ukarofi

12738 Posts
Ƙungiyar manoma ta nuna takaicinta kan yaɗuwar taki mara kyau a Jigawa

Ƙungiyar manoma ta nuna takaicinta kan yaɗuwar taki mara kyau a Jigawa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse Ƙungiyar Manoma ta ƙasa (AFAN), reshen Jihar Jigawa ta nuna damuwarta kan yadda ake samun yawaitar gurɓataccen takin zamani a kasuwanni, tare da samun yawaitar hauhawar farashin takin tare da faɗuwar farashin kayan anfanin gona. Shugaban ƙungiyar reshan jihar, Injiniya Auwalu Garba Ibrahim ne ya tabbatar da hakan jim kaɗan da gudanar da taron ƙungiyar na jihar a Birnin Dutse yayn da yake zantawa da manema labarai. Ya buna takaicinsa kan yadda taki marar kyau yake neman cika kasuwanni a faɗin jihar, wadda hakan na iya zama wata barazana ga manoma, don haka ƙungiyar…
Read More
Ƙungiyar Fulani ta bada shawarar hanyar samar da zaman lafiya a Filato

Ƙungiyar Fulani ta bada shawarar hanyar samar da zaman lafiya a Filato

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ƙungiyar Tattaunawa Don Kawo Mafita da Maslaha ta Fulani (FDF), reshen jihar Filato, ta bada shawara don samun zaman lafiya a jihar. A cikin sanarwar da ta fitar a ƙarshen taron da aka yi a ranar Asabar, ƙungiyar ta ce a shirye ta ke ta ba da damar zaman lafiya idan har gwamnati da 'yan jihar suka cika sharuɗɗan ta. Sanarwar wacce shugaban FDF, Alhaji Shehu Buba da Sakatare Salihu Musa Umar suka sanya wa hannu, mai taken ‘Buɗaɗɗiyar Matsayin Al’ummar Fulani a Jihar Filato, ta ƙunshi sharuɗɗan da suka haɗa da samar da ayyukan yi…
Read More
Mu ƙarfafawa ’ya’ya mata gwiwa kan neman ilimi

Mu ƙarfafawa ’ya’ya mata gwiwa kan neman ilimi

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Na cika da murna da farin ciki, sakamakon samun labarin nasarar da wasu ’yan mata uku ’yan Nijeriya suka samu a gasar gwada gwanintar Turanci da muhawara da aka gudanar a birnin Landan, ƙarƙashin wata ƙungiyar ƙasa da ƙasa ta TeenEagle Global. ƙasashen duniya 69 ne suka samu halartar wannan babbar gasa ta matasa ’yan ƙasa da shekara 20. Nafisa Abdullahi Aminu, Rukayya Muhammad Fema, da Hadiza Kalli Kashim su ne 'yan matan da suka samu nasara a wannan gasa. Kuma wani ƙarin abin burgewa shi ne kasancewar su ’yan Nijeriya daga Jihar Yobe a yankin…
Read More
Rundunar ‘yan sandan Kano ta yaba wa Sheikh Nuhu Idris Fallata kan tallafin kayan aikin tsaro

Rundunar ‘yan sandan Kano ta yaba wa Sheikh Nuhu Idris Fallata kan tallafin kayan aikin tsaro

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Rundunar ƴan sanda ta Jihar Kano ta yi godiya ta musamman ga Sheikh Nuhu Idris Fallata, bisa tallafin kayan aikin tsaro da ya bayar ga kwamitin bijilanti na jiha. Taron miƙa tallafin da ya gudana a Officers Mess da ke Bompai Kano, ranar Alhamis. Tunda farko a jawabinsa, wakilin Sheikh Nuhu Idris Fallata, Ambasada Aliyu Lawan Saulawa, ya miƙa kayan tallafin ga kwamishinan ƴan sanda na Kano, inda ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin gwamnati da al’umma wajen magance matsalolin tsaro, musamman ma ganin yadda lamarin ke ƙara ta'azzara a birnin Kano. Ambasada Saulawa ya…
Read More
Zaɓen cike gurbi: ‘Yan sanda a Kano sun cafke matasa 200 masu neman tada tarzoma

Zaɓen cike gurbi: ‘Yan sanda a Kano sun cafke matasa 200 masu neman tada tarzoma

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Fiye da matasa 200 ne suka faɗa komar jami'an tsaro a yayin zaɓen maye gurbi a ƙaramar hukumar Shanono-Bagwai da Ghari-Tsanyawa. Kwamishinan ƴan sanda a jihar ta Kano Ibrahim Bakori ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a Kano a ranar Asabar. A saƙon da mai magana da yawun rundunar ƴan sandan reshen jihar ta Kano SP Abdullahi Kiyawa ya aika wa manema labarai yace matasan da aka kama bisa yunƙurin kawo tarzoma a yayin zaɓukan sun kai 288 an kuma kama su da makamai kala-kala da suka haɗar da bindigogi da adda da…
Read More
An yi kira ga Gwamna Raɗɗa ya sabunta cinikayya da ƙungiyar dillalan jaridu a Katsina

