27
Aug
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Masarautar Daura a Jihar Katsina ta gudanar da gagarumin bikin ranar Hausa ta duniya domin ƙarfafa harshen Hausa da ɗaukaka harshen Hausa da kuma al'adun Hausawa. Taken ranar Hausawa an sa mata suna "Al'adun mu jiya,yau da gobe,"ya gudana a fadar mai martaba Sarkin Daura Umar Farouk Umar. Masu riƙe da sararin gargajiya, makaɗa da waƙe waƙe da maza da mata da kuma mahaya dawaki da suka zo daga sassa daban daban daga ciki da wajan jihar da kuma suka halarci bikin. Muƙaddashin Gwamnan wanda ya sami wakilcin mai ba gwamna shawara kan masarautu Usman…
