ukarofi

12738 Posts
Matatar Dangote ta fitar da tankokin CNG 4,000

Matatar Dangote ta fitar da tankokin CNG 4,000

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Matatar Mai ta Dangote ta sanar da fitar da iskar gas ɗin da ake kira 'Compressed Natural Gas' (CNG) guda 4,000.  Fitar da tankokin wani ɓangare ne na babban shiri na sauya fasalin mai a Nijeriya. Tun daga ranar 15 ga Agusta, 2025, matatar za ta fara isar da man fetur da dizal kai tsaye zuwa gidajen mai, masana'antu, kamfanonin sadarwa, kamfanonin jiragen sama, da sauran manyan masu saye - ba tare da wasu cajin kuɗaɗe ba. A cewar matatar, ana sa ran shirin zai ceto ‘yan Nijeriya daga kashe sama da tiriliyan N1.7 a duk…
Read More
Cikakken bayani akan kaɗanya

Cikakken bayani akan kaɗanya

Tattarowa: NASIR S. GWANGWAZO Mene ne kaɗanya (Shea Tree)? Kaɗanya wata bishiya ce mai girma da ake samu a yankunan Sudan, Sahel da wasu sassan Afrika ta Yamma. Sunan Turanci: Shea Tree Sunan Kimiyya: Vitellaria paradoɗa Ana fi samun ta a ƙasashe kamar Najeriya, Ghana, Mali, da Burkina Faso. Ana fitar da: ’Ya’yan kaɗanya: Wanda ake fitar da man kaɗanya (Shea butter) Gawayi da itacen kaɗanya: Ana amfani da su a girki da wuta Man kaɗanya (Shea Butter): Man kaɗanya wani mai ne mai kauri, launin fari ko ruwan zinariya da ake tacewa daga ’ya’yan kaɗanya bayan sun bushe da…
Read More
Mutuwar Sadiƙ Gentle ta zama izna ga Gwamna Abba Kabir

Mutuwar Sadiƙ Gentle ta zama izna ga Gwamna Abba Kabir

Daga ALI ABUBAKAR SADIK \Allah ya ji kan wannan matashi Sadiƙ Gentle, hadimin kwankwasiyya. Wato ban san wannan matashi ba sai a Yan watannin nan sakamakon bayan na yi wani rubutu da ya dan yi shura sakamakon Jan hankali da na yi wa Madugun kwankwasiyya wasu ke ganin ba su ji dadin rubutun ba, musamman yan darikar, saboda taken rubutun ‘Kwankwaso a local champion zai kare’. To, bayan nan ne sai na yi ta ganin hoton Sadiƙ Gentle ya na turo min domin na sahale ya zama abokina a Facebook. Na yi biris da bukatarsa na tsawon lokaci saboda na…
Read More
Titin jirgin ƙasa: Kanawa na godiya Shugaba Tinubu

Titin jirgin ƙasa: Kanawa na godiya Shugaba Tinubu

Daga SHEHU MUSTAPHA CHAJI Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya kasance Shugaba dake so da kaunar al’ummar Jihar Kano. Wannan kaunar yayi ta nunawa a aikace tun rantsar dashi a shekarar 2023 ta hanyoyi da dama. ’Yan kwanaki da rantsar da Gwamnatin Kwankwasiyya a Jihar Kano ta kaddamar da Rusau baji ba gani. Shugaba Tinubu ne yabi hanyoyin diplomasiyya ya kawo karshen mafi munin rrusau a tarihin Jihar Kano. Bayan nada Tsohon Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje a matsayin Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Kanawa da dama sun dace da nada su manyan mukaman gwamnati, saboda yawan wadanda ya…
Read More
Cibiyar CBER ta Ingila ta karrama shugabar NSUK

Cibiyar CBER ta Ingila ta karrama shugabar NSUK

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Cibiyar nazarin kasuwanci da tattalin arziki (CBER) da ke ƙasar Ingila ta karrama shugabar babban jami'ar Jihar Nasarawa da ke Keffi (NSUK), Farfesa Sa’adatu Hassan Liman da wata lambar yabo ta musamman da ake kira "fellowship award" a turance. Da yake sanar da hakan a cikin wata sanarwa ta musamman ga manema labarai, mataimakin shugaban jami’ar NSUK ɗin a fannin ilimi, Farfesa Ari Maikano ya bayyana cewa CBER cibiyar bincike ce ta kasuwanci da tattalin arziki na duniya baki ɗaya wadda aka kafa a ƙasar Ingila a shekarar 2006 da manufar bunƙasa, karramawa da…
Read More
PDP ta zargi APC da yin amfani da sojoji wajen hargitsa zaɓen cike gurbi a Zamfara