An yi kira ga Gwamna Raɗɗa ya sabunta cinikayya da ƙungiyar dillalan jaridu a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Anyi kira ga Gwamna Dikko Raɗɗa da ya dawo da shirin nan na sayen jaridu a wajen ya'yan ƙungiyar a Katsina. Gwamnatin Katsina ta daɗe tana sayen duk wata jarida da aka kawo Katsina,inda ake aikawa ofishin gwamna da mataimakin sa da sauran wasu mahimman ma'aikatun gwamnati. A wajen wasu mambobi na ƙungiyar gwamnati ke saye inda a karen wata a biya. To sai dai daga baya gwamnati ta tsaida saye wanda hakan a cewar Muhammad Rabi'u wanda ke sayar da jaridu a Sabon Layi Katsina ya jefa mafi yawan ya'yan ƙungiyar cikin halin ƙuncin…
Read More
Zaɓen Kano: Shirye-shirye sunyi nisa wajen fara jefa ƙuri’a a ƙananan hukumomin Ghari da Ɓagwai

Zaɓen Kano: Shirye-shirye sunyi nisa wajen fara jefa ƙuri’a a ƙananan hukumomin Ghari da Ɓagwai

Daga RABI'U SANUSI a Kano Yanzu haka shiri yayi nisa dangane da zaɓen cike gurbi da ake gudanarwa a wasu ƙananan mazaɓu na ƙaramar hukumar Ɓagwai na ɗan majalisar jiha da ke Jihar Kano. Ɗaya daga cikin mazaɓun sun haɗa da mazabar Kiyawa dake ƙaramar hukumar Ɓagwai, inda a cikin hotunan nan ke nuna al'umma sun hau layi za a fara tantance su dan su fara jefa ƙuri'a. Haka kuma suma a garin ƴan kifi da ke mazaɓar Ƴan Dadi a yankin ƙaramar hukumar Ghari da a ka fi sani da (KUNCHI) suma sun hau layi dan fara gudanar da…
Read More
Rodri zai sake yin jinyar watanni – Guardiola

Rodri zai sake yin jinyar watanni – Guardiola

Kocin Manchester City, Pep Guardiola ya ce ɗan wasan tsakiyar ƙungiyar, Rodri ya sake jin rauni kuma da wuya ya murmure kafin hutun watan Satumba. ɗan ƙwallon na Sifaniya ya shafe mafi yawan kakar bara a gadon jinya saboda turguɗe gwiwa da ya yi a watan Satumban 2024. Mai riƙe da kambin Ballon d'Or na 2024, ya koma taka leda a matsayin canji a wasan ƙarshe na Man City na gasar Premier League da ta buga da Bournemouth. Sai kuma wasan da Al-Hilal ta fitar da su daga gasar Club World Cup a Amurka, inda aka yi canjinsa daga baya.…
Read More
Tinubu ya amince da kafa sabbin jami’o’i masu zaman kansu guda tara

Tinubu ya amince da kafa sabbin jami’o’i masu zaman kansu guda tara

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ta amince da kafa sabbin jami'o'i masu zaman kansu guda tara a faɗin Nijeriya. Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya sanar da hakan ranar Laraba, yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban ƙasa, bayan taron majalisar zartarswa ta ƙasa da shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a Abuja. Ya ce jami’o’in da aka amince da su sun haɗa da: -Jami’ar Tazkiyah da ke jihar Kaduna -Jami’ar Leadership da ke Babbar Birinin Tarayya, Abuja -Jami’ar Jimoh Babalola a Jihar Kwara -Jami’ar Bridget, Mbaise a Jihar Imo -Jami’ar Greenland da ke Jihar Jigawa…
Read More
An kama makafin bogi suna safarar yara a Abuja

An kama makafin bogi suna safarar yara a Abuja

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wata babbar kotun Abuja a ranar Talata ta bayar da umarnin tsare wasu mata huɗu da ake tuhuma da laifin safarar yara. Rundunar ‘yan sandan ta gurfanar da matan huɗu ne da laifin haɗa baki da kuma safarar yara. Matan waɗanda a yanzu ake tuhumar su ne: Precious Silas mai shekaru 30 da Ngozi Unukwuwa mai shekaru 47 da Chisinau Onukwuagha mai shekaru 40 da Favor Ohebegeim mai shekaru 25. Waɗanda ake tuhumar dukkansu mazauna garin Karimo ne, wata unguwa da ke a yankin kashi uku na Babban Birnin Tarayya Abuja. A ci gaba da sauraron…
Read More