ukarofi

12735 Posts
Nijeriya ta jaddada matsayarta na tabbatar da ’yancin ƙasar Falasɗinu a Majalisar Dinkin Duniya

Nijeriya ta jaddada matsayarta na tabbatar da ’yancin ƙasar Falasɗinu a Majalisar Dinkin Duniya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin Tarayya ta Nijeriya ta bayyana cewa, mafita ta samar da ƙasashe biyu ita ce hanya mafi kyau da za ta kawo dawwamammen zaman lafiya ga al’ummar Falasɗinu. Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda Mataimakinsa, Kashim Shettima, ya wakilta, ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a babban taron Majalisar ɗinkin Duniya karo na 80 a birnin New York. Tinubu ya ce: “Ba mu yarda da ganin rayuwar ɗan Adam ta maƙale cikin jayayya marar ƙarewa ba. Shi ya sa muke tsayawa ba tare da shakka ba, muna cewa mafita ta samar da…
Read More
Shugaban ƙaramar hukumar Jema’a ya jaddada ƙudirinsa na aiwatar da ayyukan gina al’umma

Shugaban ƙaramar hukumar Jema’a ya jaddada ƙudirinsa na aiwatar da ayyukan gina al’umma

Daga ABUBAKAR LABARAN a Kafanchan  Shugaban ƙaraman Hukumar Jema'a dake jihar Kaduna Honarabul Peter Tanko Dogara ya jaddada ƙudirinsa na aiwatar ta ayyukan gina al'umma waɗanda suka fi buƙata. Tanko ya yi wannan albishir ne lokacin da ya jagoranci wani taron gangami na mahawara da al'umman ƙaraman hukumar a Kafanchan. Lokacin da yake bada muhimmanci akan gina karkara, wadda ya ce ita ce abin da gwamnatinsa tafi bada himma akai, shugaban ƙaramar hukuman ya ƙara da cewa, ba zai taɓa ƙasa a gwiwa ba, na tabbatar da ya aiwatar da ayyukan walwala da jin daɗin rayuwa a ko'ina cikin al'umman…
Read More
Asalin bikin Mauludi da hawan Takutaha a Kano – Ra’ayoyin malamai da al’umma

Asalin bikin Mauludi da hawan Takutaha a Kano – Ra’ayoyin malamai da al’umma

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Bikin mauludi na takutaha ya jima ana gudanar da shi a Birnin Kano da jihar baki ɗaya, inda ake yin hawa da kuma shagulgula. Wannan ya sanya Wakilin Blueprint Manhaja a Jihar Kano ya bi sahun masu hawa Goron Dutse wajen bikin Hawan Takutaha, inda ya tattauna da malamai da mabiyan Mauludi kan muhimmancin wannan rana ta zagayowar haihuwar Shugaban Halitta, Annabi Muhammad (SAW). Wannan al’ada ta shafe ɗaruruwan shekaru tana gudana daga ranar 12 ga Rabi’ul Awwal zuwa 19 ga watan, wacce a Kano aka fi sani da Takutaha. A wannan rana, jama’ar Kano,…
Read More
2027: Atiku ya musanta yi wa Yarabawa alƙawari idan aka zaɓe shi

2027: Atiku ya musanta yi wa Yarabawa alƙawari idan aka zaɓe shi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya nesanta kansa daga wata magana mai cike da cece-kuce da wani Kola Johnson ya yi iƙirarin cewa shi ne mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai. Sanarwar wadda ta yaɗu a ranar Larabar da ta gabata, ta yi zargin cewa Atiku ya yi alƙawarin bai wa Yarabawa fifiko idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a 2027. Haka kuma ya nuna cewa gwamnatin Atiku ba za ta fifita wata ƙabila fiye da wata ba, saboda alaƙar…
Read More
Gwamnan Kano ya halarci ɗaurin auren ɗan Kwamishinan Ilimi, Makoɗa

Gwamnan Kano ya halarci ɗaurin auren ɗan Kwamishinan Ilimi, Makoɗa

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya halarci ɗaurin auren ɗan Kwamishinan Ilimi na jihar, Gwani Ali Haruna Makoɗa, da aka gudanar a Masallacin Sheikh Isyaka Rabiu da ke Gauron Dutse, a makon da ya gabata. Gwamna Yusuf, wanda ya tsaya a matsayin waliyyin ango, Abdufattah Gwani Ali Makoɗa, tare da amaryarsa Maryam Sa’id Muhammad, ya jaddada muhimmancin aure a matsayin ginshiƙin samun zuriyar albarka. Ya taya ma’auratan murna tare da yi musu addu’ar zaman lafiya, albarka, da yalwar arziki mai dorewa, inda ya kuma shawarce su da haƙuri da juna da girmama…
Read More
Matasa sun rabauta da shirin Gwamna Abba na horarwa kan sana’o’in dogaro da kai a Gwarzo

