15
Aug
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Amurka ta amince ta sayar wa Nijeriya makamai wanda kuɗinsu ya kai Dala miliyan 346. Ma'aikatar Harkokin Tsaron Amurkar ta ce, makaman da za a sayar wa Nijeriyar sun haɗa da manyan boma-bomai da kuma rokoki. Ta ce, sayar da makaman zai ƙara inganta ɓangaren tsaron Nijeriya da kuma taimaka wa tsarin harkokin wajenta a yankin Kudu da Hamadar Saharar Afirka. "Cikin makaman har da wasu rokoki na zamani sama da 5,000," inji sanarwar Washington. Ta bayyana cewa, Nijeriya ta buƙaci sayen makaman 1,002 MK-82 na bai-ɗaya na bom ɗin 500 lb, 1,002 MɗU-650 Air…
