Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin Jihar Adamawa ta musanta karbar tireloli 20 na abincin tallafi daga Gwamnatin Tarayya.
Ta bayyana cewa duk da haka, maimako zaman jira, ta ɗauki matakin raba nata kayan tallafin domin rage wa al’ummar jihar halin da suke ciki na matsin rayuwa.
Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Iliya James, ranar 29 ga watan Yuni, ya sanar cewa, gwamnatin jihar ta karɓi kasonta na takin zamani da Gwamnatin Tarayya ta bayar domin raba wa al’umma.
A cewarsa, gwamnatin jihar a shirye take domin inganta walwalar jama’a, duk da ƙalubalen da ake fuskanta ƙasar.
Sai dai ya shawarci al’ummar jihar da su guji shiga taruka da ka iya haddasa tarzoma da mummunan sakamako kamar yadda aka gani a lokacin zanga-zangar ‘End SARS’.
Kwamishinan ya jaddada muhimmacnin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali don cigaban al’umma, yana mai gargaɗi ga masu neman ɓarnata dukiya ko haddasa tashin hankali.
A cewarsa, Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri da gwamnatinsa za su ci gaba da yin duk mai yiwuwa don magance matsalolin da ke ci wa Nijeriya tuwo a ƙwarya da kuma inganta rayuwar al’umma.
