Ba za mu yi haɗaka da kowa ba – SDP

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jam’iyyar SDP a Nijeriya ta yi watsi da yunƙurin haɗaka tsakaninta da sauran jam’iyyun adawa da nufin tunkarar zaɓen 2027.

Wannan na zuwa yayin da ake ganin tagomashin jam’iyyar ta SDP ya ƙaru sakamakon sauya sheƙar da wasu manya ‘yan siyasa a ƙasar ke yi zuwa cikinta.

A makon da ya gabata ne wasu jagororin adawa ƙarƙashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar na babbar jam’iyyar hamayya ta PDP suka sanar da cewa suna wani yunƙuri na ƙulla haɗaka domin kawar da APC a zaɓen 2027.

Sai dai shugaban jam’iyyar na ƙasa Alhaji Shehu Musa Gabam a hirarsa da BBC ya ce SDP ba za ta haɗe da wata jam’iyya ba.

“Mun faɗa wa duniya cewa mu ba za mu yi maja ba, ba maganan haɗewa domin akwai ƙa’idoji kuma rashin cika ƙa’idojin wata fitina ce,” inji shi.

Ya ce babu hannun SDP a yunƙurin hadewar jam’iyyun adawa domin a cewarsa jam’iyarsu tana da tsari.

Shugaban SDP ya ce sai dai duk wanda yake son ya shigo ya zo don gina jam’iyyar.

Ya ce tsarinsu shi ne, duk wanda yake son shiga jam’iyyar zai tafi ne mazaɓarsa, daga nan zai iya takarar duk muƙamin da yake so.

Alhaji Shehu Musa Gabam ya bayyana shakku kan haɗakar jam’iyyu a Nijeriya inda ya yi zargin yadda jam’iyya mai mulki ke shiga cikin jam’iyyun adawa tana karya su.

“Ba mu san su wane ne da kuma manufofin da za su shigo da su ba, wannan ya sa NWC ya ƙayyade cewa babu maganar maja,” inji shugaban jam’iyyar SDP.

Ya ƙara da cewa tsarin jam’iyyarsu ya sha bamban da sauran jam’iyyu musamman batun korar ‘yan jam’iyya da ake yi daga mazaɓar mutum.

Ya ce shugaban jam’iyya a mazaɓa ba ya da ikon korar mutum sai da amincewar shugabancin jam’iyyar.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai na cikin manyan ‘yansiyasar da suka sauya sheƙa zuwa SDP, wanda kuma a wata hira da BBC ya yi wa wasu manyan jagororin adawa tayin sabuwar jam’iyyar tasa.

Shugaban jam’iyyar SDP ya ce akwai ‘yansiyasa sama da 200 da suka yi murabus daga jam’iyyunsu suka shigo SDP, sai dai bai bayyana sunayensu ba.

By ukarofi