ukarofi

12738 Posts
Al’ummar yankin Funtua sun buƙaci gwamnatin Katsina ta inganta tsaro

Al’ummar yankin Funtua sun buƙaci gwamnatin Katsina ta inganta tsaro

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina An yi kira da gwamnatin Jihar Katsina da ta fito da wasu dabaru da sabbin tsare-tsare na inganta tsaro a yankin. Wannan kira na ɗaya daga cikin matsaya da mazaɓar Nassarawa a ƙaramar Funtua a gaɓar wajen taron sauraren buƙace buƙace na al'umma da za a sanya a kasafin kuɗi na 2025. Wasu daga cikin buƙatar al'ummar mazaɓar suke buƙatar sun haɗa da samar da aikin yi ga matasa da tallafawa mata masu ƙananan sana'o'i. Shugaban ƙungiyar haɗin kan Funtua kwamred Mannir Suleiman ɗan asalin mazaɓar ya yabawa gwamna Dikko Raɗɗa da ya ƙirƙiro da…
Read More
Yan sandan Katsina sun kama mutane 302 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban

Yan sandan Katsina sun kama mutane 302 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban

' Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya faɗi haka ga manema labarai kan nasarorin da rundunar ta ta samu a watan da ya gabata. Ya bayyana cewa a cikin su, mutane 14 aka kama da laifin fashi da makami,sai mutane 22 da zargin aikata kisan kai. Haka kuma yan sandan sun Kama mutane 25 da ake zargi da aikata fyaɗe,mutane 20 kuma da zargin lalata kayan gwamnati. Akwai mutane 26 da ake zargi da dillancin miyagun ƙwayoyi, sauran mutane 194 da aka kama da aikata laifuka…
Read More
Awaza 2024/2034: UAE ta bayyana ƙudurinta na zuba jari a fannin makamashi, sufuri da ababen more rayuwa

Awaza 2024/2034: UAE ta bayyana ƙudurinta na zuba jari a fannin makamashi, sufuri da ababen more rayuwa

A ranar Litinin, 5 ga watan Agusta, aka buɗe babban taron Majalisar ɗinkin Duniya karo na uku da ke nazari kan ƙalubalen ƙasashe 32 da ba su da iyakokin ruwa (LLDCs), a birnin Awaza na ƙasar Turkmenistan. Taron ya haɗa shugabannin ƙasa, ministoci, da wakilan manyan hukumomin duniya domin tsara hanyoyin da za su fitar da waɗannan ƙasashe daga ƙangin matsalolin su na cinikayya da ci gaba. Babban manufar wannan taro mai taken “Inganta Ci gaba Ta Hanyar Haɗin Gwiwa”, shi ne aiwatar da Shirin Awaza na Shekaru Goma (2024–2034) wanda aka amince da shi a watan Disamban 2024. Wannan…
Read More
Fitattacen ɗan kasuwar Pakistan ya shiga hannun doka kan barazanar fyaɗe da kisa ga ma’aikaciyar jirgi

Fitattacen ɗan kasuwar Pakistan ya shiga hannun doka kan barazanar fyaɗe da kisa ga ma’aikaciyar jirgi

Wata kotun birnin London ta yanke hukuncin ɗauri na tsawon watanni 15 ga Salman Iftikhar, wani attajiri ɗan asalin Pakistan, sakamakon mummunan halin da ya nuna yayin tafiya a jirgin saman kamfanin Virgin Atlantic daga London zuwa Lahore a shekarar 2023. An bayyana cewa Iftikhar ya yi barazana ga ma'aikaciyar jirgi da cewa za a yi mata fyade ta kai ga mutuwa tare da kona ta da wuta, dukkansu a gaban fasinjoji da iyalansa, ciki har da ‘ya’yansa uku. Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya fara ne bayan da aka ga Iftikhar yana zuba ƙanƙara da hannunsa daga mashayar cikin…
Read More
Yadda ‘hayaƙin janareta’ ya kashe mutum huɗu ’yan gida ɗaya a Borno

Yadda ‘hayaƙin janareta’ ya kashe mutum huɗu ’yan gida ɗaya a Borno

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Mazauna ƙauyen Chatta da ke ƙaramar Hukumar Hawul a jihar Borno sun faɗa alhini sakamakon rasuwar wasu mutum huɗu ’yan gida ɗaya. Ba a dai tabbatar da ainihin musabbabin rasuwarsu ba, amma mazauna yankin da lamarin ya faru sun ce suna zargin hayaƙin injin samar da lantarki na janareta ne ya yi ajalinsu. Majiyoyin da ke ƙauyen sun shaida wa rundunar ’yan sandan jihar cewa waɗanda suka mutun sun haɗa da Yakubu Samanja, matarsa Esther Yakubu, da ’ya’yansu biyu, Amos Yakubu da Maryamu Yakubu. Wani ɗan uwar mamatan mai suna Ibrahim Samanja, ya ce…
Read More
Nijeriya da Indiya za su haɗa kai don yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi

