Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
An rantsar da sabbin zaɓaɓɓun shugabannin cibiyar ciniki, masana’antu, ma’adinai da aikin gona na jihar Kano da aka fi sani da KACCIMA a ɗakin taro na harabar filin bajekoli na Aminu ɗantata da ke kan titin gidan Zoo.
Taron ya samu halartar mutane da dama ciki har da Kwamishinan Ciniki da Masana’antu na jihar Kano, Hon. Wada Sagagi.
Da yake jawabi bayan rantsar da su, sabon zaɓaɓɓen Shugaban Cibiyar Ciniki da Masana’antu, Ma’adinai da Aikin Gona na jihar Kano, Ambasada Usman Hassan Darma, ya bayyana cewa, zaɓen da aka yi masa ba tare da hamayya ba, ya nuna haɗin kai da fahimtar juna da nasara a tsakaninsu.
Ya yi nuni da cewa wannan nasara ba tasu ba ce su kaɗai, domin alamar amincewar mambobin cibiyar ce gare shi da sabuwar tafiya da za a yi ta inganta harkokin ciniki da masana’antu a jihar Kano da Arewa da ma ƙasa baki ɗaya.
Ambasada Usman Hassan Darma ya gode wa kwamitin da suka gudanar da zaɓen bisa yin zaɓe cikin gaskiya da adalci. Ya jinjina wa tsofaffin mambobin kwamitin gudanarwa na cibiyar a kan jajicewa da riƙon amana da kuma gode wa tsoffin shugabannin cibiyar a kan irin kyawawan tubali da suka aza da suke shirin cigaba da bunƙasa shi.
Ya ce su ma ma’aikatan Sakatariyar Cibiyar tun daga Darakta Janar har zuwa masu gadi, suna daga cikin ginshiƙai da ke riƙe da cibiyar.
Ya tabbatar da cikakken goyon baya da haɗin kai daga wannan sabon shugabancin.
Ya gode wa gwamnatin jihar Kano bisa goyon baya da take ba su, tare da cewa za su buɗe ƙofa don haɗin gwiwa tsakanin hukumomi da ‘yan kasuwa don bunƙasa tattalin arziƙin Kano da ƙara jawo saka hannun jari cikin al’umma.
Ya tabbatar wa daraktocin cibiyar za su cigaba da jagorantar cibiyar, tare da yin aiki tare domin tsara sabuwar Cibiyar mai cike da haɗin kai ta ƙirƙiro ingantattun manufofi.
Shugaban Cibiyar, Ambasada Usman Hassan Darma ya ce, dukkan mambobin Cibiyar wannan shugabanci nasu ne. Za su farfaɗo da ayyuka da ƙarfafa haɗin kai da mayar da Cibiyar matsayin da ya dace da ita a ƙasa baki ɗaya.
Shi ma a nasa jawabin, tsohon shugaban riko na Cibiyar, Alhaji Garba Imam ya bayyana irin matsalolin da suka zo suka sami Cibiyar a ciki da irin matakai da suka ɗauka na kawo gyara da sama mata kuɗin shiga da irin ayyuka da suka gudanar.
Ya ce a yanzu haka suna da ɗimbin kuɗaɗe da kadarori, tare da yin alƙawarin cigaba da bai wa sabon zubin sabbin shugabannin Cibiyar goyon baya domin kai wa ga nasara.
Cikin shugabannin ƙungiyar da aka rantsar sun haɗa da; Alhaji Abdulrahman Sabitu Muhammad a matsayin mataimakin Shugaba I, Alhaji Umar Haruna Isma’il mataimakin Shugaba II, Nura Habib mataimakin Shugaba na kasuwanci, Hajiya Samira Abubakar mataimakiiyar Shugaba mai kula da hulɗa da jama’a, Aliyu Mustapha mataimakin Shugaba mai kula da kadarori da sauran muƙamai na matakai daban-daban.
