maso Kudancin Nijeriya, bayan da 'yan majalisar dokokin jihar suka ƙuduri aniyar gudanar da bincike kan harkokin kuɗi na gwamnatin a tsawon watanni shida ƙarƙashin jagorancin ɓice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), da ya jagoranci jihar bayan Shugaba Tinubu ya kafa dokar ta-ɓaci a jihar. Ana ganin cewa matakin da 'yan majalisar suka ɗauka zai iya janyo takun saƙa tsakaninsu da tsohon kantoman riƙo na jihar, wanda a halin yanzu ake bin bahasin aikinsa. Majalisar ta jaddada cewa huruminta ne ta…
Read More
‘Yan Nijeriya ba za su sake zaɓenka ba, PDP ta buƙaci Tinubu ya shirya miƙa mulki a 2027

‘Yan Nijeriya ba za su sake zaɓenka ba, PDP ta buƙaci Tinubu ya shirya miƙa mulki a 2027

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam’iyyar PDP ta yi kira ga Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya fara shirya takardar miƙa mulki, inda ta dage cewa ‘yan Nijeriya ba za su mayar da shi kan karagar mulki ba a 2027. Da yake jawabi a sakatariyar jam’iyyar PDP a jihar Yola a ranar Juma’a, sakataren ƙungiyar na jihar Adamawa, Hamza Madagali, ya ce jama’a sun daina hakuri da gwamnati mai ci. Ya zargi jam’iyyar All Progressiɓes Congress (APC) da rashin hangen nesa da alƙibla, yana mai bayyana manufofinta a matsayin “maƙiyar mutane da tattalin arziki.” "'Yan Nijeriya a shirye…
Read More
Za mu maye gurbin Abdulmumin Jibrin da ɗan takara mai ƙarfi a 2027, Kwankwaso ga magoya bayansa

Za mu maye gurbin Abdulmumin Jibrin da ɗan takara mai ƙarfi a 2027, Kwankwaso ga magoya bayansa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar New Nigeria People’s Party, NNPP, a zaɓen 2023, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi watsi da korar Abdulmumin Jibrin daga jam’iyyar, inda ya yaba wa reshen jihar Kano kan wannan mataki. Manhaja ta tuna cewa a wata hira da ya yi da wata kafar yaɗa labarai ta yanar gizo, DCL a kwanakin baya, Mista Jibrin ya fito fili ya bayyana aniyarsa ta ficewa daga jam’iyyar NNPP. Sakamakon haka, a ranar 6 ga watan Satumba, shugaban NNPP na jihar, Hashimu Dungurawa, ya sanar da korar Mista Jibrin a wani taron…
Read More
Shawarwari ga matasa masu shirin aure (2)

Shawarwari ga matasa masu shirin aure (2)

Assalamu alaikum, kamar yadda muka faɗa a makon da ya gabata cewa, za mu cigaba daga inda muka tsaya. Abu na biyu da zan gaya muku shi ne yana da kyau ku fahimci cewa waɗannan abubuwa ba a samunsu haka kawai, wato ba sa samun mutum haka kawai, dole ne ku yi ƙoƙari wajen samar da su. Hanyar samar da su kuwa ita ce dukkan ma'auratan su so junansu. Wataƙila ku tambaya ta ya ya? Kamar yadda ake cewa ne, "ba a iya tabbatar da so da ƙauna ta hanyar ƙarfi da tursasawa", lalle haka ne don kuwa so kamar…
Read More
Magance matsalar tsaro

Magance matsalar tsaro

Mu na ƙara ba gwamnatoci shawara dangane da samun tubka da warwara ta fuskar magance matsalar tsaro. Tabbas wasu rahotanni da daɗin ji domin ana samun nasarori kamar hallaka jagororin Boko Haram, Abubakar shekau, da miƙa wuyan wasu dubban mabiyansa. Haka rahoton hallaka jagoran ISWAP Albarnawi da kuma wanda aka naɗa magajinsa, baya ga hallaka mutane kamar Buharin Daji da Awwalun Daudawa duka nasara ce. Abun mamaki daban tsoro yadda a makon ƙarshe na wancen wata Oktoba aka samu gano wata maƙera ta bindiga ƙirar AK-47 a Jos da ke Jihar Filato, haka a wata arangama jami'an tsaro a Jihar…
Read More
Halin da nake ciki bayan damfara ta kuɗin zuwa asibiti – Jaruma Halisa Muhammad 

