ukarofi

12738 Posts
Farawa da aikatau ko bayanau a jumlolin wasu marubutan Hausa: Salon magana ko ɓata tsarin ginin jumlar Hausa?

Farawa da aikatau ko bayanau a jumlolin wasu marubutan Hausa: Salon magana ko ɓata tsarin ginin jumlar Hausa?

Daga MD ASNANIC 1.0 Gabatarwa Ilimin Ginin Jumla wanda masana suka laƙaba masa suna _Syntaɗ,_ ilimi ne da ya ƙunshi tsarin haɗa jumla da halayen da ke wakana a cikinta, tun daga tsarin yadda take ginuwa ta hanyar A+A+K (S+ɓ+O) —watau Aikau + Aikatau + Karɓau da kuma tsarin ɓangarorinta biyu: Yankin Suna da Yankin Aiki/Bayani. Haka zalika wannan fage na Ginin Jumla yana tattare da ƙunshiyar bayanai game da kafatanin rukunnan Nahawun Hausa.  Wannan rubutu ya yi nazari ne game da dacewar wasu jumloli da cikin ke littattafan wasu marubuta na Hausa a bisa tsarin Ginin Jumla ko kuma…
Read More
Babu uzuri a rubutun batsa – Sadiya Nasir

Babu uzuri a rubutun batsa – Sadiya Nasir

Daga ADAMU YUSUF INDABO a Kano Fitacciyar marubuciyar Hausa daga Jahar Bauchi da ke Arewacin Najeriya, wato Sadiya Nasir Dan, ta yi wannan furuci ne tare da jan kunnen marubuta musamman marubutan yanar gizo da su tsaftace alƙalumansu ga barin rubuta abubuwa marasa amfani, da dukkan abun da bai dace ba a tarbiyyar Musulunci da al'adar Malam Bahaushe. Marubuciya Sadiya Nasir Dan, ta yi wannan kira ne a yayin da suke tattaunawa da wakilinmu Adamu Yusuf Indabo. Ga dai yadda tattaunawar tasu ta kasance: MANHAJA: Da farko dai mene ne cikakken sunan marubuciyar, da kuma taƙaitaccen tarihin rayuwarki? SADIYA: Sunana…
Read More
Gwamnatin Katsina ta kafa kwamitin tantance asarar da aka yi a rikicin ƙauyukan Rijiyar Tsamiya da Minawa

Gwamnatin Katsina ta kafa kwamitin tantance asarar da aka yi a rikicin ƙauyukan Rijiyar Tsamiya da Minawa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Sakataren Gwamnatin Jiha (SGS), Barista Abdullahi Garba Faskari ne ya ƙaddamar da kwamitin a madadin gwamnatin jiha, inda ya nuna damuwar gwamnati kan lamarin da ya faru tare da nanata aniyar gwamnati wajen cigaba da wanzar da zaman lafiya da daidaito acikin al’umma. Kwamitin na ƙarƙashin jagorancin Alhaji Lawal Rufa’i Safana, mai mai wa gwamna shawara kan sashen kula da lamurran ƙananan hukumomi. Barista Faskari, ya bayyana wannan rikici a matsayin abin takaici, inda ya umarci kwamitin da ya gudanar da sahihin bincike domin gano ainihin adadin ɓarnar da aka yi da ɗaukar matakan kare…
Read More
Tsaro: An yi kira ga Tinubu ya ɗauki matakin gaggawa a Katsina

Tsaro: An yi kira ga Tinubu ya ɗauki matakin gaggawa a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Muƙaddashin gwamnan Jihar Katsina Malam Farouk Lawal Joɓe bayan hare haren ƴan bindiga yayi ƙamari a kudancin jihar. Yakamata shugaban ƙasa cikin gaggawa ya umurci manyan shugabanin Sojojin ƙasar da su murƙushe ƴan ta'adda a jihar tun kafin su murƙushe jihar Joɓe ya ce. Wannan kira ya biyo bayan wani muhimmin hari da yan bindigan suka kai a wani masallaci a unguwar Mantau inda suka kashi mutane 13. "Cikin biyayya muna roƙon shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya umurci jami'an tsaro da su kawo ƙarshen hare haren ta'addanci a jihar,"inji muƙaddashin gwamnan. Ya bayyana cewa…
Read More
Kwamishinan lafiyar Jihar Katsina ya kai ziyarar duba aikin gyaran babban asibitin Zango

Kwamishinan lafiyar Jihar Katsina ya kai ziyarar duba aikin gyaran babban asibitin Zango

