ukarofi

12479 Posts
Karancin lantarki, tsadar sufuri da cin bashi na barazana ga bunƙasar Nijeriya – Masana

Karancin lantarki, tsadar sufuri da cin bashi na barazana ga bunƙasar Nijeriya – Masana

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Cibiyar Bunƙasa Kamfanoni Masu Zaman Kansu (CPPE) ta yi gargaɗin cewa matsalolin samar da wutar lantarki, tsadar harkokin sufuri da jigilar kaya, rashin tsaro da kuma yawan kuɗin ruwa na iya kawo cikas ga mataki na gaba na bunƙasar tattalin arzikin Nijeriya. Cibiyar ta buƙaci gwamnatin tarayya ta sauya salon da take bi wajen aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki, inda ta mayar da hankali daga daidaita manyan ma'aunan tattalin arziki zuwa bunƙasa samar da kayayyaki da ayyukan yi. CPPE ta bayyana cewa, duk da cewa sauye-sauyen baya-bayan nan sun taimaka wajen inganta daidaiton tattalin arziki, kasuwar…
Read More
Tsadar haya da lamunin gida na ƙara jefa mazauna Legas cikin matsin rayuwa – Rahoto

Tsadar haya da lamunin gida na ƙara jefa mazauna Legas cikin matsin rayuwa – Rahoto

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Matsalar samun gidaje masu sauƙin biya a Legas na ƙara ta'azzara, sakamakon aarancin kuɗin shiga, tsadar ribar lamunin gidaje, hauhawar farashin filaye da kuɗin gina gidaje, ƙarancin ababen more rayuwa da kuma matsalolin tsarin mallakar fili. Wani sabon rahoto mai shafuka 86 mai taken “Bayan Hayar Gida: Nazarin Faɗaɗa Jari Ta Hanyar Gidaje a Legas” ne ya bayyana hakan. An ƙaddamar da rahoton ne a wani taron haɗaka mai taken “Bayan Hayar Gida: Taron Gidaje da Jari na Legas”, wanda GTI Inɓestment Group ta shirya a Legas. Taken taron shi ne “Gidaje, Jari da Makomar Legas”,…
Read More
Jihar Taraba ta fara inganta nau’in shanu da fasahar ƙwan haihuwa

Jihar Taraba ta fara inganta nau’in shanu da fasahar ƙwan haihuwa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Jihar Taraba, tare da haɗin gwiwar Shirin Tallafa wa Haɓaka Samar da Dabbobi (L-PRES), ta ƙaddamar da wani shirin haɗa maniyyin ingantattun bijimai ga shanu a faɗin jihar, da nufin inganta nau’in shanu da ƙara yawan samar da madara da nama. An aaddamar da shirin ne a ranar Asabar a Jalingo, babban birnin jihar, inda ake sa ran zai taimaka wajen ƙara yawan amfanin garken shanu da kuma bunƙasa darajar kiwon dabbobi a fannin tattalin arzikin jihar. Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da shirin, Manajan Daraktan Kamfanin Liɓestock Genetics Africa Ltd, Emmanuel Nnoku, ya…
Read More
SERAP ta buƙaci INEC ta bayyana iyakar kuɗin tallafin siyasa kafin zaɓen 2027

SERAP ta buƙaci INEC ta bayyana iyakar kuɗin tallafin siyasa kafin zaɓen 2027

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD ƙungiyar Kare Haƙƙin Tattalin Arziki da Walwala da Yaƙi da Rashawa (SERAP) ta buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana ko ta yi amfani da ikon da doka ta ba ta wajen sanya iyakar kuɗin da mutum zai iya bayarwa ga jam’iyyar siyasa ko ɗan takara a zaɓen 2027. ƙungiyar ta kuma nemi Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana wa ’yan Nijeriya iyakar kuɗin tallafin siyasa da hukumar ta amince da su, tare da tabbatar da cewa an sanar da jam’iyyun siyasa, ’yan takara, masu bayar da tallafi da sauran jama’a…
Read More
WISE ta horas da mata da matasa kan kasuwancin girki cikin tsafta

WISE ta horas da mata da matasa kan kasuwancin girki cikin tsafta

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wata ƙungiya mai rajin kare muhalli, Women Initiatiɓe for Sustainable Enɓironment (WISE), tare da haɗin gwiwar Energy and Enɓironmental Law Club na Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya, ta horas da mata da matasa kan damar kasuwanci a fannin girke-girke mai amfani da makamashi mai tsafta. Shugabar kuma Daraktar WISE, Olanike Olugboji Daramola, ce ta bayyana hakan a yayin bikin EcoCare Campus Initiatiɓe 2026, wani shirin tsaftace muhalli da aka gudanar a harabar Kongo ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. An gudanar da bikin ne domin karrama Comrade Jerry Adams, tsohon Shugaban Hukumar Tara Haraji ta…
Read More
Taiwo Hassan ‘Ogogo’: Rayuwar jarumin da ya mayar da al’ada gadon Nollywood

