ukarofi

12735 Posts
An kama shi yana yunƙurin shigar da hodar iblis cikin kurkukun Kuje

An kama shi yana yunƙurin shigar da hodar iblis cikin kurkukun Kuje

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar da ke Kula da Gidajen Yari ta Nijeriya (NCoS) ta kama wani mutum mai suna Njimogu Ikedi da laifin yin yunƙurin safarar hodar Iblis da sauran muggan ƙwayoyi zuwa gidan yarin Kuje a babban birnin tarayya Abuja. Kakakin hukumar NCoS, Samson Duza ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja. Duza, wanda ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:45 na yammacin ranar Asabar a yayin da ake gudanar da bincike na yau da kullum, ya bayyana wanda ake zargin a matsayin Njimogu Ikedi, wanda ya “ɓoye…
Read More
Karɓo bashin Tinubu dabara ce ta bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya – Abbas

Karɓo bashin Tinubu dabara ce ta bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya – Abbas

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kakakin Majalisar Wakilan Nijeriya, Tajudeen Abbas ya jaddada goyon Majalisa ga tsare-tsaren karɓo rance na Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Tajudeen ya ce, Majalisar Wakilai na tare da tsarin Tinubu, yana mai bayyana karɓo bashin da wata dabara ta bunƙasa tattalin arziki da kawar da talauci. Tajudeen ya faɗi hakan ne a wurin taron shekara-shekara na ƙungiyar African Network of Parliamentary Budget Offices (AN-PBO) karo na 8 wanda ya gudana a Abuja. Ya ƙaryata rahotannin da ke cewa Majalisar ta ƙi amincewa da tsarin ciyo bashin Tinubu, yana mai kiran irin waɗannan rahotannin da “na yaudara da…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta sanar da taken ranar bikin ’yancin kan Nijeriya na cika shekara 65

Gwamnatin Tarayya ta sanar da taken ranar bikin ’yancin kan Nijeriya na cika shekara 65

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin tarayya ta sanar da taken bikin ranar samun ‘yancin kai na Nijeriya a shekarar 2025. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Segun Imohiosen ya raba wa Blueprint Manhaja ranar Laraba a Abuja. Gwamnatin Tarayya ta bayyana babban jigon bikin cikar ‘yancin kai na 2025, mai taken: Nigeria @ 65: All Hands on Deck for a Greater National na nuni da buƙatar haɗin kai, da kishin ƙasa a tsakanin cibiyoyin gwamnati, kamfanoni masu zaman kansu, ƙungiyoyin farar hula, da…
Read More
Komawar Natasha majalisa ya nuna haɗin kai zai iya yaƙar zalunci – Atiku

Komawar Natasha majalisa ya nuna haɗin kai zai iya yaƙar zalunci – Atiku

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yaba da buɗe ofishin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a Majalisar Dattawa, inda ya ce haɗin kai ya yi nasara a kan zalunci. A ranar Talata ne Majalisar ta buɗe ofishinta, bayan rufe shi da aka yi tun daga 6 ga watan Maris, 2025, lokacin da aka dakatar da ita na tsawon watanni shida saboda zargin karya ƙa’idojin majalisar. Ko da yake Kotun Tarayya ta yanke hukunci a ranar 4 ga watan Yuli cewa dakatarwar “ta yi tsauri kuma an yi ta ba bisa ƙa’ida ba.” Da yake mayar…
Read More
Tinubu ya karrama ’Yan Ogoni Huɗu da Lambar Yabo Ta ƙasa

Tinubu ya karrama ’Yan Ogoni Huɗu da Lambar Yabo Ta ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya karrama Kwamandan Hukumar Neja (CON) na ƙasa bayan rasuwa ga tsoffin shugabannin Ogoni, Albert Badey, Edward Kobani, Theophilus Orage, da Samuel Orage wanda aka fi sani da “Ogoni Four.” Jaridar Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Larabar da ta gabata lokacin da ya karɓi rahoton kwamitin tuntuɓar yankin Ogoni a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja. Shugaban ya kuma umurci mutanen yankin Ogoni da su rungumi sulhu da hadin kai bayan shekaru da dama da aka shafe ana rarrabuwar kawuna. "Bari tunaninsu ya…
Read More
Za mu ɗauki mataki kan Malam Lawan Triumph bayan samun ƙorafi a rubuce – Gwamnan Kano

