27
Sep
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kungiyar Ma’aikatan Man Fetur da Gas (NUPENG) ta tabbatar da cewa ta samu takardun kotu da ke hana mambobinta sayar da tikiti ko duk wani yunƙuri da zai kawo tsaikon al’amura a Matatar ɗangote. Shugaban NUPENG, Williams Akporeha, ya bayyana haka yayin taron manema labarai a Abuja ranar Talata, wanda aka gudanar tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Man Fetur da Gas (PENGASSAN). Akporeha ya ce ƙungiyar tana mutunta doka, kuma za ta bari shari’a ta yi aikinta har sai an kammala duk wani sha’ani a kotu. “Kamar yadda kowa ya sani, ɗangote…
