ukarofi

12736 Posts
Masarautar Ƙaura Namoda ta horar da mambobin MSSN akan tsarin shugabanci a Zamfara

Masarautar Ƙaura Namoda ta horar da mambobin MSSN akan tsarin shugabanci a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Masarautar Ƙaura Namoda ta ɗauki nauyin horaswa ga mambobin ɗalibai musulmi na Najeriya MSSN reshen Jihar Zamfara na tsawon kwanaki domin sanin tsarin shugabanci. Da yake jawabi yayin rufe taron bayar da horon da aka gudanar a ɗakin taro na Federal Polytechnic Ƙaura Namoda yau Lahadi, Mai Martaba Sarkin Ƙaura Namoda Alh. Sanusi Muhammad Asha yace maƙasudin bada horon shine a wayar da kan matasa kan ginshiƙin shugabanci. Sarkin ya jaddada aniyar masarautarsa na ganin an yaɗa ilimin addinin musulunci, yana Mai nuni da cewa, masarautar sa a shirye take ta tallafa wa duk wata…
Read More
Sakataren Gwamnatin Tarayya da takwarorinsa na jihohi sun gana a Jos domin ƙarfafa tsarin tafiyar da gwamnati

Sakataren Gwamnatin Tarayya da takwarorinsa na jihohi sun gana a Jos domin ƙarfafa tsarin tafiyar da gwamnati

Daga HABU ƊAN SARKI a Jos Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume ya ƙarfafa buƙatar Sakatarorin Gwamnatocin Jihohi su ɗauki nauyin da ke kansu da matuƙar muhimmanci, a matsayin su na zuciyar aikin gwamnati a jihohin su, domin su ne ƙashin bayan nasarar aikin da gwamnoni ke gudanarwa. Sanata Akume ya faɗi haka ne a Jos, yayin da yake ƙaddamar da babban taron majalisar sakataren gwamnatin tarayya da Sakatarorin jihohi zango na biyu, wanda ya mayar da hankali wajen tattauna haƙƙokin da ke kan sakatarorin gwamnati, da yadda za su taimaka wajen kawo sauye-sauye, da sauƙaƙa hanyoyin cimma manufofin gwamnati,…
Read More
An gano masana’antar ƙera makamai a Jihar Filato

An gano masana’antar ƙera makamai a Jihar Filato

Daga HABU ƊAN SARKI, Jos Rundunar haɗin gwiwa da ke aikin samar da zaman lafiya a Jihar Filato, Operation Enduring Peace, ta sanar da gano wata masana'antar ƙera makamai a ƙaramar hukumar Barikin Ladi da ke Jihar Filato. Kakakin rundunar, Samson Nantip Zhakom ýa sanar da cewar, a ranar 17 ga watan Satumba, 2025 ne rundunar ta samu wani rahoton sirri game da ayyukan da ake yi a masana'antar, wanda ba tare da ɓata lokaci ba dakarun rundunar suka kai samame ƙauyen da abin ke faruwa, har kuma aka samu nasarar kama mutum ɗaya, da wasu makamai. Ya ce, a…
Read More
Tinubu da ayyukan cigaban ƙasa a Jihar Kano

Tinubu da ayyukan cigaban ƙasa a Jihar Kano

Daga SHEHU MUSTAPHA CHAJI Kasancewar Jihar Kano cibiyar kasuwanci da dimokuraɗiyya a Arewacin Najeriya na daga cikin dalilan daya sa shugaban ƙasa Alhaji Bola Ahmed Tinubu ke cigaba da bai wa jihar kulawa ta musamman. Cikin ayyukan cigaban ƙasa da Shugaba Tinubu ya sahale a yiwa Jihar Kano a wannan makon sun haɗa da ware Naira Biliyan 12 dan samar da wutar solar a Asibitin Malam Aminu Kano da zai samar da megawatt bakwai da hakan zai sanya asibitin sauka daga layin lantarki ta ƙasa. Ana kuma cigaba da aikin gina bene mai hawa biyar na sashin bayar da kulawar…
Read More
Ƙaramar hukumar Matazu ta yi sulhu da ‘yan bindiga na yankin a Katsina

Ƙaramar hukumar Matazu ta yi sulhu da ‘yan bindiga na yankin a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban ƙaramar hukumar Matazu Hon. Shamsuddeen Muhammed Sayaya da kachalla Muhammadu na ɓangaren 'yan bindiga ne suka jagoranci zaman sulhun a madadin ɓangarorin mutanen su a wajan taron. Kacallah Muhammadu yana ɗaya daga cikin shugabannin 'yan bindigan da su ka addabi yankin ƙaramar hukumar Matazu da wani yanki na ƙaramar hukumar Ɗanmusa. A jawabin sa wajen taron, Fagacin Katsina kuma Hakimin Matazu Alhaji Iro Maikano ya nuna jin daɗin sa a kan wannan sulhu da a kayi tare da yan uwa Fulani, da kuma yin kira a garesu da a yafe ma juna a haɗu…
Read More
An yi sulhu da ‘yan bindiga a ƙananan hukumomin Sabuwa, Ɗandume da Faskari a Jihar Katsina

