Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar New Nigeria People’s Party, NNPP, a zaɓen 2023, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi watsi da korar Abdulmumin Jibrin daga jam’iyyar, inda ya yaba wa reshen jihar Kano kan wannan mataki.
Manhaja ta tuna cewa a wata hira da ya yi da wata kafar yaɗa labarai ta yanar gizo, DCL a kwanakin baya, Mista Jibrin ya fito fili ya bayyana aniyarsa ta ficewa daga jam’iyyar NNPP.
Sakamakon haka, a ranar 6 ga watan Satumba, shugaban NNPP na jihar, Hashimu Dungurawa, ya sanar da korar Mista Jibrin a wani taron manema labarai a Kano, saboda yadda ya yi ta cece-kuce a kafafen yaɗa labarai na jam’iyyar da shugabanninta.
Mista Dungurawa ya bayyana ɗan majalisar tarayya na Kiru/Bebeji a matsayin “mai raunin ɗan siyasa” wanda ya taka bayan tafiyar Kwankwasiyya da jam’iyyar NNPP domin ya ci zabe, maimakon ƙarfin kansa.
Da yake jawabi a ranar Alhamis lokacin da ya karɓi baƙuncin dattawa da masu riƙe da muƙaman gargajiya daga mazaɓar Kiru/Bebeji a ziyarar haɗin kai a gidansa na Kano, Mista Kwankwaso ya ce korar ta zama wajibi kuma a kan lokaci.
“Wannan shawara kan ɗan majalisa (Jibrin) ya zama wajibi domin wannan yunƙuri yana da matuƙar muhimmanci a gare mu kasancewar ita ce rayuwarmu da ta magoya bayanmu, idan aka yi la’akari da ita ita ce rayuwar jiharmu da ƙasa baki ɗaya.
“Kowane yunƙuri zai yi kasa a gwiwa ba tare da shugabanci nagari ba, kuma ba ma son wannan yunƙuri ya ci tura, a mafi yawan lokuta, ya dace a kawar da mabiya marasa kishin kasa domin a samu nasarar tafiyar.
“Kuna sane da duk abin da ya faru amma mafi mahimmanci, muna goyon bayan shugaban NNPP, Hashimu Dungurawa, da ya ɗauki matakin a madadin jam’iyyar, saboda mun yi imanin cewa abu ne mai kyau don gyara jam’iyyar,” inji shi.
Shugaban na NNPP ya kuma bayyana cewa jam’iyyar za ta gabatar da dan takara mai karfi da zai maye gurbin Mista Kofa a zaɓen 2027 mai zuwa.
“Idan lokacin zaɓe ya zo, za mu zaɓi wanda ya fi dacewa a hankali, wanda zai wakilci mutanen mazaɓa, jam’iyyar da mambobinta da kyau a majalisa,” inji Kwankwaso.
