18
Aug
Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnatin Katsina ta bayyana cewa mutane 62 da aka yi garkuwa da su sun kuɓuta daga wurin da 'yan bindiga ke tsare da su bayan wani hari ta sama da sojoji suka kai a sansanin wani ƙasurgumin ɗan bindiga, Muhammadu Fulani, a ƙaramar hukumar Ɗanmusa ta jihar. Dr Nasir Mu’azu, kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar yau Litinin a Katsina. Sojojin saman Najeriya sun kai farmakin ne a yankin Jigawa-Sawai da ke kan iyaka da Jihar Zamfara. Kwamishinan ya ce mutane…
