ukarofi

12738 Posts
Majalisar Zartarwa ta ƙungiyar RTEAN ta dakatar da Sakatare Janar, ta kafa kwamitin bincike

Majalisar Zartarwa ta ƙungiyar RTEAN ta dakatar da Sakatare Janar, ta kafa kwamitin bincike

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kungiyar Ma’aikatan Motocin Sufuri ta Nijeriya (RTEAN) na son sanar da mambobinta, masu ruwa da tsaki, da sauran jama’a cewa an gudanar da taron majalisar zartarwa na gaggawa (NEC) a ranar Laraba 13 ga watan Agusta 2025 a sakatariyar ƙungiyar, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙungiyar ya tanada da kuma ƙudirin yin gaskiya, da riƙon amana, a cikin shugabanci. Taron ya kasance ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaba na ƙasa. Muhammad Abu Bakr Bishara, yana bin izini bisa ga ƙa'idojin aiki na ƙungiyar. A yayin taron, Majalisar ta NEC ta tattauna sosai kan al’amuran da suka…
Read More
An kama basarake kan yi wa ’yar shekara 12 fyaɗe a Gombe

An kama basarake kan yi wa ’yar shekara 12 fyaɗe a Gombe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta cafke wani basarake mai suna Mohammed Tukur ɗan shekara 55 a ƙauyen Sabon Gari da ke yankin Zambuk na ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba, bisa zargin yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyaɗe. Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata. Ya ce abin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na daren ranar 9 ga Agusta, 2025, lokacin da ake zargin ya yaudari yarinyar wadda ya kaita wani wuri da babu idon jama’a…
Read More
Gwamnatin Tarayya na barazanar korar ma’aikata 3,598 bisa gaza gabatar da takardun ɗaukar aiki

Gwamnatin Tarayya na barazanar korar ma’aikata 3,598 bisa gaza gabatar da takardun ɗaukar aiki

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ma'aikatan Gwamnatin Tarayyar Nijeriya guda 3,598 su na fuskantar barazanar kora saboda gaza gabatar da takardun ɗaukarsu aiki. Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya (FCSC) ta umurci ma’aikata, waɗanda suka gaza zuwa a tantance su a 2021, su gabatar da kansu domin tabbatar da sahihancin ɗaukar su aiki. An tsara tantance ma'aikatan daga ranar 18 zuwa 28 ga watan Agusta, 2025, domin tabbatar da ingancin takardun shaidar ɗaukar aikinsu. A cewar FCSC, duk wanda ya gaza halartar wannan tantancewa da aka shirya, za a ɗauka yana riƙe da jabun takardar ɗaukar aiki. Hukumar ta umurci duka…
Read More
Shugaban ƙaramar hukumar Jakusko ya yaba wa Blueprint bisa karrama Gwamna Buni

Shugaban ƙaramar hukumar Jakusko ya yaba wa Blueprint bisa karrama Gwamna Buni

Daga GAMBO ISA a Abuja Shugaban ƙaramar Hukumar Jakusko a jihar Yobe, Hon. Umaru Aguwa, ya yaba wa hukumar gudanarwa Jaridar Blueprint bisa karrama Gwamna Mai Mala Buni. Idan dai za a iya tunawa, an zaɓi gwamnan ne tare da ba shi lambar yabo a matsayin Gwamnan Jaridun Blueprint na shekarar 2024 a wani bikin karramawar da aka yi kwanan nan a Abuja. A cikin wata sanarwar manema labarai da ya raba wa Blueprint a ranar Juma’a, Aguwa ya bayyana nasarorin da gwamnan ya samu a fannin ci gaban jama’a, samar da ababen more rayuwa, ilimi, ICT, asibitoci, bunƙasar tattalin…
Read More
Sufeto Janar ya tsawaita batun lasisin gilashin mota mai duhu zuwa 2 ga Oktoba

Sufeto Janar ya tsawaita batun lasisin gilashin mota mai duhu zuwa 2 ga Oktoba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, ya amince da ƙara wa’adin yin lasisi ga gilashin moto mai duhu zuwa ranar 2 ga Oktoba. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DCP Olumuyiwa Adejobi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Litinin. Ya ce amincewar ta biyo bayan yawaitar aikace-aikacen ta hanyar tashar hukuma, wanda ke nuna ƙaruwar bin umarnin jama'a. Mista Adejobi ya ce manufar ita ce a ba da isasshen lokaci don yin nazari sosai kan aikace-aikacen don tabbatar da cewa an ba da izinin ne kawai ga…
Read More
Dalilin da ya sa Benin ke samun lantarki daga Nijeriya duk da ƙarancinsa – ECN

