11
Aug
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Asusun kula da manyan makarantu na ƙasa (TETFUND) ya saki sama da Naira biliyan 100 ga manyan makarantun ƙasar nan a matsayin tallafin inganta ilimin likitanci da unguwar zoma da makamantansu domin ƙara yawan ma’aikatan kiwon lafiya a ƙasar nan. Shugaban asusun na TETFUND, Rt. Hon Aminu Bello Masari, ya bayyana haka a wata tattaunawa da yayi da manema labarai a Katsina. Ya ce yin hakan manufa ce ta shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ganin an shawo kan matsalar ƙarancin ma’aikata a fannin kiwon lafiya, duba da yadda likitoci da malaman jinya da sauran…
