29
Aug
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Mai martaba Sarkin Katsina ya naɗa sabbin hakimai bakwai ciki har da tsohon Ministan Sufuri Sanata Hadi Sirika a masarautar Katsina. Naɗin wanda ya gudana a fadar Sarkin Katsina ya zo ne a wani mataki na ƙarfafa tsarin gudanar da harkokin masarauta da kuma inganta shugabanci a yankunan da hakiman ke jagoranta. Hakiman da aka naɗa sun hada da Alhaji Sani Tukur Mu’azu Sarkin Rumah Katsina, Hakimin Batsari da Alhaji Abba Lawal Sani Dutsi Gabasawan Katsina, Hakimin Dutsi. Saura sun haɗa da Alhaji Gambo Abdullahi Dabai Dausayin Katsina, Hakimin Dabai daAlhaji Zakari Maina, Dan Yusufan…