Nijeriya da Indiya za su haɗa kai don yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Hukumar hana sha da fatauncin miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya, NDLEA da takwararta ta Indiya, sun amince da ƙara haɗa kai wajen yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi tsakanin ƙasashen biyu. Blueprint Manhaja ta rawaito cewa hakan na cikin batutuwan da shugabannin hukumomin, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya da Mista Anurag Garg su ka amince da su a lokacin wata tattaunawa da suka yi ta intanet. Sun ce za su fi mayar da hankali ne kan yadda ake shigar da haramtattun magunguna kamar tramadol da magunguna masu hodar ibilis cikin Nijeriya daga Indiya. Buba Marwa…
Read More
Gwamnatin Tarayya za ta ɗauki ma’aikatan lafiya 70,000 kafin shekarar 2029

Gwamnatin Tarayya za ta ɗauki ma’aikatan lafiya 70,000 kafin shekarar 2029

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirin ɗaukar ma’aikatan lafiya guda 70,000 nan da shekarar 2029 domin ƙarfafa tsarin kula da lafiyar al’umma da kuma sauƙaƙa samun lafiya a yankunan da ba su da isassun asibitoci. Daraktan Hukumar Raya Asibitocin Sha-ka-tafi na ƙasa (NPHCDA), Dr. Muyi Aina, ne ya bayyana hakan a wani taro na Nahiyar Afrika da aka gudanar a Abuja, wanda cibiyar Africa CDC da UNICEF suka shirya don tattauna batutuwan da suka shafi lafiyar al’umma da tsare-tsaren samar da ma’aikatan lafiya a matakin ƙasa da ƙasa. Dr. Aina ya bayyana cewa an tsara…
Read More
Mahukunta sun fatattaki mabarata 273, sun kama ababen hawa 670 a cikin watanni huɗu a Abuja

Mahukunta sun fatattaki mabarata 273, sun kama ababen hawa 670 a cikin watanni huɗu a Abuja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Mahukunta a Abuja Babban Birnin Tarayya ta fatattaki mabarata da ke galantoyi a sassa daban-daban har 273 sannan sun kama ababen hawa 670 domin daƙile muggan ayyuka a Abuja. Kwamishinan ‘yan sandan Abuja Wale Ajao ya sanar da haka ranar Talata a taron da ya yi da manema labarai kan matsalolin rashin tsaro da aka yi a gidan Ministan Abuja Nyesom Wike. Ajao ya ce mabaratan na tsare a ofishin Kula da inganta al’umma domin kulawa da su zuwa lokacin da za a maida su garuruwansu. Mahukuntan sun ce za a ci gaba domin…
Read More
WAEC ta janye sakamakon WASSCE na 2025 sakamakon tangarɗar na’ura 

WAEC ta janye sakamakon WASSCE na 2025 sakamakon tangarɗar na’ura 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar shirya jarrabawar kammala sakandire ta Afrika ta Yamma (WAEC) ta sanar da janye sakamakon jarrabawar kammala sakandare ta Afirka ta Yamma (WASSCE) na wucin gadi na shekarar 2025 ga ‘yan makaranta sakamakon gano abubuwan da suka shafi fasaha a tsarin fitar da sakamakon. Majalisar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da muƙaddashin shugaban hulɗa da jama’a, Moyosola Adesina, ya fitar a ranar Alhamis, 7 ga watan Agusta, 2025. A cewar sanarwar, shawarar ta biyo bayan wani nazari na cikin gida wanda ya nuna kura-kurai da suka biyo bayan wani tsari na…
Read More
Matsalar watsi da manyan ayyukan raya ƙasa

Matsalar watsi da manyan ayyukan raya ƙasa

A cikin wasu ’yan shekaru da suka gabata, Shugaban Ma’aikatar tantancewa tare da kula da kwangilolin gwamnati (Bureau of Public Procurement), Injiniya Emeka Eze, ya bayyana wa Majalisar Dattijai cewa, akwai kimanin ayyuka 19,000 a wurare daban-daban na faɗin ƙasar nan da aka yi watsi da su. Waɗannan ayyuka, sun haɗa da na Gwamnatin Tarayya da kuma na jihohi waɗanda ko dai gwamnati da ta fare su ba ta samu damar kammalawa ba, ko kuma gwamnatin da ta gaji ayyukan ta yi watsi da su. Ko shakka babu, akwai yiwuwar adadin nasu ma ya fi haka da ba don Shugaban…
Read More