ukarofi

12735 Posts
Gwamnatin Legas ta fara yin rusau a Kasuwar Baje Kolin Duniya

Gwamnatin Legas ta fara yin rusau a Kasuwar Baje Kolin Duniya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD A ranar Alhamis ne Gwamnatin Jihar Legas ta fara rusa wasu gidaje marasa aminci a harabar Kasuwar Baje Kolin Duniya da ke Ojo. Ma’aikatar Tsare-tsare, Hukumar Kula da Gine-gine da Hukumar Sabunta Birane da Hukumar Bada Izinin Tsara Gine-gine na jihar ta Legas ne suka gudanar da aikin a tare cikin aiki na haɗin gwiwa. Babban mataimaki na musamman kan harkokin kafafen yaɗa labarai ga Gwamna Babajide Sanwo-Olu, Jubril Gawat, ya tabbatar da wannan aiki a wani saƙo a shafin ɗ. A cewarsa, an ɗauki matakin ne domin dawo da oda da kuma aiwatar da dokokin…
Read More
Gwamnatin Tarayya za ta fara farautar masu takardun bogi a wajen aiki

Gwamnatin Tarayya za ta fara farautar masu takardun bogi a wajen aiki

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Tarayya ta umarci dukkanin ma’aikatu, hukumomi, sojoji da kuma cibiyoyin kuɗi da ma’aikatu masu zaman kansu da su fara tantance takardun shaidar kammala makaranta na ma’aikatansu daga ranar 6 ga watan Oktoba, 2025. Wannan mataki ya biyo bayan yawaitar bogi da takardun karatu na bogi a Nijeriya. Za a yi tantancewar ne ta hanyar tsarin amfani da kwamfuta mai suna Nigeria Education Repository and Databank (NERD), wanda aka ƙirƙiro domin adanawa da tabbatar da sahihancin takardun karatun ma’aikata. A wannan tsari, babu wanda za a ɗauka aiki ko a tabbatar masa da muƙami…
Read More
Kungiyar ƙananan ƙabilun Arewa sun gargaɗi El-Rufai ya shiga taitayinsa

Kungiyar ƙananan ƙabilun Arewa sun gargaɗi El-Rufai ya shiga taitayinsa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kungiyar ƙananan ƙabilu na Arewacin Nijeriya (NNMG) ta yi Allah-wadai da kakkausar murya da zargin da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi cewa Shugaban ƙasa Bola Tinubu na da niyyar tsawaita wa’adin mulkinsa fiye da shekarun da kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada. A fahimtarmu tsohon gwamnan, wanda yanzu ya koma ɗaya daga cikin masu kokarin kawo ruɗani da hayaniyar siyasa a ƙasar, kawai yana magana ne saboda ƙiyayya, bakin ciki da kuma rashin mutunta dimokuraɗiyya. Idan ba a manta ba, Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, ya kai wa El-Rufai ziyarar…
Read More
An tsinci gawar ɗan shekara 12 a kogin Borno 

An tsinci gawar ɗan shekara 12 a kogin Borno 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Al’ummar Maiduguri, Babban Birnin Jihar Zamfara, sun shiga cikin alhini a ranar Talata bayan an gano gawar wani matashi ɗan talla, wanda ake kyautata zaton ɗan kimanin shekaru 12 ne a duniya, a kogin Gamboru, dake unguwar Kwastam a birnin. Mazauna yankin sun shaida wa Manhaja cewa an fara ganin yaron yana shawagi a bakin kogi kafin daga bisani jama'ar gari su fitar da shi, inda suka sanar da hukuma. Lamarin nutsewa a kogi ba sabon abu ba ne a Maiduguri da kuma faɗin jihar Borno, musamman a lokacin damina da koguna da magudanan…
Read More
Ku surukaina ne – Atiku ya yi alƙawarin tafiya da Yarabawa idan ya ci zaɓen 2027

Ku surukaina ne – Atiku ya yi alƙawarin tafiya da Yarabawa idan ya ci zaɓen 2027

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya kuma jigo a Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) sannan mai neman tsaya wa takarar shugabancin ƙasar nan, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin tafiyar da gwamnati mai dunkulewa tare da iƙirarin cewa, ƙabilar Yarabawa za ta mamaye wasu manyan muƙamai, saboda kasancewar su surukansa. An yi ta zage-zage cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar zai fifita ƙabilarsa ta Hausa-Fulani fiye da wasu musamman Yarbawa. An ce Atiku ya shirya maida Yarabawa saniyar-ware a matsayin mayar da martani ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ake zargin ta fifita su fiye da…
Read More
Za a gudanar da taron kiwon lafiya na farko a Gombe

