28
Aug
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya cire jami’an da ba su da kwarewa daga cikin gwamnatinsa, yana mai cewa kasancewarsu na jawo wa gwamnatin abin kunya. Ndume, wanda tsohon shugaban marasa rinjaye ne a Majalisar Dattawa kuma jigo a jam’iyyar APC, ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Arise Tɓ. Ya ce abin da ya kira “kakistrocrats”, wato mutanen da ba su da kwarewa ko cancantar gudanar da mulki, na taka muhimmiyar rawa wajen haifar da rikice-rikice da badakalar da…
