ukarofi

12738 Posts
 Ko Amorim zai iya kai Manchester United tudun-mun-tsira a kakar wasan bana?

 Ko Amorim zai iya kai Manchester United tudun-mun-tsira a kakar wasan bana?

Manchester United ta kwashe fiye da shekara 10 ba ta yi wani kataɓus ba, idan aka kwatanta da yadda ta saba a baya, musamman lokacin da Sir Alex Ferguson yake horas da 'yan wasan ƙungiyar. Tun bayan da Sir Alex ya yi ritaya a 2013 United ke neman kocin da ya dace da ita inda suka gwada irin su Jose Mourinho da Erik Ten Haag da David Moyes da Ralph Rangnick da sauran su, amma kowanensu ya gaza dawo da Manchester United kan ganiyarta duk da cewa wasu daga cikinsu sun lashe kofuna. A watan Nuwamban 2024 ne Manchester United…
Read More
NDLEA ta kama hodar iblis da tramadol a filin jirgin saman Legas

NDLEA ta kama hodar iblis da tramadol a filin jirgin saman Legas

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), sun kama wasu kayayyaki na hodar iblis da tramadol mai nauyin kilogiram 225 da aka ɓoye a cikin madubin mota guda 71 domin safarar zuwa birnin Libreɓille na ƙasar Gabon. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan yaɗa labarai da bayar da shawarwari na NDLEA, Femi Babafemi ya fitar a Abuja ranar Lahadi. Babafemi ya bayyana cewa, an yi jigilar magungunan ne ta wurin da ake fitarwa a filin jirgin sama na Murtala Muhammed International Airport, MMIA, Ikeja Legas. Ya ce, an riga…
Read More
NDLEA ta kama masu kai saƙo suna raba miyagun ƙwayoyi a Abuja

NDLEA ta kama masu kai saƙo suna raba miyagun ƙwayoyi a Abuja

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), ta cafke wasu masu kai saƙo guda uku da ake zargin su na raba haramtattun kayayyaki a Babban Birnin Tarayya, Abuja. Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja. Babafemi ya ce, jami’an hukumar NDLEA sun gudanar da bincike a ƙarƙashin jagorancin sirri a yankunan Gwarimpa, Jahi, da Galadimawa a Babban Birnin Tarayya Abuja a ranar Laraba 30 ga watan Yuli. Ya bayyana sunayen waɗanda ake zargin Sabo Sule mai shekaru 24; Samuel…
Read More
Zulum ya ce babu fargabar samun ambaliya daga madatsar ruwa ta Alau

Zulum ya ce babu fargabar samun ambaliya daga madatsar ruwa ta Alau

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum ya kawar da fargabar ƙaruwar ruwan da ake fama da shi a madatsar ruwa ta Alau, yana mai cewa babu wani abin fargaba. Zulum ya ba da wannan tabbacin ne a ranar Asabar bayan ya duba aikin sake gina madatsar ruwa da ke kusa da Maiduguri. Ya amince da fargabar da jama’ar Maiduguri ke fama da shi, amma ya ce gwamnati ba ta hango wani mummunan ambaliya daga madatsar ruwan ba. Zulum ya bayyana cewa a baya-bayan nan wani ɗan kwangila ya nuna damuwarsa kan ƙaruwar ruwa, wanda hakan ya sa…
Read More
Akasarin ‘yan siyasar Nijeriya ba su da tarbiyya – Sarki Sanusi II

Akasarin ‘yan siyasar Nijeriya ba su da tarbiyya – Sarki Sanusi II

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II ya zargi 'yan siyasar Nijeriya da aikata cin hanci da rashawa saboda "rashin tarbiyya tun daga tasowarsu". Da aka tambayi sarkin ta cikin shirin Politics Today na kafar talabijin ta Channels TV a yammacin yau dangane da cin hanci da rashawa, Sanusi ya ce da yawa ba a koya musu yin gaskiya da riƙon amana ba. "Akasarin mutanen da ke riƙe da ofisoshin gwamnati ba su da wannan tarbiyyar, mafi yawa na shiga gwamnati ne bisa dalilai marasa kyau," in ji shi. "Ina ganin an rusa kusan…
Read More
Hatsarin Mota: Yadda hanyar Lambata ke laƙume rayuka a Neja

