ukarofi

12738 Posts
2027: PDP ta tabbatar da rahoton neman Jonathan ya tsaya takara

2027: PDP ta tabbatar da rahoton neman Jonathan ya tsaya takara

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kasa da sa'o'i 48 bayan da jaridar News Point Nigeria ta fitar da rahoto na musamman cewa jam'iyyar PDP na zawarcin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan kan yiwuwar dawowa Aso Rock a 2027, jam'iyyar adawar ta tabbatar da faruwar lamarin a hukumance. A cikin hirar da BBC Hausa a ranar Talata, Mataimakin Sakataren Yaɗa Labarai na Jam’iyyar PDP na ƙasa, Ibrahim Abdullahi, ya tabbatar da labarin farko na News Point Nigeria, inda ya tabbatar da cewa ana tattaunawa don shawo kan Jonathan ya daga tutar jam’iyyar a zaɓen shugaban aasa na 2027. "Haƙiƙa muna neman sa,…
Read More
Cocin Nijeriya ta yanke alaƙa da ta Wales kan naɗin mai goyon bayan auren jinsi

Cocin Nijeriya ta yanke alaƙa da ta Wales kan naɗin mai goyon bayan auren jinsi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Cocin Nijeriya (Anglican Communion) ta yanke alaƙa a hukumance da Cocin Wales bayan naɗin Bishop Cherry Vann, wani mai goyon bayan auren jinsi, a matsayin Babban Limamin Kirista na Wales. Shugaban Cocin Nijeriya, Rebiran Henry Ndukuba ne ya sanar da hakan a yayin buɗe taro na 14 na Cocin Nujeriya na Chancellor, Registrars da kuma jami’an shari’a a Abuja ranar Talata. Da yake kwatanta lamarin a matsayin "abin ƙyama," Primate Ndukuba ya bayyana cewa shawarar ta saɓa wa sadaukarwar cocin ga koyarwar Littafi Mai Tsarki. Ya kwatanta matakin da rabuwar Nijeriya da farko da Cocin Episcopal…
Read More
Dangote da Afreximbank sun ƙulla yarjejeniyar sake fasalin matatar mai

Dangote da Afreximbank sun ƙulla yarjejeniyar sake fasalin matatar mai

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Bankin Shigo da Kayayyaki na Afirka (Afreximbank) ya sanar da rattaɓa hannu kan wata yarjejeniyar bayar da tallafin Dala biliyan 1.35, domin tallafa wa kamfanonin Dangote. Yarjejeniyar wata ɓangare ce ta kusan Dala biliyan huɗu da aka haɗa ta hada-hadar kuɗaɗe na Dangote, babbar cibiyar masana'antu ta Afirka. Afreɗimbank ya yi aiki a matsayin mai tsarawa ne. A cewar wata sanarwa da Blueprint Manhaja ta gani, "Wannan tallafin - ɗaya daga cikin manyan lamuni na hada-hadar kuɗi a kasuwannin hada-hadar kuɗi na Afirka na baya-bayan nan - zai sake farfaɗo da kuɗaɗen da aka kashe wajen…
Read More
Mulkin Tinubu ya fi na Buhari muni — Maina Waziri

Mulkin Tinubu ya fi na Buhari muni — Maina Waziri

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Adamu Maina Waziri, ya caccaki Shugaba Bola Ahmed Tinubu da cewa gwamnatinsa ta kere ta tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta fuskar muni, wanda a yanzu ƙasar tana cikin mummunan bala’i.  Waziri, wanda jigo ne a jam’iyyar ADC (African Democratic Congress), ya bayyana haka ne a yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin na Trust Tɓ. “Babu ta inda gwamnatin Tinubu ba ta gaza ba. Ta gaza a dukkan fannoni, kama daga kan tsaro, tattalin arziki, yaƙi da cin hanci saboda komai ya tabarbare. Nijeriya…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta ware biliyan N4.2 don bunƙasa bincike da fasaha a makarantun gaba da sakandare

Gwamnatin Tarayya ta ware biliyan N4.2 don bunƙasa bincike da fasaha a makarantun gaba da sakandare

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin Tarayya ta amince da bayar da tallafin naira biliyan 4.2 ga ayyukan bincike 158 da ke ƙarƙashin Asusun Tallafawa Bincike na TETFund (NRF) na shekarar 2024. Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na TETFund, Abdulmumin Oniyangi, ya fitar a Abuja. Ya ce tantancewar da kwamitin nazari da sa ido na TETFund (NRFS&MC) ya gudanar ya biyo bayan karɓar bayanan ra’ayi 6,944 daga masana daban-daban a faɗin ƙasar. A cikin adadin, ɓangaren Kimiyya, Fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire (SETI) ya samu mafi yawan kuɗi da ya kai naira biliyan 2.34,…
Read More
Yadda wani sabon shiga aikin soja ya arce bayan hallaka wani ɗan sanda a Taraba