Taiwo Hassan ‘Ogogo’: Rayuwar jarumin da ya mayar da al’ada gadon Nollywood

Daga AISHA ASAS A lokacin da ake magana kan jaruman da suka taimaka wajen gina masana’antar fina-finan Najeriya, musamman ɓangaren fina-finan Yarbawa, sunan Alhaji Taiwo Babatunde Hassan, wanda aka fi sani da Ogogo, ba ya cikin waɗanda za a iya tsallakewa. Ogogo ya shafe sama da shekaru arba’in yana haskawa a gaban kyamara, yana taka rawar da ta sa mutane suka saba ganinsa a matsayin mutum mai mutunci, dattijo mai natsuwa, jagora ko kuma mai tsayawa kan gaskiya. Amma kafin ya zama ɗaya daga cikin fitattun fuskokin Nollywood, rayuwarsa ta fara ne da sana’ar da ba ta da alaƙa da…
Read More
Zan kawo wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20 a 2027 — Matawalle

Zan kawo wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20 a 2027 — Matawalle

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya ce yana da burin tara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ƙuri’u miliyan 20 a zaɓen Shugaban ƙasa na 2027. Matawalle ya bayyana hakan ne ranar Talata a Abuja, yayin da dubban magoya bayansa da ’yan jam’iyyar APC suka tarbe shi bayan dawowarsa Nijeriya. Ya ce zai fara tattara bayanai da neman ƙuri’u a faɗin jihohin Nijeriya 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja. “Kamar yadda kuka sani, an fara kamfen, kuma burina shi ne in kawo wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ƙuri’u miliyan 20 a zaɓen shugaban ƙasa na…
Read More
Gwamnan Gombe bai isa ya yi min ritaya a siyasa ba – Sanata Goje

Gwamnan Gombe bai isa ya yi min ritaya a siyasa ba – Sanata Goje

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Yayin da ake ci gaba da hasashen matakin da zai ɗauka bayan dambarwar da ta taso daga zaɓukan fitar da gwani na jam'iyyar APC, wadda ta kai ga ya sara tikitin takarar sanata, tsohon gwamnan jihar Gombe kuma sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya, Muhammed ɗanjuma Goje ya ce zai ci gaba da mara wa jam'iyyar APC baya domin ta samu nasara a zaɓe mai zuwa. A baya dai an yi hasashen cewa jigon a siyasar jihar Gombe da ke yankin Arewa maso gabashin Nijeriya zai sauya sheƙa zuwa wata jam'iyya domin ƙalubalantar hana…
Read More
Na yi alƙawarin tabbatar da nasarar Tinubu a Zaɓen 2027 — Yari

Na yi alƙawarin tabbatar da nasarar Tinubu a Zaɓen 2027 — Yari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sanata mai wakiltar Zamfara ta Yamma, Abdulaziz Yari, ya yi alƙawarin tabbatar da nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027. Yari ya yi wannan alƙawarin ne bayan jam’iyyar All Progressiɓes Congress (APC) ta naɗa shi Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2027. A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ya gode wa Shugaba Tinubu da jam’iyyar APC bisa amincewa da shi, yana mai cewa zai ɗauki nauyin da aka ba shi da matuƙar muhimmanci. “Ina miƙa godiyata ta…
Read More
Gwamnatin Zamfara ta gargaɗi malamai da aka horar kan su guji sakaci da aiki

Gwamnatin Zamfara ta gargaɗi malamai da aka horar kan su guji sakaci da aiki

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Gwamnatin Jihar Zamfara ta yi gargaɗi ga malaman makarantun sakandare 250 da aka horar kan su guji yin sakaci kan aikin su, tana mai cewa duk wani malami da aka samu yana da halin rashin ɗa'a da rashin zuwa aiki zai fuskanci hukuncin ladabtarwa bisa ga doka. Kwamishinan Ilimi, kimiyya da fasaha, Hon. Abdulmalik Gajam ne ya bayar da gargaɗin a yau Asabar a bikin rufe taron horar da malamai na tsawon makonni biyu na shirin Global Standard Change Program (GSTTP) da aka gudanar a Gusau. Shirin gina ƙarfin aiki ya samu hirar da malaman…
Read More