ukarofi

12736 Posts
Arewa ba za ta iya karɓar mulki ba a 2027 – Gwamna Bago

Arewa ba za ta iya karɓar mulki ba a 2027 – Gwamna Bago

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago, ya bayyana cewa babu wata dama ta sake dawowa Arewa da mulki 2027, yana mai jaddada cewa dole ne a bar Shugaba Bola Tinubu ya kammala wa’adin mulkinsa na tsawon shekaru takwas. Da yake magana a shirin Sunday Politics na TɓC tare da Femi Akande, Bago ya ce waɗanda ke tada jijiyoyin wuya a Arewa bayan shekaru biyu kacal na mulkin Tinubu, suna yin rashin imani ne da kuma adawa da tsarin shiyya-shiyya da ya sa Nijeriya ta ɗore. "Saboda kuka da babbar murya, mutumin nan ya shafe shekaru…
Read More
Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima

Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jigo a Jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi zargin cewa gwamnatin Shugaban ƙasa Bola Tinubu ba ta da niyyar gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe a 2027. Galadima ya bayyana hakan ne ranar Talata a wata hira da aka yi da shi a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise Tɓ, inda ya ce gwamnatin da jam’iyyar APC ke jagoranta ta kankane cibiyoyin gwamnati don amfaninta. “Wannan gwamnati ba ta shirya gudanar da zaɓen adalci ba. Daga yadda suke tafiyar da al’amura, za ka gane yadda suke tarwatsa jam’iyyun siyasa. Wannan yana nuna…
Read More
Shawarwari ga matasa masu shirin aure (1)

Shawarwari ga matasa masu shirin aure (1)

Assalamu Alaikum, da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai. Da farko dai yana da kyau a fahimci cewa ɗaura aure yana nufin ƙulla wata alaƙa ce da Ubangiji Maɗaukakin Sarki ya yi umarni da ita. Gaskiya ne cewa (aure) ya kasance daga cikin ɗabi'u na ɗan Adam, to amma duk da hakan Allah Maɗaukakin Sarki ya tsarkake wannan alaƙa wacce daga ƙarshe take haifar da abubuwa masu kyau. Don haka bai kamata a ɗauki wannan alaƙa a matsayin wani abu mara muhimmanci ba. ɗaya daga cikin munanan ayyukan da wasu suka yi shi ne riƙon sakainar kashin da suke…
Read More
Rayuwar gidan haya

Rayuwar gidan haya

Ina magana ne daga Jiharmu, Jihar Katsina domin a shekaru 30 zuwa sama duk wanda zai yi aure ba zai bazama neman gida ko ɗakin haya kamar a yau ba. Na samu kaina a zaman haya daga shekara ta 2000 zuwa 2002 wanda kafin in mallaki nawa gidan na fuskanci yadda rayuwar haya ta ke. Dillalai a kula; haka nan ku waɗanda ke gina gidaje ku ba da haya duka a riƙa sanya tausayi da sauƙaƙawa. Mutum ne zai zo neman gida ko ɗaki na haya za a gindaya masa wasu sharuɗɗa duka ya cika kuma kuɗi ya bada amma…
Read More
Dalilan da ya sa nake son sake fasalin Kannywood – Daraktan Wata Shida, Kamilu Dan-Hausa

Dalilan da ya sa nake son sake fasalin Kannywood – Daraktan Wata Shida, Kamilu Dan-Hausa

"Bada umarni ba wai kyamara da fitilu ba ne kawai, fahimtar al'adun mutane ne da ƙarfin labari" Daga IBRAHIM HAMISU Kamilu Ibrahim da aka fi sani da ɗan Hausa fitaccen darakta ne a masana'antar fim ta Kannywood, ya bayar da umurni a fina-finai da dama cikin akwai 'Tataɓurza', 'Mijin Hajiya', 'Dan Jarida', 'Lulu da Andalu', 'Wata Shida' da kuma sabon fim ɗin Rahama Sadau mai suna 'Amaryar Lalli'. A tattaunawarsa da Ibrahim Hamisu a Kano za ku ji tarihin rayuwarsa da kuma irin burin da da yake da shi na sauya akalar fina-finan Hausa. MANHAJA: Wane ne Dan Hausa? DAN…
Read More
Tasiri da ƙalubalen sulhu da ’yan bindiga

