ukarofi

12736 Posts
Dikko Raɗɗa ya rantsar da masu ba shi shawara guda biyu

Dikko Raɗɗa ya rantsar da masu ba shi shawara guda biyu

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya rantsar da sabbin masu bashi shawara guda biyu. Sun haɗa da Hon. Tasi'u Dahiru Ɗanɗagoro a matsayin mai baiwa gwamna shawara akan Ilimin Alkur'ani da yaran da ba su zuwa makaranta. Sai Hon. Aminu Lawal Jibia wanda aka rantsar a matsayin mai bai wa gwamna shawara akan inganta rayuwar al'umma. Aminu Lawal ya taɓa riƙe muƙamin shugaban karamar hukumar Jibiya,ya kuma riƙe muƙamin mai ba gwamna shawara a gwamnatin Aminu Bello Masari kafin ya sami wannan muƙami. Haka shima Hon Tasi'u Dandagoro ya taɓa riƙe muƙamin shugaban…
Read More
JIBWIBS ta naɗa sabon daraktan agaji a Katsina

JIBWIBS ta naɗa sabon daraktan agaji a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Majalissar Agaji ta ƙungiyar JIBWIS ta Katsina ta naɗa Alhaji Garba Galadima Charanchi a matsayin sabon Daraktan agaji na ƙungiyar. Ƙungiyar ta gabatar da sabon Daraktan Agaji na ƙungiyar ga shugaban ƙungiyar Izalatul bidi'a wa Ikamatul sunnah reshen Jihar Katsina Sheikh Yakubu Musa Hassan Sauttus sunnah. Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina ya yi maraba da tawagar tare da yaba musu bisa jajircewa wajen tallafa wa al’umma ta fuskokin agaji da jin ƙai. Ya kuma buƙaci sabon daraktan da sauran mambobin majalisar da su mayar da hankali wajen gudanar da aikinsu cikin gaskiya da riƙon amana,…
Read More
2025: An fito da ƙa’idojin gasar gajerun labarai ta Ranar Marubuta Hausa ta Duniya

2025: An fito da ƙa’idojin gasar gajerun labarai ta Ranar Marubuta Hausa ta Duniya

Daga BILKISU YUSUF ALI Kwamitin gudanarwa da tsare-tsare na shirya taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya ya fitar da ƙa’idojin shiga gasar gajerun labarai na taron, wanda za a gudanar a Dutse, Babban Birnin Jihar Jigawa a wannan shekara ta 2025.Dr. Mujaheed Abdullahi Kudan ne ya sanar da ƙa’idojin a madadin kwamitin gasar a wata sanarwa cikin makon nan, inda ya bayyana cewa, “daga cikin tsare-tsaren bikin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya na shekarar 2025, wanda za a gabatar a Dutse na Jihar Jigawa a ranakun 31/12/2025 zuwa 01/01/2026. An shirya gasar rubutun gajerun labaran Hausa a kan batun fasahar…
Read More
Za a gudanar da Ranar Marubuta Hausa ta Duniya ta bana a Dutse, Jihar Jigawa

Za a gudanar da Ranar Marubuta Hausa ta Duniya ta bana a Dutse, Jihar Jigawa

Daga BILKISU YUSUF ALI  08054137080 Jaridar Manhaja ta tattauna da sakataren kwamitin gudanar da taron Ranar Marubuta ta Hausa ta Duniya wadda za a gudanar a Dutsen Jihar Jigawa (Jigawa 2025) Dr. Abdurrahman Aliyu daga Jihar Katsina inda ya yi bayani dalla-dalla kan taken taron na bana da abin da taron ya ƙunsa da alfanun taron ga marubuta da gwamnati da ma al’ummar Nijeriya musamman Arewa. Shirye-shirye sun kankama domin gudanar da Ranar Marubuta Hausa ta Duniya a wannan shekara 2025 karo na uku a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa. Taron zai gudana a ƙarƙashin taken: “Marubuta a Karni na…
Read More
Rashin kuɗin buga littafi ne ya ƙyanƙyashe marubuta yanar gizo – MD Asnanic

Rashin kuɗin buga littafi ne ya ƙyanƙyashe marubuta yanar gizo – MD Asnanic

"Karancin ilimi ne ke hana a ba marubuci darajar da ya cancanta" Daga AISHA ASAS  Sanannen abu ne, Arewacin Nijeriya kewaye ta ke da albarkatun ƙasa da ko su kaɗai mu ka dogara da su, za su iya cin ƙarfin buƙatunmu. Duk da wannan ni'ima da aka ba mu, Allah ya mana daɗɗi da baiwar ƙirƙira, musamman a tsakanin matasanmu. Muhammad Iliyas, wanda aka fi sani da MD Asnanic, matashi ne da ƙwaƙwalwarsa ke zagaya tsakanin ɓangarorin rubutu, kai har ma da na rera waƙa. A taƙaice, matashi ne mai ƙwaƙwalwar mutane da yawa.  A wannan makon, shafin Adabi na…
Read More
Majalisar Katsina ta amince da ƙudirin hukunci mai tsanani ga masu ƙwacen waya

