09
Aug
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta ƙasa (NAFDAC), a ranar Asabar ɗin da ta gabata, ta kama haramtattun kayayyaki, kayayyakin da suka lalace da kuma waɗanda ba su da rajista da kuɗin su suka haura Naira Biliyan 1.5 a Legas. Rundunar ‘yan sandan ta NAFDAC ce ta gudanar da aikin a sashen kayan shafawa na kasuwar baje kolin kasuwanci. Hakazalika, rundunar ta samu nasarar cafke wata tirela ɗauke da jabun kayayyaki. Dokta Martins Iluyomade, Daraktan Bincike da tabbatarwa, shi ne ya jagoranci tawagar tare da yi wa manema labarai jawabi bayan atisayen. Ya ce,…
