ukarofi

12738 Posts
An gudanar da taron wayar da kan matasa kan mahimmancin sana’o’i a Katsina

An gudanar da taron wayar da kan matasa kan mahimmancin sana’o’i a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gidauniyar Sauttus Sunnah ta shirya taron na kwanaki biyu da haɗin guiwa da Gwamnatin Jihar Katsina. A jawabin sa wajen taron Shugaban ƙungiyar JIBWIS ta Jihar katsina Sheik Yakubu Musa HassanYa bayyana cewawannan gidauniya ta Sauttus Sunnah ta shirya wannan taro ne mussaman ga matasan mu masu tasowa yadda za'a ɗaura su bisa hanyoyin koyon sana'o'i da kuma gina rayuwar su bisa ga turba ta halal. Ya sanar da cewa nan gaba wannan gidauniya za ta faɗaɗa irin wannan taron bita zuwa wasu jihohi ƙasar. Sheikh Yakubu Musa Hassan ya yaba wa gwamnatin Jihar Katsina…
Read More
Yaushe Mohbad zai ‘mutu’ ne?

Yaushe Mohbad zai ‘mutu’ ne?

Daga AISHA ASAS  *Na gane wasan kwaikwayon da CP Uche ke yi – Iyabo Ojo * Zan bayyana batutuwan DNA da Iyabo ta tattauna a sirrance - VDM  *Iyabo Ojo ta rungumi wanda ya kamata ta tambaya – ’Yar uwar Mohbad *Portable ga VDM: Ka yi watsi da tafarkin adalci ga Mohbad Sanannen abu ne, mutum kan shahara ne akan abinda yake yi da ya samu karɓuwa ga jama'a, sai su kama sunansa a baki, su sanya soyayyarsa a zuciya, wanda ke kai a wasu lokuta ya rasa walwalarsa sakamakon kowa ya san shi kuma ana muradin ganin shi. Wannan…
Read More
‘Dilwale Dulhania Le Jayenge’ da ‘Kaakha Kaakha’: Fina-finan da suka kafa tarihi a zukatan masu son soyayya

‘Dilwale Dulhania Le Jayenge’ da ‘Kaakha Kaakha’: Fina-finan da suka kafa tarihi a zukatan masu son soyayya

Daga AISHA ASAS  'Sun tabbatar da cewa soyayya ba kawai da baki ake furtawa ba, sai da jajircewa da sadaukarwa' A duk faɗin duniya, musamman a nahiyar Asiya, fina-finai sun daɗe suna taka rawar gani wajen bayyana labarai na zuciya, al’adu, ƙauna da gwagwarmaya. A sinimar Indiya da ta Tamil, fina-finai biyu sun fi fice wajen tabbatar da irin wannan tasiri, wato 'Dilwale Dulhania Le Jayenge' da 'Kaakha Kaakha'. Waɗannan fina-finai sun sauya fuskar sinima, sun gina wani sabon fahimta game da ƙauna da rayuwa, kuma har yau suna zaune a zukatan masu kallo, shekaru da dama bayan fitarsu. Dilwale…
Read More
Zuwa ga masu shirin aure (I)

Zuwa ga masu shirin aure (I)

Assalam alaikum. Da fatan kowa ya yi sallah lafiya? Allah ya albarkaci jaridar Blueprint. A yau zan yi wasiƙa ne a kan zaɓin ma'aurata, domin shi ne babban abin da ke ci wa kowa tuwo a ƙwarya a halin yanzu. Wanda kuma hakan ke jawo yawan mace-macen aure, domin ana auren ne kawai barkatai ba tare da sanin wa ya kamata a aura ba. Babban hadafin da ya ke sanya mu zaɓar wanda zamu rayuwa da shi ko wacce zamu rayu da ita a matsayin rayuwar aure shi ne samun nutsuwar rayuwa, shi kuwa samun nutsuwar ruhi da abokiyar zama…
Read More
Sake zaɓen Tinubu zai lalata makomar Nijeriya — El-Rufai 

Sake zaɓen Tinubu zai lalata makomar Nijeriya — El-Rufai 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce idan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC suka sake lashe zaɓe a 2027, hakan zai lalata makomar ’yan Nijeriya. El-Rufai, ya faɗi haka ne a Jihar Sakkwato yayin wani gangamin wayar da kan jama’a da jam’iyyar adawa ta ADC, ta shirya. Ya ce yana goyon bayan wannan haɗaka, kuma zai taimaka wajen ganin ’yan Nijeriya sun sauke APC daga kan mulki. “Idan muka bar wannan gwamnati ta ci gaba da mulki zuwa karo na biyu, ragowar abin da ya rage na haɗin kai da amincewa…
Read More
Idan aka zaɓe ni zan yi wa’adi ɗaya na shekaru huɗu na sauka daga mulki – Obi 