Za a gudanar da taron kiwon lafiya na farko a Gombe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  An kammala shirin gudanar da taron lafiya karo na farko a tarihin Jihar Gombe, wanda za a fara a ranar 2 ga Oktoba. Da yake zantawa da manema labarai wannan Larabar a Gombe, Kwamishinan Lafiya, Dakta Habu Dahiru, ya bayyana cewa, za a gudanar da taron na tsawon kwanaki biyu domin tattauna matsalolin bangaren lafiya da zummar samo mafita. Ya ce, taron zai samu halartar manyan baki ciki har da Uwargidan Shugaban ƙasa, Sanata Remi Tinubu; Mataimakiyar Sakataren Majalisar ɗinkin Duniya, Hajiya Amina Mohammed; Ministan Lafiya, Farfesa Ali Pate; tare da wasu abokan hulda,…
Read More
Muna yaba wa Gwani Makoɗa kan sakamakon NECO da ɗaliban Kano suka yi zarra – Hon. Doguwa

Muna yaba wa Gwani Makoɗa kan sakamakon NECO da ɗaliban Kano suka yi zarra – Hon. Doguwa

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Jagoran siyasar ƙaramar Hukumar Doguwa kuma mai ba wa Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf shawara kan dabarun tafiyar da siyasa, Hon. Ali Abdu Dogowa, ya bayyana cewa, nasarar da Kano ta samu a sakamakon jarrabawar kammala sakandire na hukumar shirya jarrabawa ta NECO babbar nasara ce ga al’ummar Kano da Arewa bakiɗaya. Hon. Dogowa ya jaddada cewa wannan nasara ta samo asali ne daga jajircewar Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusif, tare da kulawar Ma’aikatar Ilimi ƙarƙashin jagorancin Hon. Gwani Ali Haruna Makoɗa, wanda ya taka rawar gani wajen gyara tsarin ilimi a jihar.…
Read More
An kama mace tana rubuta wa kwamishiniyar Taraba jarrabawar ICAN

An kama mace tana rubuta wa kwamishiniyar Taraba jarrabawar ICAN

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD An kama wata mata da ake zargin tana zana jarrabawar makarantar 'Chartered Accountants of Nigeria' (ICAN) a madadin Sarah Enoch Adi, Kwamishiniyar Kuɗi ta Jihar Taraba. A wani faifan bidiyo da Sahara Reporters ta wallafa, masu kula da jarrabawar sun yi wa wadda ake zargin tambayoyi, inda ta bayyana kanta da Leaɓitt Feliɗ. Sai dai bayanai sun nuna cewa ɗalibar da ta yi rijistar wannan jarrabawar ita ce kwamishina Sarah Enoch Adi. Lokacin da masu kulawa suka matsa mata, Feliɗ ta faɗi cewa tana rubuta jarrabawar ne a madadin Sarah Adi. Da aka nemi sunan ta,…
Read More
Kada ku rungumi fasahar AI a makance – ECOWAS ga mambobinta

Kada ku rungumi fasahar AI a makance – ECOWAS ga mambobinta

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Majalisar ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin ƙasashen Yammacin Afirka ECOWAS, ta gargaɗi ƙasashen Afirka da su guji rumgumar ƙirƙirarriyar basira ta AI, musamman a harkokin majalisar, tare da jaddada buƙatar yin taka tsantsan da fasahar. An yi wannan kiran ne a taron ƙara wa juna sani na majalisar ECOWAS na 2025 da aka gudanar a garin Fatakwal na jihar Ribas. ƙwararru da 'yan majalisa sun yarda cewa yayin da AI ke ba da babbar dama, dole ne ɗan dama ya yi wasu abubuwan da kansa. A yayin tattaunawar, ‘yan majalisar da suka haɗa da Guy Marius Sagna…
Read More
Saudiyya ta gindaya sabbin sharuɗɗan zuwa aikin Hajji

Saudiyya ta gindaya sabbin sharuɗɗan zuwa aikin Hajji

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tuni dai aka fara bayyana fargaba bayan da ƙasar Saudiyya ta ɓullo da wasu sabbin tsauraran ƙa'idoji ga maniyyata aikin Hajjin bana. Saudiyya ta tsaya kai da fata wajen yin aiki da sababbin ƙa'idojin, wanda idan ta tabbata da yawa daga cikin maniyyatan Nijeriya ba za su samu damar zuwa sauke farali a aikin Hajjin da ke tafe ba. Yanzu haka dai wasu jami'an hukumar alhazan Nijeriya suna ƙasar mai tsarki, domin tattauna yadda za a fuskanci sababbin matakan. Fatima Sanda Usara, mai riƙon muƙamin daraktar yaɗa labarai ta hukumar alhazan Nijeriyar, wato NAHCON…
Read More