29
Aug
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya ce dawo da tallafin man fetur zai iya mayar da Nijeriya cikin matsalolin tattalin arzikin da ta fuskanta kafin cire tallafin. Idris ya ce matakin cire tallafin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ɗauka ya taimaka wajen samar da karin albarkatun da aka raba tsakanin Gwamnatin Tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi. Ya ce a shekarar 2022, Nijeriya ta kashe kusan dala biliyan 10 wajen tallafin man fetur, a lokacin da kasar ke fama da raguwar samar da danyen mai da karancin kudaden…
