ukarofi

12738 Posts
Gwamnan Zamfara ya jajanta wa al’ummar Ƙaura Namoda bisa hare-haren ‘yan bindiga

Gwamnan Zamfara ya jajanta wa al’ummar Ƙaura Namoda bisa hare-haren ‘yan bindiga

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya ziyarci ƙauyukan Banga, Sakajiki da Kuryar Madaro da wasu ‘yan bindiga suka kai wa hari a ƙaramar hukumar Ƙaura Namoda da ke jihar. An kashe mutanen yankin da dama tare da jikkata wasu da dama inda maharan suka yi garkuwa da wasu yayin harin makonnin da suka gabata. Gwamnan wanda ya jagoranci wata tawaga mai ƙarfi da ta haɗa da mataimakin sa Mani Mumuni da sakataren gwamnatin jihar Abubakar Nakwada da sauran manyan jami’an gwamnati sun ziyarci al’ummomin ne a yau Laraba domin jajanta wa jama’a kan abin da…
Read More
Majalisar Dokokin Kano ta dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Rano

Majalisar Dokokin Kano ta dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Rano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Majalisar dokokin Jihar Kano ta dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Rano Alhaji Naziru Ya’u na tsawon watanni uku sakamakon rashin Iya tafiyar da mulki da karya dokokin aiki tare da umartar sa ya miƙa aiki ga mataimakin sa. Majalisar ta ɗauki wannan matakin ne yayin zaman da ta gudanar a wannan rana ta Laraba. Rahotanni sun nuna cewa an ɗauki matakin ne saboda zargin shugaban ƙaramar hukumar da sayar da tsohuwar kasuwar Rano. Sannan ana zarginsa da sayar da takin zamani ko karkatar da shi wanda gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya rabawa…
Read More
Majalisar dokokin Katsina ta amince da kafa hukumar samar da lantarki

Majalisar dokokin Katsina ta amince da kafa hukumar samar da lantarki

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Dokar ta samu amincewar majalisar ne bayan gabatar da rahoton kwamitin ayyukan cigaba da walwalar al’umma, ƙarƙashin jagorancin Hon. Mustapha Tukur Ruma, inda Shugaban Masu Rinjaye, Hon. Shamsuddeen Abubakar Dabai, ya karanta dokar na uku kuma na ƙarshe domin tabbatar da ita. Hon. Dabai, yace kafa hukumar zai inganta samar da hasken wutar lantarki cikin sauƙi ga al’umma ta hanyar amfani da ingantattun kayan aiki na zamani. Bayan amincewa da dokar, kakakin majalisar ya umarci akawun majalisa da ya tura cikakken kwafin ta ga gwamnan jihar domin sanya hannu. Haka kuma ɗan majalisa mai wakilan…
Read More
Ranar Matasa: Gwamna Inuwa ya ɗauki matasan GOSTEC aiki

Ranar Matasa: Gwamna Inuwa ya ɗauki matasan GOSTEC aiki

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe A lokacin bikin ranar matasa ta duniya da aka gudanar a Gombe, shugaban ƙaramar hukumar Gombe kuma Shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi na jihar (ALGON), Barista Sani Ahmad Haruna, ya yabawa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya bisa ɗaukar matasan da aka horar ƙarƙashin shirin Gombe State Traffic and Environmental Corps (GOSTEC) a matsayin cikakkun ma’aikata. Ya ce matakin ya nuna jajircewar gwamnati wajen tallafawa matasa domin rage zaman banza da inganta rayuwarsu. “Yanzu wasu daga cikinsu sun zama masu amfani ga kansu da al’umma, saɓanin yadda rayuwarsu ta kasance a baya,” in ji shi. Barista Sani…
Read More
Sanata Wadada na SDP ya koma APC, ya ce ba mai karawa da Tinubu a 2027

Sanata Wadada na SDP ya koma APC, ya ce ba mai karawa da Tinubu a 2027

Daga JOHN D. WADA, a Lafiya Sanata wanda ke wakiltar shiyar Nasarawa ta Gabas da ke Jihar Nasarawa a majalisar dattawa ta ƙasa, Sanata Aliyu Ahmed Wadada ya canja sheka daga tsohuwar jam'iyyar sa ta SDP zuwa ta APC mai ci a jihar sa ta Nasarawa bayan wani ganawa na musamman da yayi da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban ƙasar da ke birnin tarayya Abuja a yammacin jiya Talata. Ya bayyana kan sa a matsayin cikakken ɗan sabuwar jam'iyyar APC ɗin duk da bai canja shekar a hukumance ko ba. A cewar sanata Aliyu Ahmed Wadada da…
Read More
Sabbin marubuta kan ji ba daɗi kan wariyar da ake nuna masu – Indian Girl 

