ukarofi

12738 Posts
Kano: Hukumar Hizba ta warware ƙorafe-ƙorafen aure 62 a shekarar 2024 

Kano: Hukumar Hizba ta warware ƙorafe-ƙorafen aure 62 a shekarar 2024 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta samu ƙorafe-ƙorafe har 83,776, kuma 621 da ta warware sun dangancin aure ne a shekarar 2024. Kwamandan rundunar, Sheikh Amin Ibrahim Daurawa, ne ya bayyana hakan yana mai cewa hukumar ta samu cigaba tun bayan zuwan gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf a ranar 29 ga Mayun 2023. Ya ce, hukumar ta farfaɗo da ayyukanta masu yawa ciki har da lalata dubunnan kwalaben barasa bayan samun umarnin kotu kamar yadda jaridar Kadaura24 ta rawaito. Rundunar ta kuma yi nasarar musuluntar da mutane da dama tare da raba…
Read More
Gwamnatin Nijeriya ta ƙara kuɗin yin fasfo zuwa N100,000 da kuma N200,000

Gwamnatin Nijeriya ta ƙara kuɗin yin fasfo zuwa N100,000 da kuma N200,000

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya ta kara farashin yin fasfo daga ranar day aga watan Satumbar 2025. A cewar wata sanarwa da Kakakin hukumar, ACI AS Akinlabi ya fitar ranar Alhamis, hukumar ta ce karin ya shafi iya wadanda suka nemi fasfo din a iya cikin Najeriya ne. “A yanzu duk fasfo mai shafi 32 ya koma N100,000 wanda zai yi shekara biyar kafin ya daina aiki, yayin da mai shafi 64 da zai shekara 10 ya koma N200,000,” in ji sanarwar. Sai dai sanarwar ta ce har yanzu kudaden da…
Read More
Baba Goni ya yaba wa Blueprint bisa karrama Gwamna Buni a matsayin gwarzon gwamna 

Baba Goni ya yaba wa Blueprint bisa karrama Gwamna Buni a matsayin gwarzon gwamna 

Daga GAMBO ISA a Abuja Shugaban ƙaramar Hukumar Fune a Jihar Yobe, Honorabul Baba Goni Mustapha, ya yaba mahukuntan gidan Jaridun Blueprint bisa karrama Maigirma Gwamna Mai Mala Buni, a matsayin Gwarzon Gwamna na shekarar 2024. A wata takardar manema labarai da ya raba wa jaridar Blueprint, Hon. Mustapha ya bayyana karramawar da aka bayar a otal ɗin Abuja Continental (tsohon otal ɗin Sheraton) a ranar 22 ga Yuli, 2025, a matsayin wacce ta cancanci. A cewarsa, nasarorin da Gwamna Buni ya samu daga muhimman sassa daban-daban da suka haɗa da bunƙasa cigaban ɗan Adam, ababen more rayuwa, hanyoyi, ilimi,…
Read More
Yaƙi da bautar da yara ƙanana

Yaƙi da bautar da yara ƙanana

Sanarwar da ƙungiyar ƙwadago ta Majalisar ɗinkin Duniya (ILO) ta yi na baya-bayan nan ya nuna cewa, sama da yara miliyan 152 ko kusan ɗaya cikin yara 10 a duniya na fama da tilastawa wajen aure ko yin aikin ƙwadago wanda hakan ba wai kawai abin baƙin ciki ba ne amma har da nuna rashin mutuntaka. ƙungiyar ta ce, ƙananan yara sama da miliyan 10 ke aiki a matsayin baran gida ko kuma masu hidima a ƙasashen duniya, wanda ake danganta shi da bauta. ƙididigar da hukumar ta bayar cikin makon da ya gabata, ya nuna cewa, cikin adadin kashi…
Read More
Babu ɗaya daga cikin buƙatunmu da gwamnati ta aiwatar — Shugaban ASUU

Babu ɗaya daga cikin buƙatunmu da gwamnati ta aiwatar — Shugaban ASUU

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaban ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya (ASUU), Farfesa Chris Piwuna, ya ce Gwamnatin Tarayya ba ta aiwatar da ɗaya daga cikin yarjejeniyar da ta ƙulla da ƙungiyar ba. Ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin hira da gidan talabijin na Trust Tɓ. Farfesa Piwuna, ya ce ASUU a koyaushe na zaɓar tattaunawa da jami’an gwamnati a matsayin mafita. Amma duk da cewa sun cimma matsaya kan batutuwa masu muhimmanci kamar kuɗaɗen gudanarwa, albashi, ’yancin malamai, ‘yancin jami’o’i, da sake duba wasu dokoki, ba a ɗauki mataki kan kowanne ba. “Babu saɓani a tsakaninmu…
Read More
NLC ta yaba wa Gwamna Uba Sani bisa dawo da malaman makarantar da El-Rufai ya kora