Halin da nake ciki bayan damfara ta kuɗin zuwa asibiti – Jaruma Halisa Muhammad 

Daga MUKHTAR YAKUBU Tun bayan fitar labarin damfarar da wani mai suna Bashir ya yi wa Jaruma Halisa Muhammad kan tafiyar ta zuwa ƙasar Saudi Arabia neman magani a kwanakin baya, jama'a suka zuba ido su ga irin matakin da hukumomi da sauran al'umma za su bi domin kwato wa wannan marar lafiya Halisa Muhammad da take cikin mawuyacin hali domin a ceto rayuwarta. Wannan hali da baiwar Allah Halisa Muhammad ta shiga ya taɓa ziciyar mutane, saboda tsawon lokaci da ta shafe cikin rashin lafiya da kuma neman taimakon yadda za ta ceto rayuwarta. A daidai lokacin da damar…
Read More
Hattara da sojojin waya, masu fushi da fushin wani

Hattara da sojojin waya, masu fushi da fushin wani

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Na san mai yiwuwa taken rubutun nan zai bai wa wani dariya. ƙila ma wani ya tambayi ko su waye kuma sojojin waya? To, in dai ka san su waye ake nufi da Sojojin Baka, ba za ka kasa gane Sojojin Waya ba. Kamar yadda aka san Sojojin Baka da shiga tashoshin rediyo suna sayen fili don kare muradun wasu ko cin mutuncin wasu abokan hamayyar ubangidansu na siyasa, don ƙara angiza wutar adawa ko son a sani. Haka su ma sojojin waya suke yin nasu yaƙin ta zaurukan sada zumunta, suna rubuce-rubuce na ɓatanci ko…
Read More
Gwamnatin Katsina ta raba tallafi ga mutane 600 da ambaliya ta shafa a Kankiya

Gwamnatin Katsina ta raba tallafi ga mutane 600 da ambaliya ta shafa a Kankiya

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugabar hukumar agajin gaggawa SEMA Hajiya Binta Hussaini Dangani ta jagorancin ƙaddamar da raba kayan tallafin a ƙaramar hukumar Kankya. Kayan tallafin ya haɗa da nau'in abinci da kuma kayan kwanciya gami da sauran kayan amfanin yau da kullum, da suka haɗa da, shinkafa, masara, gero, dawa, katifa, tabarma, bargo, magi, gishiri da kuma man gyada. Da ta ke gabatar da jawabinta yayin da ta ke ƙaddamar da tallafin, shugabar hukumar Haj. Binta Husaini Dangani ta bayyana cewa tallafin ya samu ne bisa umarnin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa domin a rage raɗaɗi ga…
Read More
2027: Ƙungiyar APC a Zamfara ta amince da Matawalle a matsayin ɗan takarar gwamna

2027: Ƙungiyar APC a Zamfara ta amince da Matawalle a matsayin ɗan takarar gwamna

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Gamayyar ƙungiyar siyasa ƙarƙashin jam'iyyar APC reshen Jihar Zamfara da aka fi sani da Talban Anka Coalition ta amince da ƙaramin ministan tsaro Hon. Bello Mohammed Matawalle ya zama ɗan takarar gwamna a zaɓen 2027 a jihar. Shugaban ƙungiyar kuma tsohon kwamishinan filaye da gidaje Hon. Sharu Dan Sarki ya bayyana haka a yayin wani taro da aka gudanar a babban masaukin baki da ke Gusau "Command Guest Inn" yau Asabar. Ya bayyana cewa ƙungiyar a shirye take ta marawa Matawalle baya domin ya zama Gwamnan Zamfara na gaba a zaɓen 2027. Dan Sarki ya…
Read More
Ku na shan wahala ne sakamakon tiyatar da mu ke yi wa Nijeriya – Tinubu

Ku na shan wahala ne sakamakon tiyatar da mu ke yi wa Nijeriya – Tinubu

Daga USMAN KAROFI a Abuja Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa matsalolin tattalin arzikin da ‘yan Najeriya ke fuskanta sakamakon wasu sauye-sauyen da gwamnatinsa ta aiwatarwa ne. Ya bayyana cewa wannan yanayi ya damu ne saboda tiyata da gwamnatin sa ke yi wa tattalin arzikin ƙasar.Tinubu ya ce wannan wahala da ake ciki ba za ta dawwama ba domin tattalin arzikin ƙasar ya fara murmurewa daga matsalolin da ya faɗa, inda ya gode wa ‘yan ƙasa bisa haƙuri da juriyar da suka nuna. Tinubu ya yi wannan bayani ne a ɗakin taro na Mapo Hall dake Ibadan, Jihar…
Read More