28
Aug
Daga HABU Ɗan SARKI a Jos Reshen ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi ta Nijeriya (ALGON) ya sake jaddada cikakkiyar sadaukarwarsa wajen bunƙasa dukkanin ƙananan hukumomi a dukkan faɗin jihar, tare da sake jaddada goyon baya ga jagorancin Gwamna Caleb Mutfwang wanda suka ce yana kawo sabbin sauye-sauye na cigaba a jihar. Shugabannin ƙananan hukumomi guda 17 sun bayyana cewa gwamnatin Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang ƙarƙashin jam'iyyar PDP, ta samar musu da kyakkyawan yanayi da nuna jagoranci nagari, ƙwarewa a harkar shugabanci, da inganta rayuwar mutanen karkara, wanda yake daga cikin ƙudirorin gwamnati mai ci a Jihar Filato. Shugabannin sun bayyana haka…