Dalilin da ya sa Benin ke samun lantarki daga Nijeriya duk da ƙarancinsa – ECN

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Duk da ƙarancin wutar lantarki da ke ci gaba da addabar miliyoyin ‘yan Nijeriya, Hukumar Wutar Lantarki ta Nijeriya (ECN) ta ce, samar da wutar lantarki ga ƙasashe makwabta irin su jamhuriyar Benin ya kasance wani muhimmin tsari na tattalin arziki. A wata hira da gidan Talabijin na Channels, Darakta Janar na ECN, Mustafa Abdullahi, ya ce kusan kashi 6 na wutar lantarkin da Nijeriya ke samarwa ke zuwa Jamhuriyar Benin, galibi daga madatsun ruwa da ke kusa da kan iyaka. "A wani lokaci, Jamhuriyar Benin ta so ta kafa dam kusa da namu, wanda zai…
Read More
Atiku ya jinkirta karɓar katin ADC ana tsaka da raɗe-raɗin takarar Jonathan a PDP

Atiku ya jinkirta karɓar katin ADC ana tsaka da raɗe-raɗin takarar Jonathan a PDP

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya jinkirta karɓar katin zama cikakken memba a jam'iyyar ADC a hukumance, lamarin da ya janyo cece-kuce kan rikicin siyasa da ya kunno kai da tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, wanda ake raɗe-raɗin zai iya koma wa takarar shugaban ƙasa na 2027 a Jam’iyya PDP. Atiku wanda kwanan nan ya fice daga jam’iyyar PDP bayan da aka daɗe ana taƙaddama, an shirya zai karɓu katin zama ɗan jam’iyyar ADC a mahaifarsa ta Jada, jihar Adamawa a ranar 6 ga watan Agusta. Bikin, wanda aka shirya yi a ranar Laraba, 6…
Read More
Fayemi ya musanta iƙirarin Amaechi kan haɗakar ADC

Fayemi ya musanta iƙirarin Amaechi kan haɗakar ADC

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ofishin yaɗa labarai na Dekta Kayode Fayemi, tsohon gwamnan Ekiti, ya yi watsi da wata iƙirari da ake yaɗawa daga Rotimi Amaechi na cewa mutanen biyu ne suka kafa sabuwar jam'iyyar haɗaka ta ADC. Ameachi tsohon Gwamnan Ribas ne kuma tsohon Ministan Sufuri a ƙarƙashin Marigayi tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban ofishin yaɗa labarai na Fayemi, Malam Ahmad Sajoh, ya fitar ranar Lahadi a Abuja. Sajoh ya ce, babu wata kwakkwarar hujja, da suka haɗa da bidiyo ko rahotanni masu inganci da za su iya tabbatar da…
Read More
Yadda manoma ke kokawa a daminar bana

Yadda manoma ke kokawa a daminar bana

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Manoman a Nijeriya na ci gaba da bayyana damuwa a kan abin da suka kira koma bayan da ake ta samu na noman masara da shinkafa a ƙasar, lamarin da suka ce yana barazana ga makomar sana'ar su. Sun koka da tsadar kayan aikin gona, da kuma shigar da masara da shinkafa da ake yi cikin Nijeriya daga ƙasashen waje. Manoman sun bayyana fargabar cewa lamarin zai haifar masu da gagarumar asara a kakar bana, saboda haka kuma mafi yawansu ba za su iya noma masara da shinkafa ba a daminar baɗi, al'amarin da…
Read More
Za a gyara tarbiyyar tubabbun ’yan daban Kano

Za a gyara tarbiyyar tubabbun ’yan daban Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya shawarci matasan da ake ribatarsu a matsayin ’yan daban siyasa da a yanzu suka tuba da su guji tashin hankali, yana tabbatar musu da shirye-shiryen gwamnatinsa na gyara tarbiyyarsu tare da mayar da su cikin al’umma. Gwamnan ya yi wannan alƙawari ne a taron wuni ɗaya da aka gudanar tare da shugabannin rukunan ’yan daban da suka tuba a ƙarƙashin Shirin Safe Corridor. Gwamnan, wanda Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Waiya, ya wakilta, ya ce: “Ba za a sake ɗaukar makami da sunan faɗan siyasa…
Read More