Yadda wani sabon shiga aikin soja ya arce bayan hallaka wani ɗan sanda a Taraba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Wani soja wanda ba a daɗe da yaye su ba, Dauda Dedan, ya yi layar zana bayan zargin sa da kashe wani ɗan sanda, Aaron John, ta hanyar daɓa masa wuƙa a Jalingon jihar Taraba. A yayin da yake magana da manema labarai a ranar Laraba, James Lashen, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9 na dare a Mayo-Goyi, da ke wajen garin Jalingo. Lashen ya ce, ɗan sandan ya samu rashin fahimta ne da wasu mazauna yankin da wannan soja ya soka…
Read More
Hukumar KSCHMA ta kammala shirye-shiryen shiga Jami’ar Northwest University Kano

Hukumar KSCHMA ta kammala shirye-shiryen shiga Jami’ar Northwest University Kano

Daga RABIU SANUSI a Kano Hukumar Kula da Lafiya ta Jihar Kano (KSCHMA) ta kammala wasu muhimman shirye-shirye a Jami’ar Northwest a Kano gabanin ƙaddamar da shirin bayar da gudunmawar kula da lafiya na ɗalibai (SCHEP) da aka shirya yi ranar Litinin mai zuwa. Tawagar KSCHMA ƙarƙashin jagorancin Dr. Jamila Mustapha a madadin Sakatariyar zartawar ta hukumar Dr. Rahila Aliyu Mukhtar ta samu kyakkyawar tarba daga Mataimakin Shugaban Jami’ar Farfesa Muktar A. Kurawa, inda ta yaba da ƙoƙarin hukumar na ba da fifiko kan kiwon lafiya da jin daɗin ɗalibai a manyan makarantun jihar Kano. Cikin jawabin, Farfesa Kurawa ya…
Read More
Ma’aikatan Hukumar ƙananan Hukumomin Nasarawa sun yaba wa sabon shugabansu Abdullahi Aliya

Ma’aikatan Hukumar ƙananan Hukumomin Nasarawa sun yaba wa sabon shugabansu Abdullahi Aliya

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Ma’aikatan hukumar kula da harkokin ƙananan hukumomin jihar Nasarawa da ake kira Nasarawa State Local Goɓernment Service Commission a Turance, sun yaba wa sabon shugabansu na hukumar wato Abdullahi Mustapha Aliyu dangane da tsarinsa na musamman na tabbatar da cigaban hukumar kawo yanzu da zuwansa kujerar wata biyu kacal. Ma’aikatan hukumar sun bayyana haka ne a lokacin wata ziyarar neman rahoto na musamman da wakilinmu ya kai sakatariyar hukumar a fadar gwamnatin jihar wato Lafiya a mako da ake ciki. Sun ce zuwa yanzu cikin watanni 2 kacal akwai wasu ingantattun tsare-tsare da shugaban…
Read More
Mun fara shirin farfaɗo da masaƙun Kaduna don inganta tattalin arziki – Ministan Masana’antu

Mun fara shirin farfaɗo da masaƙun Kaduna don inganta tattalin arziki – Ministan Masana’antu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ƙaddamar da wani shiri na farfaɗo da masana’antun auduga, masaƙu da tufafi a ƙasar, inda ƙaramin Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Sanata John Enoh, ya kai ziyara jihar Kaduna domin duba muhimman masana’antun da suka shafi ɓangaren. Ministan ya bayyana cewa sake farfaɗo da waɗannan masana’antu zai taimaka matuƙa wajen haɓaka tattalin arzikin ƙasa da samar da ayyukan yi ga matasa da ma sauran ’yan ƙasa. Bayan gudanar da wannan ziyara ta gani da ido, Sanata Enoh ya halarci wani taro tare da masu ruwa da tsaki domin tattaunawa…
Read More
Kuwait ta bai wa Nijeriya rancen Dala miliyan 25.35 don magance rashin zuwa makarantar yara a Kaduna

Kuwait ta bai wa Nijeriya rancen Dala miliyan 25.35 don magance rashin zuwa makarantar yara a Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Tarayya ta ƙulla yarjejeniyar rance mai rangwame na dala miliyan 25.35 da Asusun Raya Tattalin Arzikin Larabawa na Kuwait domin tallafawa shirin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Jihar Kaduna. Jaridar PUNCH ta rawaito cewa rancen, wanda aka sanya hannu a madadin Jihar Kaduna, na cikin ƙunshin kuɗi na dala miliyan 62.8 da haɗin gwiwar abokan ci gaba na ƙasa da ƙasa, da nufin faɗaɗa damar samun ingantaccen ilimi ga yara marasa galihu. Sanarwar da Ma’aikatar Kuɗi ta fitar ta bayyana cewa kuɗin zai tallafawa shirin “Reaching Out-of-School Children”, wanda…
Read More