Hatsarin Mota: Yadda hanyar Lambata ke laƙume rayuka a Neja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Mutum 22 sun gamu da ajalinsu, yayin da wasu 20 suka jikkata, bayan wata babbar mota da ta yi lodin mutane da dabbobi ta yi hatsari a kan hanyar Lambata zuwa Lapai da ke Jihar Neja. Hatsarin ya auku ne da safiyar ranar Litinin. Motar ta taso daga Kano zuwa Legas ne lokacin da hatarin ya auku da misalin ƙarfe 3 na safe, sakamakon gudun wuce ƙima. Hukumar Kiyaye Haɗura ta ƙasa (FRSC), ta ce dukkanin fasinjojin da ke cikin motar maza ne. An kai gawarwakin Babban Asibitin Suleja, yayin da aka garzaya da…
Read More
Kano: Za mu shirya wa mazauna gidan gyaran hali da gidan yaran Nassarawa wa’azi – Hukumar Shari’a

Kano: Za mu shirya wa mazauna gidan gyaran hali da gidan yaran Nassarawa wa’azi – Hukumar Shari’a

Daga RABIU SANUSI a Kano Hukumar Shari'a ta Jihar Kano za ta shirya wa mazauna gidan ajiya da gyaran hali na Janguza da gidan yara na Nassarawa, Wa'azi, domin faɗakar da su akan gyaran tarbiyya. Shugaban hukumar Shari'ar a nan Kano Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ne ya bayyana hakan a lokacin da hukumar ta ziyarce gidan gyaran hali na Janguza, a Larabar nan, domin ƙara ƙulla alaƙar aiki, a wani ɓangare na cika umarnin gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, wajen ragewa mazauna gidajen wani raɗaɗi. Hukumar Shari'ar ta kuma ziyarci gidan gyaran hali na Goron Dutse, da gidan kula…
Read More
Bai kamata a riƙa bai wa ɓarayi muƙamin gwamnati ba — Sarki Sanusi

Bai kamata a riƙa bai wa ɓarayi muƙamin gwamnati ba — Sarki Sanusi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Malam Muhammadu Sanusi II, ya ce, bai dace a riƙa bai wa mutanen da suka wawure dukiyar ƙasa manyan muƙaman gwamnati kamar ministoci ba. A cikin shirin ‘Politics Today’ na gidan talabijin na Channels, Sanusi II, ya bayyana damuwarsa game da yadda ’yan Nijeriya ke son dukiya fiye da gaskiya da tarbiyya. Ya ce, al’umma na girmama masu kuɗi, ko da kuwa an san kuɗin na haram ne. “ƙasar da ke bai wa mutanen da aka san sun wawure dukiyar ƙasa muƙamin minista, za ta ci gaba da tafiya a…
Read More
’Yan sandan Kaduna sun kama boma-boman da aka ɓoye cikin kayan gwangwan daga Borno

’Yan sandan Kaduna sun kama boma-boman da aka ɓoye cikin kayan gwangwan daga Borno

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD a Kaduna Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta kama wasu bama-bamai da ba su fashe ba da wasu tarin makamai da aka shigar da su jihar cikin kayan gwangwan daga jihar Borno. Lamarin dai ya jefa fargaba a zukatan mutane kan yadda kayayyaki ke yawo babu bincike daga jihohin da ke fama da rikici. Kakakin rundunar a jihar, DSP Mansir Hassan ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce an kama kayan ne ranar Asabar bayan wasu bayanan sirri da rundunar ta samu. Ya ce, an samu kayan ne a cikin wani kamfanin da ke hada-hadar…
Read More
‘Yan sanda sun tsare Sowore bisa zargin tunzura al’umma

‘Yan sanda sun tsare Sowore bisa zargin tunzura al’umma

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta tsare ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC a zaɓen 2023 kuma fitaccen ɗan rajin kare haƙƙin bil’adama, Omoyele Sowore bisa zarginsa da yin ayyukan bogi da kuma tunzura jama’a. An rawaito cewa, a ranar Larabar da ta gabata ne Sashen sanya ido na 'yan sanda na ƙasa (IGP) ya gayyaci Sowore, wanda ke jagorantar ƙungiyoyin ReɓolutionNow da Take-Back zuwa hedikwatar rundunar da ke Abuja domin amsa tambayoyi. Ya amsa gayyatar da aka yi masa, ya isa harabar da rana tare da rakiyar wasu magoya bayansa. A cewar wata sanarwa da…
Read More