29
Aug
Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi Gwamnatin jihar Kebbi ta ƙaddamar da kwamiti don soma shirye-shiryen yadda za a gudanar da bikin kamun kifin ƙasa da ƙasa na Argungu da za yi a watan Fabrairu na shekarar 2026. Babban daraktan gudanarwa na bikin Alhaji Sufyanu Garba Bena ne bayyana haka a garin Birnin Kebbi ranar Talatar da ta gabata. Ya bayyana cewa tuni Gwamna Malam Nasir Idris ya umarci babban kwamitin shirye-shiren bikin ƙarƙashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar Sanata Umar Abubakar Argungu (Tafidan Kabi) da ya gaggauta kammala duk wani shiri da ya dace don ganin bikin na shekarar 2026…