Majalisar Katsina ta amince da ƙudirin hukunci mai tsanani ga masu ƙwacen waya

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Majalisar Dokoki ta Jihar Katsina ta amince da ƙudirin yin hukunci mai tsanani ga masu ƙwacen waya ta amfani da makami tare da buƙatar kirkiro da Jami'an tsaron Al'umma CWC a cikin ƙaramar hukumar Katsina. Ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina Hon. Aliyu Abubakar Albaba ya gabatar da ƙudirin, a zaman majalisar ƙarƙashin jagorancin mataimakin kakakin majalisar Rt. Hon. Abdul Jalal Haruna Runka. Da yake gabatar da jawabinsa yayin da yake gabatar da ƙudirin, Hon.Aliyu Abubakar Albaba ya bayyana cewa gabatar da ƙudirin ya biyo bayan yawaitar ƙwacen waya da makami a cikin garin…
Read More
Masana guba sun nemi a zuba jari da gaggawa domin samar da maganin saran maciji

Masana guba sun nemi a zuba jari da gaggawa domin samar da maganin saran maciji

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Ƙungiyar masana harkar guba ta Najeriya (Toxinological Society of Nigeria TSN) ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da na jihohi da su mai da hankali wajen zuba jari a samar da maganin cizon maciji a cikin gida tare da inganta cibiyoyin kiwon lafiya, domin daƙile mace-macen da ke faruwa sakamakon cizon maciji a ƙasar. Wannan kira ya fito ne daga sanarwar bayan taro da babban sakatare na TSN, Dokta Mustapha Shehu Muhammad, ya fitar bayan taron nasu karo na biyu na ƙungiyar, wanda aka gudanar daga 14 zuwa 17 ga watan Satumba a Jami’ar Gombe. Taron…
Read More
NSCDC ta sami sabon kwamanda a Katsina

NSCDC ta sami sabon kwamanda a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Abbas Ɗan Ale Moriki shine sabon kwamandan hukumar tsaro na farin kaya (Civil Defence) a Jihar Katsina. Wata sanarwar da jami'in hulɗa huɗɗa da jama'a na hukumar a Katsina SC Buhari Hamisu ya fitar, sabon kwamandan ya canji Kwamanda Aminu Datti Ahmad da aka yiwa sauyin wajen aiki. A jawabinsa na ban kwana kwamanda Aminu Datti ya yabawa jami'an hukumar a Katsina bisa irin goyon baya da suka bashi ya gudanar da aikin sa a jihar. Sai yayi kira ga jami'an hukumar da su ba sabon kwamandan irin goyon bayan da suka bashi domin samun…
Read More
Sojoji sun raba taki ga manoma domin ƙarfafa zaman lafiya a Zamfara

Sojoji sun raba taki ga manoma domin ƙarfafa zaman lafiya a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Rundunar sojojin Najeriya ta 1 Brigade Gusau, ta rabawa manoma 100 taki kyauta a Jihar Zamfara, a wani ɓangare na dabarun yaƙi da ta’addanci, domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar. Kwamandan Brigade ɗin, Brig. Janar Mustapha Jimoh wanda mataimakin shugaban ma’aikatan Rundunar Sojin, Laftanal Kanal Isah Galadima ya wakilta a lokacin rabon ya bayyana cewar, an gudanar da wannan shiri ne domin bunƙasa samar da abinci da kuma ƙarfafa dangantakar jama’a da rundunar sojoji. "Ba ko yaushe muke ɗaukar makamai ba domin yaƙi da ta'addanci, muna amfani da hanyoyin da dabarun…
Read More
Mafi yawan masu karɓar bashin da ya karya min jari maza ne – Saddiƙa Jibrin Abdullahi

Mafi yawan masu karɓar bashin da ya karya min jari maza ne – Saddiƙa Jibrin Abdullahi

"A wannan lokacin ya zama dole mata su kama sana'a" Daga MUKHTAR YAKUBU A yanayi na rayuwa a yanzu mata sun farka wajen neman na kansu wajen kama sana'o'i da sauran ayyuka domin samun yadda za su gudanar da rayuwarsu ba tare da sun jira a kawo musu ba. Saddiƙa Jibrin Abdullahi wadda aka fi sani da Mama Saddiƙa tana cikin mata 'yan kasuwa da take gudanar da harkokin kasuwanci kala-kala domin ta samu ta rufawa kanta asiri. Wani abu da ya fi burge mutane shi ne yadda ta ke gudanar da harkar kasuwancin dankalin turawa da ake ganin harka…
Read More