23
Sep
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya sanar da haka a lokacin da yake buɗe taronta masu ruwa da tsaki don gyara tsarin ilimin almajiri da islamiyya a jihar. Gwamna Raɗɗa ya sanar da sabbin makarantun Tsangaya guda uku da za a gina kafin ƙarshen shekara. Ya bayyana cewa masu haddar Alkur’ani za su samu guraben karatu kan MBBS, Nursing, da sauran fannoni na ƙwarewa kan kiwon lafiya. Masu ruwa da tsaki a wajen taron da sun bada goyon baya ga gyare-gyaren da gwamnatin jihar ta ɓullo da su don ƙarfafa ilimin addini da na zamani.…