Tasiri da ƙalubalen sulhu da ’yan bindiga

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Wani labari da ya mamaye kafafen sadarwa a cikin wannan mako mai ƙarewa shi ne na batun sulhu da aka yi da  wani gungun wasu ’yan bindiga a ƙaramar Hukumar Faskari ta Jihar Katsina ƙaraashin jagorancin babban ƙasurgumin ɗan bindigar nan, Ado Alero. Wannan na zuwa ne sakamakon yadda rashin tsaro ke ƙara ta'azzara a jihohin Katsina, Zamfara, Sakkwato, da wasu sassan jihohin Kebbi, Naija, Filato, Binuwai, da Taraba. Wannan ya haɗa shiyyoyin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya. Rayuka da dama sun salwanta sakamakon hare-haren ’yan bindiga kan jama'ar ƙauyuka da birane a waɗannan…
Read More
An naɗa Dakta Basira Umar matsayin babbar magatakarda a babbar kotun Katsina

An naɗa Dakta Basira Umar matsayin babbar magatakarda a babbar kotun Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ma'aikatar Shari'a ta Jihar Katsina ta amince da naɗa Dakta Basira Umar a matsayin babbar magatakardar babbar Kotun Jihar Katsina, (Chief Registrar Of Katsina State High Court), Wannan shine karo na farko da aka naɗa mace a wannan matsayi tun da aka ƙirƙiro Jihar Katsina a shekarar 1987. A wata takardar sanar wa ɗauke da sa hannun jami'in hulɗa da jama'a na babban kotun Musa Usman,ya ce kafin naɗa Dakta Basira a wannan matsayi,itace daraktan kula da kotunan sasanci a jihar. Ta sami wannan muƙami ne bayan da tsohon babban magatakardar babban kotun Mustapha Hassan…
Read More
Tokyo 2025: Ajayi ya kafa wa Nijeriya sabon tarihi a gasar tseren gudu

Tokyo 2025: Ajayi ya kafa wa Nijeriya sabon tarihi a gasar tseren gudu

Ɗan wasan tsalle-tsalle da guje - guje, Kayinsola Ajayi ya kafa tarihin zama ɗan Nijeriya na farko da ya kai wasan ƙarshe a gasar ƙasashen Duniya da ke ci gaba da gudana a birnin Tokyo na ƙasar Japan, bayan shafe shekaru 18. Ajayi wanda ya yi tseren Gudun Mita 100, ya ƙarƙare a mataki na biyu a wasan dab da na kusa da na ƙarshe wato semi final, da ya kammala Gudun cikin daƙiƙa 9 da digo 93 a gasar ta 'Tokyo World Championship'. Nasarar ƙarewa a matakin na biyu, ya bashi damar zuwa wasan ƙarshe da ya sa ya…
Read More
Tsohon ɗan wasan Barcelona Abidal ya musanta jita-jitar mutuwarsa

Tsohon ɗan wasan Barcelona Abidal ya musanta jita-jitar mutuwarsa

Tsohon ɗan wasan bayan Barcelona Eric Abidal ya musanta jita-jitar mutuwarsa da ya karaɗe shafukan sada zumunta a wannan makon. Labaran da aka yi ta yaɗawa  a shafukan sada zumunta sun nuna cewa Eric Abidal ya mutu ne bayan matsalar taɓarɓarewar lafiya da ya fuskanta sakamakon dashen hanta da aka yi masa a shekarar 2025, lamarin da ya sa dole ya fito ya bayyana cewa yana da rai. A shekarar 2011 ce gwaji ya fara tabbatar da cewa Abidal mai shekaru 46 ya harbu da cutar dajin hanta. A cikin shekarar aka cire ƙarin daga hantarsa, kana aka masa dashe…
Read More
Flick ya caccaki Sifaniya kan nuna halin ko-in-kula da raunin Yamal

Flick ya caccaki Sifaniya kan nuna halin ko-in-kula da raunin Yamal

Kocin Barcelona, Hansi Flick ya ce ya kamata hukumar ƙwallon kafar Sifaniya ta ɗauki matakin kula mafi inganci, bayan da Lamine Yamal ya ji rauni lokacin da yake buga wa kasar tamaula. Mai shekara 18 ba zai buga wa Barcelona wasa da Valencia ranar Lahadi a gasar La Liga ba, watakila ba zai yi fafatawar da za ta fuskanci Newcastle United ba a makon gobe a Champions League. Haka shima Frenkie de Jong ya ji rauni a lokacin da yake buga wa Netherlands tamaula, kenan shima ba zai buga wasan Valencia ba. Sai dai Marc Bernal, mai shekara 18 zai…
Read More