PDP ta zargi APC da yin amfani da sojoji wajen hargitsa zaɓen cike gurbi a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jam’iyyar PDP mai mulki a Zamfara ta zargi jam’iyyar APC reshen jihar da yin amfani da sojoji a lokacin zaɓen cike gurbin ɗan majalisar dokokin jihar a ƙaramar hukumar Ƙaura Namoda ta kudu. Shugaban jam’iyyar na jiha Jibo Magayaki Jamilu ne ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a ofishin sa a yau Lahadi. A cewarsa, sojojin sun mamaye ƙauyen Sakajiki inda suka fatattaki masu zaɓe daga rumfunan zaɓe, dalilin da ya sa ba a gudanar da zaɓen a yankin ba. “Dalilin da ya sa hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta bayyana zaɓen…
Read More
Zamfara: INEC ta ayyana zaɓen majalisar dokokin Ƙaura Namoda bai kammala ba

Zamfara: INEC ta ayyana zaɓen majalisar dokokin Ƙaura Namoda bai kammala ba

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta bayyana zaɓen majalisar dokokin jihar da aka gudanar a mazabar Ƙaura Namoda ta Kudu a matsayin wanda bai kammala ba. Jami’ai biyu da suka gudanar da zaɓen, Dakta Sa’ad Lawal da Dr. Aminu Idris ne suka sanar da hakan. A cewarsu, za a gudanar da kammala zaɓen a runfunan zaɓe biyar na Kyambarawa da Sakajiki. Sun kuma bayyana cewa, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC za ta sanar da wata rana na kammala zaɓen da ba a kammala ba. Blueprint ta tattaro cewa jam'iyyar…
Read More
Koyar da ilimin jima’i a makarantu

Koyar da ilimin jima’i a makarantu

Yanzu dai ta tabbata, ma'aikatar ilimi ta ƙasa ta bai wa hukumar kula da shirya jadawalin koyarwa a makarantu ta NERDC ta cire duk wani abu da ya shafi ɓangaren koyar da ilimin jima'i a makarantun ƙasar nan. Matakin da ƙungiyoyin sa kai na al'umma su 54 suka haɗu wajen ƙalubalantar wannan mataki na Gwamnatin Tarayya, bisa hujjar cewa hakan zai iya dawo da hannun agogo baya, a yaƙin da ake yi da yaɗuwar cutar HIV mai karya garkuwar jiki. Masu goyon bayan wannan tsarin na ganin koyar da yara sanin ilimin jima'i zai taimaka musu wajen sanin mai ya…
Read More
Zuwa ga masu shirin aure (II)

Zuwa ga masu shirin aure (II)

Assalamu alaikum, kamar yadda muka faɗa a makon da ya gabata cewa, za mu cigaba daga inda muka tsaya. Abu na biyu da zan gaya muku shi ne yana da kyau ku fahimci cewa waɗannan abubuwa ba a samunsu haka kawai, wato ba sa samun mutum haka kawai, dole ne ku yi ƙoƙari wajen samar da su. Hanyar samar da su kuwa ita ce dukkan ma'auratan su so junansu. Wataƙila ku tambaya ta ya ya? Kamar yadda ake cewa ne, "ba a iya tabbatar da so da ƙauna ta hanyar ƙarfi da tursasawa", lalle haka ne don kuwa so kamar…
Read More
Kiɗa a ƙasar Hausa 

Kiɗa a ƙasar Hausa 

Daga HAFIZ ADAMU KOZA Gabatarwa: Ana zaton ɗan Adam ya fara amfani da kiɗa ne a lokacin da ya fara neman abinci ta hanyar farauta. Daga nan kuma da mutane suka fara yaƙe-yaƙe a tsakaninsu, sai sana’ar kiɗa ta ƙasaita (Ibrahim, 1983:ɓii). Masana adabi da al'adun Hausawa suna ganin busa ita ce abu na farko da Hausawa suka fara fahimta a matsayin wani nau’i na kiɗa (Salihu, 1985:1). Hausawa mutanen farko, sun fara amfani da wannan amo don yin sadarwa da kuma faɗakarwa. Sukan yi amfani da ƙaho wajen faɗakar da junansu bisa wani abu na murna ko na tsoro…
Read More