15
Aug
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta ƙasa (NAFDAC) ta yi wani gagarumin gargaɗin cewa jabun magunguna, da abinci mara kyau, da kayayyakin gyaran fuska da ba a tantance ba, sun fi kashe rayuka a Nijeriya fiye da rikicin Boko Haram. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Dr. Martins Iluyomade, Daraktan Bincike da Tabbatar da Doka na NAFDAC, yayin ganawa da manema labarai a ranar Talata bayan wani gagarumin aikin tabbatar da ingantacin kayayyaki a kasuwar Legas. Tsawon kwanaki biyar ya kai ga kama sama da katon 10,000 na lalataccen tumatur ɗin gwangwani da…