Za mu ɗauki mataki kan Malam Lawan Triumph bayan samun ƙorafi a rubuce – Gwamnan Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa, da zarar gwamnatinsa ta amshi ƙorafi a rubuce kan malamin addinin Musulunci, Sheikh Lawan Abubakar, wanda ake kira da Triumph, za ta ɗauki matakin da ya dace akan sa. Wasu mazauna birnin Kano sun yi zanga-zangar lumana game da zargin malamin addinin, Lawan Triumph da kausasa kalamai kan Annabi Muhammadu (SAW). Masu zanga-zangar sun dangana da farfajiyar gidan gwamnatin Kano, inda Gwamna Abba ya tarɓe su tare da yi musu jawabi. A baya-bayan nan ne aka ga malamin a wani bidiyo yana musanta batun cewa,…
Read More
Za mu ci gaba da gwagwarmayar haɗa kan ’yan siyasar Nijeriya – Sule Lamiɗo

Za mu ci gaba da gwagwarmayar haɗa kan ’yan siyasar Nijeriya – Sule Lamiɗo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ɗaya daga cikin dattawan babbar jam'iyyar hamayya ta PDP ya ce za su ci gaba da yin gwagwarmaya da ƙoƙarin haɗakan duk wani mai faɗa-aji a siyasar Nijeriya don tabbatar da ci gaban ƙasar da ma dimukraɗiyya. Alhaji Sule Lamido, wanda tsohon gwamnan jihar Jigawa ne, ya shaida wa BBC cewa ya sha faɗin cewa idan kana tunkarar abu, to baka kawo rashin nasara a cikinsa. Ya ce,"Ko shakka babu muna ta faɗi tashin ganin mun yi sulhu a inda ya kamata a yi, sannan muna wayoyi da tuntuɓa domin Nijeriya ta ci gaba,…
Read More
Mun ci ribar biliyan N601 a watanni shidan farkon 2025 – Bankin GT

Mun ci ribar biliyan N601 a watanni shidan farkon 2025 – Bankin GT

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kamfanin GTCO, mamallakin bankin GT, ya bayyana samun ribar Naira biliyan 601 a watanni shida na farkon shekarar 2025. Sai dai bankin ya ce duk da haka ribar tasa raguwa ta yi a kan ta Naira tiriliyan daya da ya ci a farkon shekarar da ta gabata. Wannan na kunshe ne a cikin sakamakon binciken kudi kamfanin ya fitar, wanda ya ƙare ranar 30 ga Yuni, 2025. Bankin ya kuma ce amma ribar kafin a cire haraji ce, idan aka cire kuma za ta koma biliyan 449.01, idan aka kwatanta da biliyan 905.57 a…
Read More
ANLCA za ta ci gaba da bin doka da oda — Hafizu Lurwanu

ANLCA za ta ci gaba da bin doka da oda — Hafizu Lurwanu

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Kungiyar masu fitar da kaya ƙarƙashin shugabancin shugabanta na Kano, Alhaji Hafizu Lurwanu, ta gudanar da taro na musamman a Kano a ranar Juma’a da ta gabata, inda shugabannin reshen ƙungiyar da dama suka halarta. Wannan ƙungiya ce mai suna Association of Nigerian Licensed Customs Agents (ANLCA), wacce ke da izinin gudanar da harkokin fitar da kaya bisa ƙa’ida da doka. A jawabinsa, Alhaji Hafizu ya bayyana cewa ƙungiyar na da dimbin mambobi, kuma tana taka muhimmiyar rawa wajen samar da ayyukan yi ga matasa da kuma bunƙasa tattalin arzikin ƙasa. Ya ce babban manufar…
Read More
Dalilin da muke goyon bayan Tinubu kan karɓo bashi — Majalisar Wakilai

Dalilin da muke goyon bayan Tinubu kan karɓo bashi — Majalisar Wakilai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Majalisar Wakilai ta bayyana cewa ta amince da duk wasu tsare-tsare da dabarun karɓo rancen kuɗaɗe na Shugaba Bola Tinubu, bisa la’akari da ƙoƙarin da yake yi na farfaɗo da tattalin arziki da kuma rage talauci a ƙasar nan. Shugaban Majalisar, Abbas Tajudeen ne ya bayyana hakan a yayin da yake jawabi ranar Litinin, a taron shekara-shekara karo na takwas kan bitar kasafin kuɗaɗe na majalisun dokokin nahiyar Afirka (African Network of Parliamentary Budget Offices) da ke gudana a Abuja. Abbas ya ƙaryata raɗe-raɗin cewa majalisar ta ƙi amincewa da tsare-tsaren karɓo rance na…
Read More