Matasa sun rabauta da shirin Gwamna Abba na horarwa kan sana’o’in dogaro da kai a Gwarzo

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da shirin koyar da sana'o'in dogaro da kai ga matasa a garin Getso da ke ƙaramar Hukumar Gwarzo. Da yake jawabi yayin bikin buɗe cibiyar, babban daraktan yaɗa labaran gwamnan Kano, Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa, wanda ya jagoranci wakilan cibiyar jami'an yaɗa labarai da hulɗa da jama'a (NIPR) domin sheda ƙaddamar da bayar da horon da kuma ganewa idanun su wasu ayyuka da gwamnatin jihar Kano take aiwatarwa, ya bukaci wadanda zasu amfana da shirin su mayar da hankali kan sana'o'in da za a koya musu. Ya ce gwamnatin…
Read More
Yajin aiki: Ma’aikatan wutar lantarki sun jefa Nijeriya cikin duhu

Yajin aiki: Ma’aikatan wutar lantarki sun jefa Nijeriya cikin duhu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Masu amfani da wutar lantarkin da ke dogaro da layin wutar lantarki na ƙasa na iya fuskantar tsawaita wuta cikin sa'o'i bayan ƙungiyar ma'aikatan wutar lantarki ta ƙasa a ranar Laraba ta fara yajin aikin gama gari a faɗin ƙasar sakamakon rashin warware taƙaddamar ma'aikata da kamfanin sadarwa na Nijeriya. ƙungiyar, a wata takardar da ke ɗauke da sa hannun muƙaddashin babban sakataren ta, Dominic Igwebike da Manhaja ta samu, ta umurci mambobinta da ke faɗin ƙasar nan da su janye ayyukansu na tsawon lokaci har sai lokacin da hukumar za ta magance matsalolin…
Read More
Sarkin Daura ya yi wa Mawaƙi Rarara huce-haushi da sarautar Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa

Sarkin Daura ya yi wa Mawaƙi Rarara huce-haushi da sarautar Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa

Daga UMAR GARBA a Katsina  Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruƙ Umar, ya ba wa fitaccen mawaƙi Dauda Kahutu Rarara sarautar Sarkin Waƙar ƙasar Hausa, lamarin da wasu za su iya kallo a matsayin wani huce-haushi biyo bayan badaƙalar ba wa mawaƙin digirin girmamawa na ƙarya. Naɗin na zuwa ne a yayin da jama’a ke yin ta cece-kuce game da karramawar da wata jami’a mai suna European-American Uniɓersity ta janye wa fitaccen mawaƙin bayan an ba shi digirin girmamawa na dakta. Reshen jami’ar da bayanai a yanar gizo suka nuna cewar, hedikwatarta ta ƙasar Faransa ce ta yi bikin…
Read More
Ban ƙullaci kowa a raina ba – Jonathan ya yi wa’azin yafiya a taron rasuwar Audu Ogbeh

Ban ƙullaci kowa a raina ba – Jonathan ya yi wa’azin yafiya a taron rasuwar Audu Ogbeh

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya bayyana cewa ba ya jin haushin kowa kan taƙaddamar siyasa a baya ko kuma kai hari, yana mai jaddada cewa afuwa, tawali'u, da sasantawa na da matuƙar muhimmanci ga haɗin kan Nijeriya da ci gaban dimokraɗiyya. Jonathan ya bayyana hakan ne a yammacin Larabar da ta gabata a Abuja yayin wani taro na karrama marigayi Audu Ogbeh, tsohon ministan noma da raya karkara kuma wanda ya taɓa riƙe muƙamin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa. A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Ikechukwu Eze ya…
Read More
Gwamnatin Kano ta ɗauki ƙarin malamai fiye da 4,000

Gwamnatin Kano ta ɗauki ƙarin malamai fiye da 4,000

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano A ƙoƙarinta na inganta da farfaɗo da harkar ilimi tun daga tushe, gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf ta ɗauki ƙarin malaman makarantar firamare guda 4,315, domin kawo ƙarshen matsalar ƙarancin malamai a makarantu a faɗin jihar. Da yake mika takardun aikin na dundundun ga sabbin malaman a ɗakin taro da ke filin wasa na Sani Abacha, ƙofar Mata, Kano, Gwamna Abba ya ja hankalin sabbin malaman da su rungumi aikin da gaskiya da riƙon amana tare da zama jakadun hali nagari ga ɗaliban da za su koyar. Gwamnan ya…
Read More