Real Madrid ta yi rashin nasara a gasar la Liga a karon farko cikin wasanni 43 bayan da ta sha kashi da ci 4-0 a hannun babbar abokiyar hamayyarta Barcelona a wasansau da aka buga a filin wasan Santiago Bernabeau da ke birnin Madrid.
Robert Lewandowski ya jefa ƙwallo biyu a cikin ragar Madrid a minti na 54 da 56, kafin lamine Yamal ya ƙara a minti na 77. Raphinha ne ya ƙarasa Madrid a minti na 84.
Madrid ta nemi kamo Barcelona a matsayin waɗanda suka fi daɗewa ba tare da yin rashin nasara a La Liga ba, bayan da ba a doke ta ba a wasanni 43 da ta buga a baya.
Wannan sakamakon na nufin Wasan Classico na farko da Kyllian Mbappe zai buga bai yi masa daɗi ba, bayan na soke wa ɗan wasan na Faransa ƙwallo biyu da ya ci kafin a tafi hutun rabin lokaci.
Barcelona tana kallo Real Madrid ta lashe kofin la Ligar kakar wasan da ta gabata da tazarar maki 10, kuma wannan kakar rashin tagomashi da ta samu a bara gami da barazanar tattalin arziki ya sa ta dogara ne kan matasan ’yan wasa a kakar wasan bana.
Amma da alamu sun fara cin gajiyar wannan lamarin sakamakon cewa tawagar Hansi Flick ta ci wasanni 10 a kakar wasan bana inda ta yi rashin nasara a wasa ɗaya kacal.
Babu Shakka Lamine Yamal shi ne matashin da ya fi ɗaukar hanlkali a tawagar Barcelona a halin yanzu, amma akwai wasu matasan da ke taka muhimmiyar rawar gani inda ’yan wasa irinsu Casado da Balde suka taimaka aka zura ƙwallaye a ragar Madrid.
