Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Majalisar Malamai na ƙungiyar Jama’atul Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS), Sheik Sani Yahaya Jingir, ya ce ba zai goyi bayan takarar Bola Tinubu ba a zaɓen 2027 matuƙar ya canza Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa.
Ya bayyana hakan ne yayin wani taron wa’azi a masallacinsa na ’Yan Taya da ke Jos, babban birnin jihar Filato.
Manhaja ta rawaito cewa a zaɓen 2023 da ya gabata dai Sheikh Jingir ya goyi bayan Tinubu sannan ya umarci magoya bayansa da su ma su yi haka a wancan lokacin.
Jita-jitar da ake yaɗawa dai a kan cewa akwai yiwuwar Tinubu ya ajiye Kashim ɗin a matsayin abokin takararsa a zaɓe mai zuwa ta dada ƙamari a ’yan kwanakin nan.
To sai dai da yake nasa tsokacin a kan batun, malamin addinin ya ce, “Na ji akwai wasu mutane marasa kishin ƙasa daga ciki da wajen APC da ke ƙoƙarin lalata alaƙar da ke tsakanin Tinubu da Kashim domin cimma mummunar manufarsu. To mu ba ma maraba da wannan Shugaba Tinubu.
“Ni da wasu na kusa da ni mun goyi bayan Tinubu da Kashim, kuma za mu sake goyon bayan takararku a tare. Duk wani yunƙuri saɓanin haka ba na tare da shi kuma ba zan goyi baya ba saboda a baya sun amince su yi aiki tare.
“Na goyi bayansu ba tare da sun ba ni ko sisi ba. duk da yake ina da kusanci da Atiku, amma na ce Tinubu da Kashim zan yi. Akwai jita-jitar da ke yawo cewa dangantaka ta yi tsami a tsakaninsu, amma ni ban yarda da, na fi tunanin aikin makiya ne,” inji malamin.
Sheikh Jingir ya kuma yi kira ga Shugba Tinubu da kada ya saurari masu kiran nasa da ya ajiye Kashim ya canza shi da wani a 2027, inda ya bayyana waɗannan mutanen a matsayin marasa son ci gaba.
