12
Aug
Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Hukumar sadarwa ta Najeriya NCC, ta horar da mata 100 sana’o’in fasahar zamani domin ƙarfafa musu gwiwa su zama masu dogaro da kai. Shugabar Sashen fasahar dijital na hukumar, Hajiya Hauwa Wakil a jawabinta a wajen ƙaddamar da horon da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Gusau a ranar Talata, ta yi kira ga mata da su ba da fifiko kan sana’o’in kasuwanci na zamani domin ci gaban su. Ta ce, an zaɓo mahalarta taron ne daga dukkan ƙananan hukumomi 14 na Zamfara domin su ci gajiyar shirin. A cewarta, hukumar a shirye take…