Idan aka zaɓe ni zan yi wa’adi ɗaya na shekaru huɗu na sauka daga mulki – Obi 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon ɗan takarar shugabancin Nijeriya a jam'iyyar Labour, Peter Obi ya ce idan ya samu nasarar zama shugaban ƙasar, wa'adi ɗaya na shekara huɗu kawai zai yi kamar yadda ya yi alƙawari. Obi ya bayyana haka ne a shafinsa na X, inda ya ce ko tsohon shugaban Amurka, Abraham Lincoln wa'adi ɗaya ya yi na shekara huɗu, "sannan John F. Kennedy bai ma ƙarasa wa'adi ɗaya ba, amma ana cigaba da tunawa da su a matsayin shugabanni masu adalci." Ya ce ko a Afirka, Nelson Mandela ya zama abin koyi a duniya wajen shugabanci…
Read More
2027: APC a Kano ta bayyana goyon baya ga Tinubu 

2027: APC a Kano ta bayyana goyon baya ga Tinubu 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Masu ruwa da tsaki na Jam'iyyar APC a Jihar Kano sun bayyana goyon baya ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin ya sake tsayawa takara a zaɓe na biyu a 2027, tare da tabbatar da biyayyarsu ga jagoran jam’iyyar a Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje. Sun bayyana goyon bayan ne a taron masu ruwa da tsaki na musamman da ya gudana a ranar Talata a gidan Ganduje da ke Kano. Taron ya mayar da hankali ne kan haɗin kan jam’iyya, shirin zabe mai zuwa, da kuma ci gaban da gwamnatin Tinubu ke samu a…
Read More
Sauya halayyar ’yan daba muka sa a gaba – Shugaban ƙungiyar Jos Peace Vanguard

Sauya halayyar ’yan daba muka sa a gaba – Shugaban ƙungiyar Jos Peace Vanguard

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Garin Jos, babban birnin Jihar Filato na ɗaya daga cikin manyan biranen arewacin ƙasar nan da suke fama da matsalar taɓarɓarewar tsaro, da ya shafi yadda ƙungiyoyin matasa 'yan daba suke ɗaukar makamai suna shiga anguwanni suna sare-saren kan-mai-uwa-da-wabi da ƙwacen wayoyi. Yawaitar wannan masifa ce ta zaburar da mutane irin su MALAM NURA ALHASSAN da masu ra'ayi irin nasa suka tashi tsaye don ganin yaran da suke wannan aika-aika sun dawo kan hanya, da samar da tsaro a cikin al'umma. Wanne ƙalubale irin wannan aikin sa-kai ke fuskanta? Wacce nasara aka samu? Kuma wanne tallafi…
Read More
Yadda za a kawo ƙarshen cin zarafin mata

Yadda za a kawo ƙarshen cin zarafin mata

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Gwagwarmayar yaƙi da cin zarafin mata ta kwanaki 16 da aka saba gudanarwa duk shekara ta zo ta wuce, amma ba za a iya daina magana kan cin zarafi, cin zali da tauye haƙƙin da ake yi wa 'ya'ya mata ba. Har sai ranar da aka wayi gari aka ce yau mata suna rayuwa cikin 'yanci da kwanciyar hankali tare da maza abokan rayuwarsu, babu fargaba ko tsoron wani abu, ba a nan Nijeriya kaɗai ba har ma da duniya bakiɗaya. ƙungiyoyin mata daban-daban a ƙasar nan sun shiga cikin wannan gangami na kwanaki 16 da…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya bi sahun al’ummomi wajen sauraren buƙatun al’umma na kasafin kuɗin 2026

Gwamna Raɗɗa ya bi sahun al’ummomi wajen sauraren buƙatun al’umma na kasafin kuɗin 2026

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina An gudanar da sauraron jama'a kan buƙatar su da zai taimaka wa gwamnatin jihar wajen tsara kasafin kuɗin 2026. Gwamna Dikko Raɗɗa ne ya ƙirƙiro da wannan tsari kuma ya umurci zaɓaɓɓun wakilai da masu riƙe da muƙamin siyasa da suje mazaɓun su jagoranci sauraron al'ummar su. Malam Dikko Raɗɗa ya gana da al'ummar mazaɓar sa ta Raɗɗa, da ke ƙaramar hukumar Charanchi, a wajen taron shirin tattara muhimman buƙatun al'umma da za a sanya a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026. Taron wanda Gwamnan ya halarta ta yanar gizo na matsayin wani mataki na bin…
Read More