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina A cigaba da ziyarar manyan asibitoci da gwamnatin jihar ke ginawa, kwamishinan lafiya Hon Musa Adamu Funtua ya kai ziyarar dubiya a asibitin Zango da ke ƙaramar hukumar zango. A yayin ziyarar, kwamishinan ya zagaya sassa daban-daban na asibitin da ake aiwatar da gyare-gyare, inda ya yaba da aikin dake gudana ya daceda ƙa’idar kwangila da ingancin kayan da aka tsara. Kwamishinan ya tattauna da kamfanin da ke jagorantar aikin, tare da jan hankalinsu kan muhimmancin kammala aikin akan lokaci. Hon Musa Adamu Funtua ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta sanya inganta harkar lafiya abu…
Read More
Gwamnatin Katsina ta ƙara tura jami’an tsaro domin daƙile hare-haren ‘yan bindiga a Malumfashi

Gwamnatin Katsina ta ƙara tura jami’an tsaro domin daƙile hare-haren ‘yan bindiga a Malumfashi

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Wannan mataki da gwamnati ta ɗauka ya biyo bayan wani gari da ƴan bindiga su ka kai a unguwar Manatau a ƙaramar hukumar Malumfashi inda suka kashe mutane 13. Sanarwa da kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro Dr Nasiru Mu'azu Ɗanmusa ya fitar,ya bayyana cewa yan bindigan sun kashe waɗannan mutane a wani masallaci lokacin da al'ummar Musulmin unguwar ke gudanar da sallar Asuba. Kan haka mutanen unguwar Manatau suka ɗauki fansa inda suma suka kashe da dama tare da ceto wasu mutanen da 'yan bindiga suka sato daga ƙauyen ruwan sanyi a cewar kwamishinan.…
Read More
Ɓarayin daji sun halaka mutane 13 a wani masallaci yayin sallar Asuba a Katsina

Ɓarayin daji sun halaka mutane 13 a wani masallaci yayin sallar Asuba a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta ƙara tura jami'an tsaro bayan wani mummunan hari da 'yan bindiga suka kai ƙauyen Unguwan Mantau a ƙaramar hukumar Malumfashi, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 13 a wani masallaci yayin sallar Asuba. Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kai harin ne a matsayin ramuwar gayya bayan da al’ummar ƙauyen suka yi musu kwanton-ɓauna kwanaki biyu da suka gabata, inda suka yi ajalin wasu daga cikinsu, tare da kuɓutar da waɗanda ɓarayin suka yi garkuwa da su, tare da ƙwace babura uku da bindigogi AK-47 guda biyu. Kwamishinan tsaron cikin gida,…
Read More
Lafiya ce ginshiƙin cigaban kowace mace – Amina Mohammed

Lafiya ce ginshiƙin cigaban kowace mace – Amina Mohammed

Da wuri na gano haɗarin sankarar mama na yanke shawarar cire nonona – Angelina Jolie Daga AISHA ASAS  Nono ba kawai abin ƙawa ba ne, tushen lafiya da rayuwa ne: Mai karatu barkan mu da sake ganin zagayowar sati lafiya, sannunku da jimirin bibiyar jaridar Blueprint Manhaja.  Kamar satin da ya gabata, mun sake zaƙulo maku darasi mai muhimmanci da muke hasashen za mu ƙaru da shi, wato za mu tattauna kan nonon mace, yadda yake, amfanin shi, cututtukan da ka iya samun mace ta ɓangaren sa, da ma ma'anar shi a ilimance. Amma kafin komai bari mu fara shimfiɗa…
Read More
Domin ku matan aure

Domin ku matan aure

Daga AISHA ASAS Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin kwalliya na jaridar al'umma Manhaja, sannunku da jimirin bibiyar mu. Kamar yadda muka yi alƙawarin kawo ma ku wasu daga ci gaban kayan da za su samar da ni'ima dawamamma ga mace, kuma kayan da ta ke da tabbacin tsafta da lafiyar su, kasancewar ita da kanta ne zata dinga haɗawa. Sai dai kafin nan, zan so in yi amfani da wannan dama in janyo hankalin mata kan illar shan maganin mata da ke bayar da ni'ima ta ɗai rana. Mata ku guji amfani da maganin mata mai bayar…
Read More
Uwa: Makarantar farko ga ‘ya’yanta

Uwa: Makarantar farko ga ‘ya’yanta

Daga AISHA ASAS Annabin rahma ya ce, “daɗin duniya na tattare da samun mace ta gari” domin da mace ta gari ce za ka samu kwanciyar hankali, za ka samu natsuwa tare da biyan buƙatun yau da kullum, ga uwa uba samun ‘ya’ya na gari. A yau darasinmu na iyali zai karkata ne kan maza, tun daga samari da ba su yi aure ba, zuwa magidanta da ke shirin ƙarin aure. Domin dai kuskuren daga wurin ku ne ya samo asali. Da yawa daga maza abin da suka fi kallo a matar da za su aura ba shi da tasiri…
Read More