An yi sulhu da ‘yan bindiga a ƙananan hukumomin Sabuwa, Ɗandume da Faskari a Jihar Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina A ƙoƙarin samar da zaman lafiya mai ɗorewa, a Jihar Katsina, ƙananan hukumomin Sabuwa, Ɗandume da Faskari sunyi zaman sasanci da yan bindiga na yankin. Shugabannin ƙananan hukumomin Sabuwa, Ɗandume da Faskarisu ka jagoranci sasanci da 'yan bindigan da ke da sansani a garuruwan Kabalawa Dugun Ma'azu dake cikin ƙaramar hukumar Sabuwa. Daga ɓangaren ƴan bindigar da su ka jagoranci sasancin, akwai Kabiru, Kachalla Rusku, Kachalla Murtala, Kachalla Mai saje, Kachalla Dawa da dai sauran su. Shugabannin ƴan bindigar na bayyana jin daɗin su akan sasanci tare da yaba ma shugabannin ƙananan hukumomin akan dattako…
Read More
Kwamitin aikin hajjin 2025 na Jihar Filato ya miƙa rahotonsa ga Gwamna Mutfwang

Kwamitin aikin hajjin 2025 na Jihar Filato ya miƙa rahotonsa ga Gwamna Mutfwang

Daga HABU ƊAN SARKI a Jos Kwamitin da aka ɗora wa alhakin shiryawa da gudanar da hidimar aikin hajjin bana da ya gabata, ƙarƙashin hukumar kula da jin daɗin Alhazai ta Jihar Filato, ya miƙa wa Gwamnan jihar Caleb Manasseh Mutfwang rahoton sa. Da yake miƙa rahoton, Amirul Hajj na bana, Mai Martaba Sarkin Wase, Dr Muhammadu Sambo Haruna na ll ya bayyana jin daɗinsa da yadda aka samu nasarori masu yawa a wannan shekarar fiye da a shekarun baya. Sannan ya yaba da irin haɗin kan da sauran ýan kwamitin da hukumar Alhazai ta jiha suka ba shi, wanda…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta gana da MACBAN kan shanun da ke yawo a titunan Abuja

Gwamnatin Tarayya ta gana da MACBAN kan shanun da ke yawo a titunan Abuja

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD A ƙarshen makon da ya gabata ne Gwamnatin Tarayya, Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, da sauran masu ruwa da tsaki suka gana da shugabannin ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti-Allah (MACBAN) kan rahotannin da ake samu na cewa shanu suna yawo a titunan Abuja. An gudanar da zaman tattaunawar ne a babban masallacin ƙasa da ke Abuja, a wajen Sarkin Musulmi, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin amintattu na ƙungiyar MACBAN. Taron ya kuma samu halartar manyan masu ruwa da tsaki da suka haɗa da Ministan Dabbobi, Alhaji Idi Mukhtar Maiha, babban sakataren hukumar kula da ilimin…
Read More
Manoma sun koka kan tsadar taki a Nijeriya

Manoma sun koka kan tsadar taki a Nijeriya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Rahotanni daga jihohin da ke samar da yawancin kayan amfanin gona sun tabbatar da cewa manoma na barin shukan masara da shinkafa saboda tsadar takin zamani. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamnatin Tarayya ke cewa ta raba takin zamani kyauta ga manoma. Manema labarai sun tattauna da manoma da sauran masu ruwa da tsaki domin jin halin da suka shiga kan tsadar taki a bana. Wasu daga cikin manoman sun bayyana cewa, yanzu haka ba za su iya sayen buhun taki ba saboda hauhawar farashin sa wanda ya kai sama da N50,000 a…
Read More
Sama da mutum miliyan 3.7 ke fuskantar yunwa a Arewa maso Gabashin Nijeriya – ICRC

Sama da mutum miliyan 3.7 ke fuskantar yunwa a Arewa maso Gabashin Nijeriya – ICRC

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar Ba Da Agaji ta ƙasa da ƙasa ta Red Cross ta koka kan ƙaruwar yunwa a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya, inda sama da mutane miliyan 3.7 ke fuskantar ƙarancin abinci a halin yanzu. A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, ƙungiyar ta ce, yawancin waɗanda abin ya shafa manoma ne da a da su ke ciyar da al’ummarsu amma a yanzu su na fafutukar rayuwa. Rikicin da aka kwashe shekaru ana yi ya raba iyalai da muhallansu, da rashin samun filayen noma, da kuma kawo cikas ga samar da abinci a…
Read More