Sabbin marubuta kan ji ba daɗi kan wariyar da ake nuna masu – Indian Girl 

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Idan ka ji an ce ga wata Indian Girl, mai yiwuwa tunaninka ya ta fi zuwa ƙasar Indiya, ko kuma ka fara tunanin ganin wata yarinya ýar ƙasar Indiya. To, wannan Indian Girl ɗin ta marubuta ce, kuma ýar Nijeriya daga Jihar Kano. Tana daga cikin matasan marubutan onlayin masu baje ilimi da basira a zaurukan marubuta na WhatsApp da Facebook, inda take fitar da labarai da suka shafi soyayya da zamantakewa. A zantawarta da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, Indian Girl, wacce asalin sunanta shi ne Zainab Muhammad ta bayyana yadda aka yi ta…
Read More
Magoya bayan Ɗankwambo na akwatin zaɓe sun sauya sheka zuwa APC a Gombe

Magoya bayan Ɗankwambo na akwatin zaɓe sun sauya sheka zuwa APC a Gombe

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe A wani muhimmin sauyin siyasa da ya auku a Jihar Gombe, magoya bayan akwatin rumfar zaɓen tsohon Gwamnan Gombe, Dakta Ibrahim Hassan Ɗankwambo, sun sauya sheka daga jam’iyyar su ta PDP zuwa jam'iyyar APC. Shugaban ƙungiyar shugabanin ƙananan hukumomi na Gombe wanda shi ne shugaban ƙaramar hukumar Gombe Barista Sani Ahmad Haruna , shi ne ya karɓe su a wani biki da ya samu halartar manyan jiga-jigan siyasa da magoya baya daga tushe. Wannan sauyin sheka, wanda hadimin gwamna na musamman kan harkokin GOSTEC, D.J. Mai Taya, ya jagoranta, ya haɗa da ɗimbin tsofaffin…
Read More
2027: ADC ta ƙaddamar da kwamitocin gudanarwar na Jihar Nasarawa

2027: ADC ta ƙaddamar da kwamitocin gudanarwar na Jihar Nasarawa

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Sabuwar Jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) ta ƙasa ta bayyana sunayen sabbin shugabannin ta na reshin Jihar Nasarawa tare da ƙaddamar da kwamitocin gudanarwar cewa sun haɗa da tsohon mataimakin gwamnan jihar ta Nasarawa, John Mike Abdul a matsayin shugaban kwamitin ɗin kuma kodineta haɗe da shugabam jam'iyyar a jihar duk shi kaɗai. Sauran membobin kwamitin sun haɗa da: Sen. Suleiman Adokwe- MambaHon Adamu Oyanki - MambaDr. Umar Musa Galadima - MambaBarr. John Matthew- MambaHon. Musa Bako Karshi - MambaPrince Yamusa Chindo- Mamba Sauran sune: Comr. Idris Ojoko Jibrin - MambaHon. Aminu Nagogo -…
Read More
Wararrun ‘yan majalisar dokokin Zamfara sun yi Allah wadai da gwamnatin jihar kan matsalar tsaro

Wararrun ‘yan majalisar dokokin Zamfara sun yi Allah wadai da gwamnatin jihar kan matsalar tsaro

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Wararrun ƴan majalisar dokokin Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Rt Hon Bashar Aliyu Gummi ta sake yin Allah wadai da halin ko in kula da Gwamna Dauda Lawal Dare ke yi kan matsalar tsaro a jihar. 'Yan Majalisar sunyi kira ga gwamnatin tarayya da ta haɗa kai da jami’an tsaro a Zamfara domin ceto rayukan al’ummar jihar da dukiyoyinsu kamar yadda yake ƙunshe a kundin tsarin mulki Kashi na biyu. A zaman su na yau, ‘yan majalisar sun yi nasu bitar yadda ‘yan bindiga suka lalata jihar ta hanyar kai hare-hare a wasu al’ummomi da dama…
Read More
Fursunoni 19 sun tsere daga gidan yarin Keffi a Nasarawa

Fursunoni 19 sun tsere daga gidan yarin Keffi a Nasarawa

Daga JOHN D WADA a Lafiya Kimanin 'yan gidan gyara hali 16 ne suka tsere daga gidan gyaran hali da ke garin Keffi hedikwatar ƙaramar hukumar Keffi a Jihar Nasarawa a yau Talata 12 ga watan Agustan shekarar 2025 da ake ciki. Lamarin yayi sanadiyar samun munanan raunuka da wasu jami'ai dake kula da gidan yarin su biyu suka samu. Tuni mahukuntar gidan yarin suka tabbatar da aukuwar lamarin inda suka bayyana cewa jami'ai biyun da suka samu munanan raunin a yanzu haka suna samun kulawar likitoti a wani asibitin gwamnati. Mai magana da yawun gidan yarin, Abubakar Umar ya…
Read More