26
Sep
Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano A ƙoƙarinta na inganta da farfaɗo da harkar ilimi tun daga tushe, gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf ta ɗauki ƙarin malaman makarantar firamare guda 4,315, domin kawo ƙarshen matsalar ƙarancin malamai a makarantu a faɗin jihar. Da yake mika takardun aikin na dundundun ga sabbin malaman a ɗakin taro da ke filin wasa na Sani Abacha, ƙofar Mata, Kano, Gwamna Abba ya ja hankalin sabbin malaman da su rungumi aikin da gaskiya da riƙon amana tare da zama jakadun hali nagari ga ɗaliban da za su koyar. Gwamnan ya…