NLC ta yaba wa Gwamna Uba Sani bisa dawo da malaman makarantar da El-Rufai ya kora

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Kungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), reshen Jihar Kaduna, ta yaba wa Gwamna Uba Sani bisa dawo da wasu daga cikin malaman makaranta da gwamnatin Nasir El-Rufa'i ta kora a jihar. Shugaban NLC na Jihar Kaduna, Ayuba Suleiman ne ya yi wannan yabo yayin da ya ke jawabi ga mambobin ƙungiyar ‘Yan Jaridu Masu Bincike ta ƙasa (NGIJ) wadanda ke jihar domin duba yadda ake tafiyar da mulki. A tuna cewa gwamnatin da ta gabata Kaduna karkashin Nasir El-Rufai ta kori malamai sama da dubu 23, ciki har da tsohon Shugaban Kungiyar Malaman Makaranta ta…
Read More
Honorabul Yakubu  Suleiman ya yaba wa jaridar Blueprint bisa karrama Gwamna Buni

Honorabul Yakubu  Suleiman ya yaba wa jaridar Blueprint bisa karrama Gwamna Buni

Daga GAMBO ISA a Abuja Dan majalisar da ke wakiltar Fika ta Gabas a majalisar dokokin jihar Yobe, Honorabul Alhaji Yakubu Suleiman, ya taya Gwamna Mai Mala Buni murnar zama Gwarzon Gwamnan Jaridar Blueprint na shekarar 2024. A wata takardar manema labarai da aka rabawa Blueprint a Abuja, Hon. Suleiman ya yabawa mahukuntan gidan jaridar bisa karramawar da Gwamna Buni ya samu, inda ya bayyana karramawar a matsayin wacce ta dace. An gudanar da bikin bayar da kyautar ne a otal ɗin Abuja Continental (tsohon otal din Sheraton) a ranar 22 ga Yuli, 2025. Hon. Suleiman ya bayyana cewa ana…
Read More
Na ɗauki alhakin hatsarin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna – Shugaban NRC

Na ɗauki alhakin hatsarin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna – Shugaban NRC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Nijeriya (NRC), Kayode Opeifa, ya ce ya ɗauki alhakin hatsarin jirgin ƙasa da aka samu ranar Talata, wanda aka samu lokacin da jirgin ya kama hanya daga Abuja babban birnin ƙasar zuwa Kaduna. A tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels, Opeifa ya ce ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen binciken abin da ya sanya jirgin ya kauce daga kan layi. “Bayan neman gafarar 'yan Nijeriya, a matsayina na shugaban hukumar, na ɗauki cikakken alhakin abin da ya faru,” inji shi. Opeifa ya tabbatar da cewa duk…
Read More
Yadda wani ɗan sanda ya harbe soja a Bauchi

Yadda wani ɗan sanda ya harbe soja a Bauchi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wani jami’in ’yan sandan kwantar da tarzoma (MOPOL) mai muƙamin Insfekta ya harbe wani soja har lahira a garin Futuk, da ke ƙaramar Hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi. Manhaja ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne bayan wata taƙaddama da ta taso kan wata mota mai ɗauke da ma’adinai da ake zargin ta wani kamfanin haƙar ma’adinai na ƙasar Sin ce. Mai riƙon muƙamin Daraktan Hulɗa da Jama’a na rundunar soji, Laftanar Solomon Atang Hallet, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kama ɗan sandan da ake zargi, kuma ana ci gaba…
Read More
Tinubu ya umurce ni na yi aiki da Ganduje – Sabon Shugaban APC

Tinubu ya umurce ni na yi aiki da Ganduje – Sabon Shugaban APC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dokta Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarce shi da ya ci gaba da haɗa kai da magabacinsa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, domin samun haɗin kan jam’iyyar da kwanciyar hankali. Manhaja ta ruwaito cewa Yilwatda ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a lokacin da Ganduje ya kai masa ziyarar ta'aziyyar rasuwar mahaifiyarsa. Ya jaddada cewa duk da ya gaji Ganduje, jagorar tsohon shugaban da gogewar siyasa za su yi matuƙar amfani wajen samun nasarar mulkinsa. "Maigirma Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya roƙe…
Read More